SAMEEHA R

_????SÂMÊÊHÂ????_*
(R)
Ya ƙarasu daf da ƙofar momy ta dakata da bugun ƙofar ta tsaya da bala’in da take yi Sameer yasa key ya buɗe ƙofar suka shiga cikin ɗakin a tare,ko da suka faɗa fallon basu iske kowa a cikinsa ba suka nufi cikin ɗakin da sauri suna dube dube nan ma wayam basu ga Sameeha ba suka kuma shiga ɗakin Sameer daya bari shima dai babu kowa cikin sa har momy ta buɗe baki zatayi magana kenan Sameer ya ɗaga mata hannu cikin hanzari alamar tayi shiru ƙarar zubar ruwa na ƙara kwaranya daga chan wajan fallon da suka baro,a hankali suka ƙara dawowa cikin fallon suna bin duk inda sautin ruwan ke tashi.
Cikin tafiyar sanɗa har suka isa daf da banɗakin dake cikin ɗakin Sameeha a dai dai lokacin ne ruwan ya tsagaita kwaranya daga cikin banɗakin ba afi ƴan mintina kaɗan ba aka fara ƙoƙarin buɗe murfin banɗakin har aka buɗeshi gaba ɗaya Sameeha tayi turus ganin su Sameer da momy a gabanta sun tsareta da ido kamar zasu bugeta cikin tsoro da firgita Sameeha ta duƙa a hankali ta ce””
“”Inaaaaaaaa,bata kai ga ƙarasa abinda take son faɗa ba momy tasa hannu ta finciko wuyanta daga cikin banɗakin suka fito har fallon ɗakin momy ta ce””
“”Me kika aikatawa Zainab a ƙafarta dame kikazo cikin gidan nan kika kassara min yarinya zaki faɗan ko sai jikin ki ya gaya miki yanzu yanzun nan.
“ki fara sakar mini rigata tukun kafin nabaki amsar abinda kika tambaye ni momy.
Eyeeeee lalai kan mage ya waye ni kike faɗawa haka Sameeha.
ki rabu da ita momy muga ƙarshen rashin mutuncin da ta iya ki sakar mata zanin ta faɗa mana abinda tayi wa Mya love daga baya mayi mata hukuncin daya dace da ita.
Wallahi bazan sake ta ba har sai ta sanar dani abinda ta ƙunsa ko aka ƙonso mata tayiwa ƴata Sameer kasan abinda nakeji a raina kuwa ƴar tawa guda laya tal a duniya ina bazai yuba ke dan Ubanki me kika yi mata,momy ta dawo da dubanta ga Sameeha dake tsaye tana kallonsu rai a matuƙar ɓace momy ta ɗora da'”
“””Ki hanzar ta sanar dani da sauri kar ki ja abinda baki taɓa tunanin zanyi miki ba maza ki karya abinda kike ƙula akan ƴata.
ni babu abinda nayi mata wallahi Allah ko taɓani batayi ba ku tambayeta idan nayi ƙarya dan Allah ku barni na tafi gidanmu bazan kuma dawowa ba har a bada.
Kalaman Sameeha shi ya ƙara tabbatarwa da momy yanzu ras Sameeha take tunda har tasan wacece ita tasan daga inda take, maganar kuma su saketa bai tasoba a haka momy ta janyo Sameehaa har cikin ɗakin ta sameer na biye da ita ta umarce shi daya samo igiya me kauri ya kawo mata cikin hanzari Sameer ya amsa da”to,ya juyo jikinsa har rawa yake ya fita.
kamar yanda momy ta umarci sameer da yayi hakan ya yi bai jima da fita ba ya dawo da igiya me kauri momy ta ce ya miƙo mata,kokawar ƙwace kanta sameeha ke yi momy ta riƙe ta gam tana ƙoƙarin ɗaura mata igiyar a dantsan hannayen ta ganin sameeha na neman ƙwacewa yasa sameer matsowa daf da su momy yasa hannu suka haɗu da momy suka danne sameeha suka ɗaure hannayenta biyu a waje ɗaya da ƙafafun ta suma a guri guda,kuka ta saka ta na haɗasu da Allah su barta batayi musu komai ba ta koma wajan Abbanta da Ummanta har Mona sai da ta ambata tana kuka tana roƙonsu momy ta ce da sameer ya koma chan inda zee ke kwance ya jireta an barta ita kaɗai sameer ya amsa ya fita bayan sun ɗaure sameeha tam da igiya.
“Laluban layar da momy ta soketa a jikin ta ta shiga yi,laya ta ce ɗauke ni a inda kika ajiye ni hankalin momy ya mugun tashi ta shiga zazzage komai na jikin ta sameeha sai kuka take tana roƙon momy ta barta ta tafi gida,ko ta kanta momy bata bi ba ta shiga dube dube tana neman inda layar ta ta faɗa hankali a tashe ba laya babu dalilinta dama kiran sarkin hatsabibai zata yi su san abinda zasu yiwa Sameeha a kuma binciki abinda ya samu zee laya tayi ɓatan damo, burkicewa momy tayi sosai ganin bata ga layar ta ba tasan masifa da tashin hankalin da zata faɗa na ɓatan layar gaba ɗaya momy ta rikice ta nufo waje da gudu ko ƙarasa fita waje momy batayi daga cikin ɗakin ba igiyar da suka ɗaure Sameeha ta fara kwance kanta da kanta ita kanta Sameeha sai da ta razana da ƙarfi aka umar ce ta da”””
*””KI TASHI DA SUNAN ALLAH KI FITA KARKI KUSKURA KI WAI WAYO BAYANKI KO DA ZAKI JI MURYOYIN DA KIKA SANI………..*
Da rarrafe Sameeha ta nufi ƙofar fita daga ɗakin bakin ta ɗauke da””
……………………………………
*KU BIYO NI A PAGE NA GABA DAN JIN YA ZATA KAYA????♀️*
*AFUWAN NA JINA KWANA 2 DA BAKUYI BA NA SHIGA WATA SAFGAR NE AMMA KUNA RAINA MASOYA NA????*
_*By*_
_*Maman Dr*_