Uncategorized

SAMEEHA L


????SÂMÊÊHÂ????_*

           (L)


Tun da Sameer ya koma chan ɓangaran da zama gaba ɗaya momy ta kanainaye kansa,zee ke dafa masa abinci ta bashi ya sha da, duk wata ɗawainiyar kulawarsa ta koma hannun su,Sameeha na ɓangaran ta basu damu da cin ta ko shan ta ba,babu wanda yake bin ta tata Allah yaso da komai da komai na cimar ɗan adam a ajiye,wani lokacin har shirya kayan ta take tsaf ta yafa mayafi ta fito da zumar guduwa gida abin mamakin da tazo dai dai get ɗin gidan zataji ta manta komai har ita kanta sai jalolo ko baba me gadi yaje ya sanar da momy zata fito da kuka tana rarrashin Sameeha da ban baki akan abinda sameer

yake mata ta janyo ta ɓangaran ta su haɗu su biyun su jibgeta yanda suke so wai zata tona musu asiri daga ƙarshe ma kafeta momy tasa aka yi a iya ɓarin ta,ko harabar gidan sameeha bata isa ta fito ba har aka haɗa uban kayan lefen Sameer da Zee kasuwa guda,dan kayan ya wuce hankali mai hankali kamar ba mace ɗaya za’akaiwa ba.


    Zaune suke su uku a fallon suna tsara yanda biki zai kasance Zee da Sameer da momy suka jiyo sallama daga bakin fallon,amsawa momy tayi ta bada umarnin shigowa kai tsaye mona ta shigo fallon ɗauke da ledar ƴar babba a hannun ta,tsugunawa tayi a dai dai inda ta shigo ɗin ta ce.


“”Momy ina yini.


lafiya lau mona ko Allah yasa na faɗi dai dai.

murmushi mona tayi tace da momy.


dai dai kika faɗa momy,ta dubi inda sameer yake zaune tace.


“yaya Sameer ina yini.


ya juyo da sauri ya dubi mona ya dubi momy da gaba ɗaya fuskar ta ta chanja ya ce.


Momy ita kuma wannan daga ina ko ita ce zatayi mana aikin,Zee ita kika zaɓar mana bana ce ɗayar tafi girma ba.


dummm gaba ɗaya wajan yayi mona tasake cewa da sameer.


baka gane niba yaya Sameer to inmaka gwari gwari ni ce Maimun ƙanwar ya Sameeha daka aura.


Wace ce kuma Sameeha momy kinji fa…….kai dan Allah bar wannan wasan kin san sameer da barkwanci yaya mutanan gidan naku suke.


Ba wani barkwanci momy har cikin zuciya ta ban shaida wannan matar ba ummm amaryata muje muga holl ɗin da zamu kama kar wasu su rigamu 


mona tayi zuru tana kallon ikon Allah,tashi sameer yayi zee tabiyo shi a baya ta gefan mona gaba ɗaya suka zo suka wuce baki har kunne mona ta bisu da kallo da ɗunbun mamaki fall a cikin ranta…………..








_*By*_

_*Maman Dr*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button