SAMEEHA P

“”Me yasa ban murje banza na nuƙashi da kaina ba?
me yasa har na bari shashashan mutanan nan suka farga da cikin?
me yasa me yasa tunani na bai kawo haka zata iya faruwa ba kai cona na zama banza na zama shashasha,menene abinyi,ta daki jikin durowar ta sai zagaye ɗakin ta ke tana furta””
bazaka zo duniya ba in sha Allahu ko komai nawa zasu ƙare na rantse da wanda ya halicce ni bazaki haifi abinda ke cikin ki ba Sameeha ko duk duniyar nan zasu taru akan ki sai inda ƙarfina ya ƙare zaro layar ta tayi ta danneta da ƙarfin tsiya rai a ɓace sarkin hatsabibai ya bayyana,sun ɗauki tsawon lokaci suna tufka da warwara har suka ƙula abinda suka ƙula ya ɓace daga ɗakin momy ta ɗauki gyale da mukulin mota ta fita.
……………………
Allahu Akhubar,har an yi bakwai ɗin Abba Sameeha na gida ƴan uwa da abokan arziƙe duk an cika ana ƙara jimantawa,har Sameer a ranar sai da yazo sakamakon da momy ta tasoshi a gaba da uban kayan sha tara na arziƙe ya ware tas dashi kamar bashiba har ƴar tsokanar junna sukayi da mona abin ya bala’in bata mamaki har umma sai da ta kuma tara da maganar,umma ta ce sauƙi ya samu da kansa ya nemi Sameeha ta koma a yau momy ta ɗan saka baki wai ya barta ta kuma kwana biyu bai furta komai ba sai da momy ta zura hannunta a wayence ta matse ƙawarta dake cikin jaka da sauri Sameer ya ce.
“Hankali na ne baya nan baya gida Umma ayi haƙuri idan na takura,yana faɗi yana sosa ƙeyarsa kamar munafuki mona tayi charf ta ce”
“aiko sai dai yayi ta yawo a sararin samaniya ya sameeha sai ta sauke.
“Haba ƙanwa ta haka zamuyi dake to ai shikenan zan saka ki cikin layin manyan……….,momy ta amshi zanchan”
“”kama isa mona ɗin tawa guda kaje zan tawo da ita insha Allah.
Sallama Sameer yayi musu haɗe da ajiye kuɗi masu nauyi yayi kuma alƙawarin kulawa da Umma da mona kamar yanda zaiwa momy,Addu’a kam yashata sai da yatafi yaya jummai ta ƙaraso sunyi saɓani da aka faɗa mata abinda ya wakana,ta dubi momy da ita ma momy ke duban ta tace””
“”Mun gode bama buƙatar taimakon kowa sai na Allah.
ya jummai ta bar ɗakin kowa yayi tsit a ɗakin saboda kunya,koda dare yayi jalolo yazo ɗaukar su momy da sameeha kuka sosai sameeha da mona suka dinga yi duk da rashin sanin wace ce ita amma hakan ya taɓa zuciyar sameeha sai kallon Umma da mona take tana kuka wiwi kamar bazata sake ganin su ba da ƙyar momy ta janyota tana bata haƙuri da ban baki har ta tusa ta mazaunin baya ita ma momy ta shiga jalolo ya ja suka ɗauki hanyar gida.
Ko da suka iso gida jalolo ya danna (horn) baba me gadi ya fito da sauri ya buɗe (get) ɗin gidan suka shigo chan gefe ɗaya jalolo ya tsaida motar momy ta buɗe ƙofar motar ta fito ta zagayo ta buɗewa Sameeha ma ta fito baba me gadi yayi shiru yana duban sameeha bayan yaiwa momy san da zuwa,sallamar su momy tayi cikin tsawa da ɗaga murya kowa yayi inda yake momy ta kamo hannun Sameeha suka nufi ɓangaranta suna shiga fallon momy na hankaɗa sameeha ta tafi taga taga zata faɗi kamar wace aka riƙo ta ta tsaya gam ta haɗe da saka kuka,zee dake kwance a kan kujera ta miƙe tsaye a hankali ta tako ɗas ɗas har daf da gaban Sameeha hannu ta ɗaga ta wankawa Sameeha mari masu zafi har sau biyu sameeha ta dafe kumatun ta da sauri haɗe da sakin ƙara me razanarwa zee ta kuma sa ƙafa ta kaiwa cikin sameeha duka,wani wulwula akayi da zee aka yarɓar jikin kujerar dake fallon ta faɗi a kan ƙafar da ta kaiwa Sameeha har wani ƙara ƙafar tayi tsabar bugun da zee ta sha momy ta nufo inda zee ta baje a ƙasa tana ihu da kiran momy!!! momy!!! momy!!…………………………
*Alhamdulillah,nasan fan’s yau zakuji daɗi anwa zee ƙafa ɗaya????*
_*By*_
_*Maman Dr*_