Uncategorized

SAMEEHA O

 _????SÂMÊÊHÂ????_*

            (O)

A hankali mona ta ƙaraso daf da gawar Abba dake kwance a kan tabarma Umma na kusa dashi sai Addu’o’in nema masa rahama take,Mona ta durƙushe ƙassa ta dubi Abba ta juya ta dubi umma,bakinta na rawa ta ce””

“Umma Abba na……..,kuka me ƙarfi ya ƙwace mata umma ta dubeta da ita ma kukan take har yanzu ta ce”Abba ya tafi maimuna ya barmu shikenan mutuwa ta rabamu dashi har abada wayyo Allah duniya ba matabbata ba La illaha illallahu Muhammadan Rasulullah S’A’A,Allah yasa ka huta Abba yasa chan tafi nan.


girgiza kai mona ta shigayi tana jijiga gawar Abba dake kwance tana”


“A a bai mutu ba Umma da ransa,katashi Abba ka nuna musu baka mutu ba kana da ranka Abba karka tafi ka barmu dan Allah ka tashi ka faɗa musu wayyo Allah na ya Sameeha Abba na……..kuka sosai mona da Umma suke kamar ransu zai fita da ƙyar aka ɓanɓare mona daga jikin gawar Abba maƙota da abokanan arziki suka fara ƙoƙarin shirya Abba,an buƙaci ko Umma zatayi masa wanka Umma ta ce bazata iya jirewa ba kasan cewar Abba bai da ɗa namiji ƴan uwansa ma duk matane su uku aka baiwa limamani unguwar yayi masa wanka ya shirya shi kamar yanda addini ya gabatar aka feshe gawar da turare me ƙamshi aka kira umma da sauran ƴan uwa suyi sallama.


Innalillahi kowa ka dubeshi hawaye ne yake zuba har da yaya jummai da maganar ta ma gaba ɗaya ta ɗauke sai jijjiga kai take da charbi a hannun ta, mona kuwa faɗuwa tayi ƙassa tana kiran Abba da ya Sameeha tazo kar atafi da Abba ahaka aka fita da Abba za akai shi gidansa na gaskiya.????


        Alhamdulillah kyakkyawan zato da yabo Abba ya samu mutum ne me haƙuri da rayuwar duniya ka ɓata  masa yana murmushi haka inka kyautata masa,sam bai da abokin faɗa magana ma bata dameshi ba ga son zuminci da son yataimaki wanda bai dashi koda nashi ne ya saura,ya samu al’umma da yawa wanda suka rakashi da Addu’o’,i har aka dawo gida.


Zazzaɓi ne me zafi ya rufe Mona da har yanzu kuka take tana kiran Abba da ya Sameeha nan ƙannan abba suka tambayi Sameeha da ma waƴanda suke shigowa gaisuwa,sai dai ace bata ƙaraso ba aka shiga kiran layin ta na waya bayan an kira na Sameer duk a kashe,an samu kiran ya shiga sai dai ba’a ɗaga wayar shine umma ta bada layin momy aka kira kai tsaye momy ta ɗaga da”””


“,Hello,wake magana.



“Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah.



cike da isa da gadara momy ta amsa da.



“Wa’alaikumssalam,waye?.


“Daga gidan su Sameeha ne.


da sauri momy ta gyara maganar haɗe da ƙalƙalo murmushin dole kamar a gaban su ta ce’


Ayya wallahi ban lura ba dayake number ce kuma ɗazu akai ta damuna da wata number.


lah babu komai wallahi Saratu ce ƙannawar mahaifin Sameeha dama mun kira numbera Sameer tun ɗazu akashe itama sameeha mun kira ta bata ɗaga ba.


“Ayya ina ji Sameer chaji yasa ka,ita kuma Ɗiyata ko bata kusa da wayar amma bari na kai mata lafiya kuwa. 


