Uncategorized

SAMEEHA J


        Da wannan damar Momy ta ƙara maimaye kan Alhaji bukar baya ganin kowa da gashi sai ita da ƴarta,ko mutane sun tsegunta masa halin momy,zagi da masifa ce tsakaninsu dashi sun sakawa iyalin sa ido zagin mutane da shawarar da wata aminiyar momy ta bata na janye Sameer ta kyautata masa yanda shima zai taso sai abinda tace dashi,ta hakan zata ƙara samun Alhaji bukar a tafin hannun ta,hakan kuwa tayi idan ba momy ba sameer bai san kowa ba har sanda yayi aure ita yake gani kamar mahaifiyar sa,ko auran sa ma,Allah ne ya ƙaddara za’a ɗaura dan sai bayan auran ma su hajiya fatima suka sani.




*CIGABAN LABARI????*



       “Ko da zee tayi ɓarin su Sameer ki ciɓus sukayi da Sameeha ta fito daga ɗaki, zuru zee tayi tana kallon Sameeha,itama Sameeha ta kalle ta,da mamaki zee ta furta,,””yaya ita da aka ce tazo ta duba ko Sameeha ta wula,zata tarar kamar yanzu ta diro duniyar ba shiri ta juyo tayi ɓangaran momy da sauri har ta ƙarasa ta kutsa dakin kai tsaye ta na””””


“”Momy ga baƙin labari,ido momy ta zubawa zee tana soraron abinda zata faɗa daga zaune,zee ta ƙaraso ta na”””


“Momy garau yarinyar chan take na rantse da Allah kamar babu abinda ya sameta,a tsaye fa naje na same ta.


Anya kuwa ba gizo take yi miki ba Zainabu,yarinyar da ko motsin kirki batayi na baro ta.


wallahi zo mije kigani da idanun ki anya kuwa aikin nan yayi.


gaskiya bana shakku akan aikin mu amma muje dai nagani da idanu na,momy ta miƙe da sauri,da miƙewar momy da shigowar Alhaji bukar ɗakin kusan atare ya ƙaraso yana.


   “Maza maza ɗauki mayafi ke da zee muje kuga gidan da Sameer zai zauna,yanzu akayi min waya nazo nagani ko yayi na basu kuɗin su,shine nace bari mutafi tare idan yayi muku to yayi mun nima sai abiya akarɓi takardun ku hanzarta Zainabu.


Amma Alhaji dakaje kai kaɗai idan yayi maka muma yayi mana babu wani abu a ciki.



Aa tare nake son muje mu gani nasanku ku mata da ƙananan magana,dakuce nan yayi chan beyi ba,sai chan yayi kaza da kaza ku wuce kawai muje mu dawo.


Alhaji kaje mana………Nace ku wuce muje ko sai na ɓata miki rai ne Asma’u.


kutumar……….abinda momy ta furta a zuciyar ta kenan ta ƙarasa da.


lallai ma Bukar ni zakayiwa tsawa kamar ƴarka,hmmmm laya bakya kusa amma,tayi kwafa,zan rama,”duk daga cikin zuciyar momy take maganar a fili ta zari hijabinta ƙato suka fito ita da zee suka shiga mota,sai da Alhaji bukar yazagayo mazaunin direba tukunna momy tasan shi zai tuƙa motar ba sameer ba, da tayi kamar zatayi magana sai taji an ɓame mata baki,tayi shiru har Alhaji bukar yaja motar da kaɗan ya rage su fita daga cikin gidan ta hangi Sameer yayi nashi ɓangaran da Sameeha take,haka kawai taji gaban ya faɗi suka fita daga gidan.



*IN DA RAI DA RABO,IN ALLAH YASO ABU BABU WANDA YA ISA YA HANA,SAMU DA RASHI DUK DAGA ALLAH YAKE,ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CHARA KO ANA SHAWO KO ANA MUZURU SAI YA KAI.*


“A wannan rana a dai dai lokacin Allah yayi ikonsa akan,Sameer da Sameeha,a nan fallon nasu shi kansa bai san taya ya hakan ta kasance ba tsintar kansa kaɗai yayi cikin wata duniya me wahar fassaruwa.












_*By*_

_*Maman Dr*_

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button