SAMEEHA S

_????SÂMÊÊHÂ????_*
(S)
“”Laa’ilaha’illallahu Wahdahu la shareeka lahu,Allahu’Akbar kabeeran,walhamdulillahi katheeran,Subhanallahi Rabbil’alameen,’la haula wa la ƙuwwata’illa billahil-Azeezil-Hakeem._,Sameeha ke ta mai mai tawa da ƙarfi tana ƙara rarrafowa har ta fito fallon momy ta nufi ƙofar da zata kai ta harabar gidan a duƙe,Sameer na kusa da Zee yana aikin yi mata sannu kamar an tsikare shi ya ɗago kansa gilmawar abu kawai ya gani ya wuce yayi kamar zai miƙe tsaye ya duba sai kuma ya fasa ihun zee da gunjinta ya ɗauke tunanin sa ya dawo da duban sa ga zee ya cigaba da rarrashin ta yana daddana mata sahun ƙafar,duk inda momy tasan zata ga layar ta ta duba samma ko ƙassa bata ganta ba har ɗakin Sameer sai da momy ta bincike ko ina ta koma ɓarin sameeha shima ta
duba ko ina bata ganta ba,sake juyowa ɗakin ta tayi da wani tunani ya faɗo mata a rai ko ta mai da layar mazaunin inda take,”kai amma nafita da ita zuwa asibiti kuma tabbasa ban ciro ta daga jikina ba,bari dai na duba ƙasan gado ko na mai da ita ma’ajiyar ta,momy ta fito daga ɓarin Sameeha tayi nata ɓangaran ko da ta shiga fallon kai tsaye ta nufi ɗakin ta da sauri sauri ta shiga,mutuwar tsaye momy tayi kanta ya fara juyawa ganin igiya kaɗai a ƙasa babu Sameeha a ɗakin hantsilawa momy tayi haɗe da ƙwallawa Sameer kira ta miƙe da gudu ta nufo fallon shima Sameer dake a fallo ya nufo ɗakin momy a guje.
Gware sukayi da junna a dai dai bakin ƙofar shigowa ko wane ya ja da baya yana sosai goshin sa momy ta ce””
“Sameeha!! Sameeha Sameer,”Momy me ya ke faruwa me Sameeha tayi mike?
suka haɗa baki atare momyta sake buɗe baki ta ce””
“Ta gudu Sameer sam Bata cikin ɗaki ta fita wallahi ta gudu Sameer kayi sauri ka bi bayanta karta gudu.
Sameer ko amsawa momy bi yi ba ya juya a guje ya nufi bakin ƙofar get ɗin gidan momy ma ta rufa mishi baya su ka nufo get ɗin tare da ƙofar take a wangale alamar wani ya fita suna isa bakin ƙofar suka hangi Sameeha na gudu akan titi a gigice momy ta shiga kwarawa Sameeha kira Sameer ma ya fara kiran sameeha suna gudu suna kwara mata kira jin ana kiran ta yasa Sameeha ƙara ƙarfin gudun nata wata zuciyar tana ce mata”ki waiwaya kiga ko sun kamo ki,wata na faɗin”kar ki juya tunda an gargaɗeki,gudu sosai take tana dube duben inda zata faɗa ko wani mutum da zata nemi taimakon sa ga titin babu kowa kasancewar unguwar shiru shiru ce gidajen manya manya ne basu fi a ƙirga ba su Sameer suka biyo bayan Sameeha a guje suna kwara mata kira,ganin bazasu kamo ta ba yasa sameer komowa baya ya nufi gida a guje kamar zai tashi sama da gudu ya nufi motarsa da wani irin ƙarfi ya buɗe murfin ƙofar ya faɗa ciki ya tada motar haɗe da danne horn yana kwarawa baba me gadi kira dan jin kansa Sameer yake kamar wani ingarman zaki wani ƙarfi da fusata na shiga jikin sa zuciyarsa har bugawa take yana wani fusga shi kaɗai a motar ganin baba me gadi zai ɓata masa lokaci ya buɗe murfin motar a kunne ya fito ya barta ya ture baba me gadi da zuwansa kenan ya shiga ƙoƙarin janye get ɗin yana wani irin fuzar da iska daga bakin sa, ƙasa baba me gadi ya faɗa sameer ya janye get ɗin da sauri ya dawo mota da gudu ya sureta saura kaɗan ya bi takan baba me gadi baba me gadi yayi sauri ya mirgina gefe sameer ya fita da motar a sittin ya bi bayan sameeha har yazo ya wuce momy dake gudu tana kwarawa Sameeha kira data ga wucewar sameer ta shiga”
“Bi takan ta ka take kowa ya huta Sameer……
Wani ƙirrrrrrrrr motar Sameer tayi a dai dai jikin Sameeha da ta rintse ido ta ƙanƙame jikinta waje ɗaya Sameer ya fito daga motar a fusace ya chafki Sameeha da ta buɗe ido jin hannun mutum a jikin ta,cizo ta kaiwa Sameer da duka da hannu yayi charaf ya chafe hannun ya saƙalo hannun nata ta baya ya haɗe da ɗayan ya fara janta zuwa mota sameeha na tirjewa tana ƙoƙarin komawa baya sameer ya ƙara chakumar wuyanta azaba tasa Sameeha sakin wani irin ihu sameer yaji zata tara masa jama’a ya toshe bakin cikin sauri ya fusgota ya kuma tura ta cikin motar ya shige ciki, belet ɗin jikin motar ya fisgo ya fara kokawar ɗaure Sameeha tana gocewa har sameer ya samu damar ɗaɗɗaure sameeha da belt ɗin ya haɗa da ɗankwalin kanta ya toshe bakin ta ya jingina da bayan motar yana mai da numfashin wahala da ita ma Sameeha ke mai da numfashi tana kukan zuci da hawaye kaɗai yake zirarowa daga idanuwan ta.