“Wallahi Abban ta ne Allah yayiwa rasuwa ɗazu ɗazun nan.



“INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJU’UN,Abba kuma YA SALAM,bari na nemi waje na zauna jiri ke ɗiba na baiwar Allah.


Yi a hankali hajiya Allah yafi mu son shi kuma lokacin sa ne yayi sai haƙuri.


Kuka Momy ta saka tana” 



“in sha Allahu yanzu yanzu zamu iso ai da tun kan akai shi aka kira aka faɗa mana amma babu komai Allah sarki ɗiyata ko ya zanyi na sanar mata.


Wallahi an kira lokacin bamu farga da number ɗin ki ba kowa hankali atashe ki barta in kunzo taji daga bakinmu ko ta gani kar hankalinta ya tashi.


“to to shikenan wayyo rayuwa bawan Allah nan ba sawa ba cirewa mutumin arziƙi dan Allah ayiwa ƴar uwata Umma gaisuwa kafin mu iso da sauran jama’a,duk cikin kuka momy ke furtawa sukayi sallama da Saratu momy tasa tishu ta goge hawayen ta haɗe da miƙewa tsaye tana rawa tana””



Nasara dai boka hatsabibi uban hatsabibai buƙata ta biya kifi yatafi saura kifanyar tabi bayansa da sannu sannu tafiya zatayi nisa,momy ta shige ɗakin ta tana rawa,ƙarƙashin godo ta zura hannunta wannan kwaɗon ta zaro ta buɗe bakinsa ta zira ƴan yatsunta guda biyu ta zaro layar sai mutsu mutsu ƙwaɗon yakeyi momy ta danna layar da ƙarfi haɗe da kiran.


         “”Hatsabibi.


take sarkin hatsabibai ya bayyana a ɗakina ya na””



 “”Buƙata ta biya me kuma kike da buƙata.



murmushin jin daɗi momy tayi ta buɗe baki zata furta kenan,cikin sauri sarkin hatsabibai ya dakatar da ita da.


“ba wata matsala aciki yanzu zan saka Aljana *Unushka* ta kawo ta amma dole ke zaki sarrafa ta yanda zatayi magana da wannan layar ta hannunki na san ba sai nayi miki bayani ba,cike da farin ciki momy tayi godiya sarkin hatsabibai ya ɓace ba afi minti uku da ɓacewar sa ba Sameeha ta bayyana a ɗakin da wannan igiyar a hannun ta,zagaye ta momy tafarayi da layar a hannu idanuwan sameeha suka juye chan kuma suka dawo dai dai momy ta kwance mata igiyar ta umarceta da ta miƙe.




miƙewa tsaye Sameeha tayi,momy ta sake cewa ta zauna,nan ma sameeha ta koma ta zauna.

(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

   dariya momy ta saki lokaci ɗaya ta murtuke fuska ta ce da Sameeha.




“Saka kuka.



Sameeha ta fashe da matsanancin kuka harda gunji da karaɗi momy ta ce”yi shuru,take Sameeha tayi shiru kamar ba ita ke gafza kuka yanzu ba.



da kanta momy ta haɗawa Sameeha ruwan wanka a banɗakin ta tace da ita taje tayi zungwi zungwi Sameeha ta je tayo wankan ta fito mai momy ta miƙa mata nan ma ta karɓa ta shafa momy ta bata sababbin kaya tasaka doguwar riga da zunbulelan hijabi ita ma momy tasaka ƙaton hijab ta shiga mota Sameeha na gaba tajasu da kanta suka tafi gidan su sameeha.




         

isar su gidan kenan momy ta nemi waje tayi fking,kallon sameeha tayi ta ce””



“Saka kuka.



A take Sameeha ta kwaɓe baki ta fara kuka momy ma tasaki kukan suka fito daga cikin motar hankalin jama”a gaba ɗaya ya yo kansu…….








_*By*_

_*Maman Dr*_

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button