Uncategorized

SAMEEHA D






★★★★




       “”Haba Yaya tunda nace ki ajiye dan Allah ki ajiye awajan ki idan buqatar kar6ansu yataso Sameeha zata zo da kanta ta kar6a tunda hakkin ta ne bana muba,to ai shi kenan tunda kin nace zan ajiye aguna Amma da babanta kika bawa shi yafi kowa chanchanta daya ajiye agurinsa Sha anin kudi wahala gareshi.


Shima yasan da hakan yace abaki ki ajiye tun Randa aka Kai ta na sha’afa ban Baki ba saboda taron jama’a daya sha Kai na Yaya jummai.


Ni dai wlhy har Zuciya ta ban niyar ta6a kudin nan ba bare kar6ansu Amma yazanyi zan Danna zuciyata na ajiye Yaya ko wajan Sameeha.


Alhamdulillah tana Nan lafiya.


Ya akai kika San haka ko Moona taje ne.


Aa Babu Wanda yaje tace zata na hanata zuwa Naga yaushe sameeha tabar gidan da har za’aje dubata ita ba qaramar yarinya ba.


Hmmmmm shi kenan Dan kin aurar da ita tabar kulawarki ki bar yarinya taje ta gano Mana lfyar ‘ya ba sai ta dauki wani dogon lokaci ba yauwa ga wannan rubutun idan Moona zataje ki Bata ta Kai mata kwanannan sai mugayen mafarkai nake akanta marasa dadin ji Ni hankalina Bai kwanta da gidan Nan nasu ba Sam wlhy.


Murmushi Umma tayi tace.


Yaya jummai kenan Dan Allah Musa aranmu Babu wani Abu dazai taso face Khairan mu Dena wannan tunanin.


Wlhy bazan Dena ba ki bayar akai mata bake nace ki Shaba ba Kuma cutar da ita zanyi ba ato Ayoyi ne na tsari malama.


Bata Kai ga haka ba insha Allah zan bawa Moona ta Kai mata,to Ni na wuce sai na sake dawowa naji lafiyar ‘yata danke haihuwarsu kadai kika iya.


Ummm Yaya jummai kenan.


Naji ko me Zaki ce sai na Fadi gaskiya Kinga sai anjima Ni natafi,,fuuu ta miqe ta fito daga dakin.


To ki gaida gida, Yaya jummai tayi hanyar qofa, Umma ko sai juya rubutun take tana tunanin yazatayi dashi Dan ba kaiwa Sameeha zatayi ba……





_*By*_

_*Maman Dr✍️*_

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button