Ƙara sowar momy wajan yasa sameer motsawa daga jingenan da yayi,ya buɗewa momy murfin motar ta shiga baya inda sameeha ke ɗaure ta zauna sai hakki take da idanun ta suka sauka akan Sameeha dake ɗaure a jikin motar Sameer ya tada motar ya juyo ya nufi gida koda isowar su gidan horn ya danna jikin baba me gadi har rawa yake ya zo ya buɗe get ɗin suka danna cikin gidan Sameer bai tsaya a ko ina ba sai a dai dai harabar ɓarin Sameeha ya tsaida motar ya buɗe ya fito ya zagayo mazaunin baya shima ya buɗe musu murfin momy ta fara fitowa shi kuma ya shige ciki,duk wata da bara da yasan Sameeha bazata iya ƙwacewa ba Sameer yayi ya tsinke belt ɗin daga jikin motar a ɗaure ya sunkuci Sameeha yayi cikin falon momy ta biyo bayansa,yana dire sameeha akan dandarrayar kafet ya fara ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa da sauri momy ta dube shi ta ce”
“Ka bar ni da ita ba sai ka doke ta ba Sameer ka koma ka zauna ka huta.
momy ki ƙyale ni wallahi sai na yi mata hukunci dai dai da abinda ta aikata mu zata rainawa hankali ta gudu.
Na san da hakan nace ka barta komai a hankali ake bi bada zafi zafi ba ko fitar da tayi ai ta wahala duk da muma ta wahalar damu ɗin.
shi yasa nace kai barni na jibge ta gaba idan ance ta tafita ko taku ɗaya baza ta iya ba dan Allah momy ki ƙyaleni na hukunta ta ko zuciyata zata samu salama.
ajiyar zuciya momy ta sauke ta dubi Sameer ta ce”
“Sameer!
Na’am momy.
bani nace ka ƙyale ta ba kasan me na tanadar mata.
A’a momy.
to ka rabu da ita tun da ni nace haka nasan matakin da zan ɗauka yanzu ka nemi waje ka zauna ka jire min ita ina zuwa dan bazamu ƙara barin ta ita ka ɗai ba akwai me son taimakon yarinyar nan a ɓoye kuma wallahi sai na ganoshi ko waye shi a ƴan kwanakin nan.
guri sameer ya samu ya zauna kafin haka sai da yasa ƙafa ya shuri Sameeha da ke ɗaure a zaune momy ta miƙe ta fita dag fallon ta koma nata ɓarin,ko da shigarta fallon a ƙasa ta iske Zee ta faɗo daga kan kujera har bacin wahala ya ɗauke ta momy ta gyarawa zee kwanciyar ta ta sa mata matashin kujera ƙafar zee ɗin ta kalla ta miƙe da sauri tayi ɗakin ta ƙarƙashin gadon ta nufa da zuwa ta durƙushe a dai dai inda ma’ajiyar ta,take ta leƙa ta zaro wannan tukunya ta hangi layar a gefan ƙwaɗon sai baki yaƙe buɗewa yana ɗif ɗif ɗif da maƙogwaronsa momy ta dafe ƙarjinta haɗe da furta”
“Amma kuwa na auna arziƙi,ashe duk walar danake kina nan ma ajiyar ki kai amma ko naji daɗin da bantaɓa jin irinsa ba Sameeha gareki, momy tayi ƙwafa ta mai da tukunyar inda take bayan ta damƙe layar a hannu ta miƙe tsaye tayi kicin,kaskon wuta ta ɗauka ta lalubi inda ƙatuwar muciyar gidan take ta ɗauka ta duba inda duk kayan dakan ta yake taje ta ibo barkono daga ma’ajiyarsa da yawa ta kantami gishiri da leter ta sake ɗaukar kofi da cokali ta fito daga kicin ɗin ta koma nata ɗakin,irin gwayin nan ta ɗauki ledarsa guda ɗaya ta fito tayi ɓangaran sameeha tana murmushi a bayyani,koda ta shiga fallon umarni ta bawa sameer daya fita ya sayo mata omo jakar sa guda ya kawo,sameer ya amsa da to ya fito daga ɓarin ya ɗauki motars ya fice daga cikin gidan.