SAMEEHA S

layar momy ta fiddo daga hannun ta ta mai da ita hannun haggu ta matseta da ƙarfi haɗe da kiran sanun Sarkin hatsabibai sau uku kan ta rufa baki har Sarkin hatsabibai ya bayyana cikin wata iriyar shiga me munin gani da ban tsoro sai muzurai yake yana furzar da baƙin hayaƙi daga bakinsa.
******
“Maimuna yi sauri mana ki fito mu leƙa Allah zanyi tafiya ta na barki kin san bana son jira.
“gani nan Umma mayafi na nake nema ban ganshi ba.
to dole sai mayafin zaki saka ki ɗauki hijabin ki mana na makarantar ku ki yafa wallahi yafi miki kyau nesa ba kusa ba da mayafin nan gashi komai naki a rufe banda iyayin ki ma maimuna ina ke ina mayafi.
lah ai kin gan shi ma umma ashe yana sif ɗinki ba nawa ba.
to ai sai ki fito mu tafi tunda kin ganshi ba surutu na tambaye ki ba kinga yaya jummai na jiranmu kin san halinta sarai idan tayi ƙorafi bamu isa akan lokaci ba dake zan haɗa ta.
wai rufa min asiri umma masifa irin ta yaya jummai ai batayi ba wallahi ko hutawa bata yi idan ta fara kamar karatu,mona ta fito tana yafa mayafin akan ta umma ta dube ta tace””
ke kinko ji warin da mayafin nan yake yi maimuna ko babu hanci a fuskar ki ne.
laha’illah wallahi sai yanzu naji warin Umma ya kwana biyu ban yafashi ba Allah sarki tun Abba na da rai,mona ta ƙare batun da fidda ƙwallah daga idanun ta,dubanta umma tayi ta haɗe rai ta ce””
za’a fara ɗin ko.
kai umma dan Allah.
ki wuce muje karki ɓata mini rai da ranan nan.
bari na ɗan fesa tiraran da Momy ta baku kaɗan zai gusar da warin dan Allah umma bazan jima ba.
kai kai maimuna anya kuwa.
ɗan fesawa kaɗan zanyi ba da yawa ba kinji ummata ta kai na na fesa ɗin?
amma karki daɗe kina wuce minti ɗaya Allah kya biyo ni a baya.
yauwa Ummata ko sakan bazan wuce ba yanzun nan zaki ga na fesa na fito,a gudu mona tayi cikin ɗakin umma tana dariya turaren guda biyu na ajiye a miron Umma mona ta kai hannu kan wanda Abba ya fesa ta ɗauka ta shiga fesawa a ko ina na mayafin har jikin kayan ta tayi sauri ta dangwarar da kwalbar turaran tayo waje…
Kai kai kai Maimuna kwalbar turaran kika feshe a jikin ki ko yaya,umma ta toshe hancin ta tana matsawa gaba da inda mona tazo ta tsaya mumushi mona tayi ta shaƙi ƙamshin daya bugu hancin ta har cikin maƙogwaran ta ta lumshe ido ta ce”
Gaskiya Umma ƙamshi yayi a rayuwa kin ko ga ɗan abinda na fesa,kaɗan na fesa fa amma ji yanda ƙamshin turaren ya game ko ina ko banza yau ni ma na buɗa kamar Ƴar maiduguri.
dayake an ce miki turaran kwalba suke bulbulawa jikin su wallahi har cikin bakina nake jin sa oh yau naga abu.
Umma muje kina tsayar damu.
Ƙaniyar ki Allah dana sani ban jira ki ɗin ba.
dariya mona ta sake sakaya ta dubi Umma da ita ma umman take du banta tace””
Umma ta tawa ta kaina wallahi ina sonki umma ina Addu”a Allah Ubangiji ya rayamu cikin ƙoshin lafiya da wadata na kai ki makka da madina na saya miki duk abinda kike so ke kaɗai ya rage mana,sai kuma siraran hawaye suka biyo baya jikin Umma ne gaba ɗaga ya mutu ta kasa cewa komai banda ƙwallar data cika mata ido ta kama hannun mona suka fito waje tasa mukuli ta rufe gidan suka jira atare suka nufo titi……….
_*By*_
_*Maman Dr*_