NOVELSUncategorized

A GIDANA 16

 Shafi na Sha Shida

 A hayarsu ne yana tafe sundanyi shiru, kallanta yai yace “Yau Honey ba bacci sosai.”
 Kallansa tai tace “yanzu na daina ai, waccen zuwan nasu kaga na damu?”
Murmushi yai sannan yace ” Dadyn fa? Haryanzu bakwa ko waya?”

Yanayin fuskarta ne ya canza ta juya kanta zuwa jikin window.
Dariya yai yace “sorry Honey bansan ya akai zancen nan ya fito daga bakina ba.”

 Bata tankamai ba har ya kara cewa “Honey ina Kwaro yaje ne?”
Kallansa tai fuskarta haryanzu ba a sake ba tace “yaje wani guri ne.” Ta rasa meyasa ta samu kanta dakin fadamai babanshi ne baida lafiya.”
Kafin yace wani abu tace “Sadiya fa?”
Kallanta yai da sauri, tace “menene? Da matsala ne?”
“A’a tana makaranta inta gama zata kirani.”
To kawai tace tai shiru, suna zuwa ta sauka ta shiga shiru yai yana kallanta harta shiga ciki.

 Office din editing ta fara shiga ta duduba ta wuce office dinta.
Shiru tai akan kujera tana kallan takardun da zata duba, waya ta dauka ta kira ciki, kace tazo.
Nan ta ajiye wayar, Ramlah ce ta kwankwasa, Zainab ta bata izini ta shigo.

 A tsorace ta gaisheta, Zainab ta kalleta tace “ina report din danace ki kawon?”
Ramlatu tace “Am sorry yanzu nake karasa editing.”

 Wani wulakantacen kallo ta mata tace “yanzu kike me?”

 Yawo ta hadiya ta kalleta tace “banida lafiya……..”
 Bakida lafiya? 
A tsorace ta daga kai, Zainab ta dau wayarta ta kira director sannan tasa wayar a handsfree tace “Sir wannan wacce bansan ta yanda akai ta samu aiki anan ba.”
Daga can cikin rawar jiki yace “Ramlah?”
Tace koma wa sunanta bai damenba sai dai kai da ka kawota inaso ka sanar da ita wannan shine dama na karshe da zan bata, idan harna kara bata aiki batamin zata taradda takardar kora a saman kafarta.”

 Director ya canza yanayin maganarss yace “Yahkuri Zainab, ni kaina bansan amfaninta ba, kiyi hakuri zan ja mata kunne.”
Bata bashi amsa ba ta kashe wayarta, kallanta ti tace “dafatan kinji?”

 Ramlatu wace ranta ya gama baci da yanda Director ya wulakantata yasa ta saukar da kanta kasa, Zainab tace “banida damuwa da duk iskancin da zakiyi, am i your mother? Ko nice babanki? Banida hadi dake rayuwarki ce sai dai inzakiyi iskancinki kije kiyi a hotel amma nan gun aiki ne, idan baki kawon report din nan in an hour ba bansan me zai biyo baya ba, Get out.”
Ta nuna mata hanyar kofa, Ramlatu tana hawaye ta fita, tana fita ta shige toilet tasa kuka.

 Zainab kam tana fita taja tsaki, ranta ya kara baci, wani abu ta hadiya na bakin ciki, maimakon ta duba takardun dake gabanta kwantar da kanta tai tare da rufe idanunta.

 Mahaifiyarta ta hango kwance a kasan tiles, ga jini a malale ta kasanta, ita kadai a gida babu kowa, hawayene suka gangaro ta gefen idanunta wanda batabi ta kansu ba, hangota tai a rikice tana kuks ta rasa ta yanda zata taimaki Ummynta, kusa da ita kawai taje tana kuka tare da rike hannunta.
 Kuka take sosai, a hankali Ummy tace “Uwata ki dsu wayata ki kira Kamisu driver.”

 Kalan cikinta wanda taketa murna zata samu kani ko kanwa tai, a tsorace tace “Ummy! Ummy…..”
Jinin dake zuba ta kalla da sauri taja wani wahalalen numfashi sannan ta bude idanunta tana hakki.

Bakinta ta shiga motsawa tana kokarin maida kukan dake neman kwance mata ta shiga kokarin yi, da sauri ta jawo takardun dake gabanta ta fara dubawa.

 Wayarta ta daga ta kira Sabir, daga can ya amsa yace “Zee!”
Tace “ya? Ya kiraka?”
Eh tun dazu harna gama na dawo office dina, hatsari yai ne?”
I don’t know.
Yace “okay, amma meye hadinki dashi? Shine mijin naki?”
Dan karamin tsaki tai tace “kaifa matsalata dakai tambayar abinda baishafeka ba, nagode.”
Bata jira mai zaice ba ta kashe wayarta.

 Harkarta ta cigaba dayi, sai dai kasan ranta a ciki yake da tausayin mahaifiyarta da kuma tsanar mahaifinta.

鈥�************

 Sai yamma lis sannan ta koma northwest ta naka ma Adam kira, yana zaune a majalisa ana hira yaji wayarsa tai kara, mikewa yai da sauri ya matsa sukasa mai dariya Yaran Hajiya ya amsa kira.

 Adam yace “kingama?”
“Eh yaya nagama.”
Okay bari na taho.
Ya kashe wayar ya musu sallama, da sauri ya fada motarsa ya shiga y nufi makarantar.
 Tana bakin inda ya ajiyeta, yana yin parking ta shiga ta zauna, juya kan motar yai suka fara tafiya ba tare da kowa yayi magana ba, can sai da suka danyi nisa tace “Yaya nagode sosai.”
Ya kalleta yace “bakomai, kingama ko?”

 Tai shiru tare da yin kasa dakai, kallanta ya sakeyi yace “baki gama ba?”
Kai ta daga alamar eh tace “bangama ba yaya, kayi hakuri.”
Dariya yadanyi kadan yace “hakurin me? Ki zauna ki karasa a hankali, gobe zaki koma kenan?”
Tace “gobe Friday kuma ko naje ba zan iya gamawa in bazan takurama ba inasan in bari sai Monday.”

 Adam ya kalleta, kasa tai dakai tace “yaya kayi hakuri.”
Da sauri yace “bakomai, kizauna sai monday din.”

 Shiru suka danyi kafin tace “Yaya kayi hakuri akwai lokutan da zakaga ina abubuwan da basu dace ba dan Allah inkaga haka kayi hakuri kamar yanda nacema rannan inada larura ne wlh wanda nikaina bana sanin abinda na aikata.”

 Kallan ta yai har yadansa tari yace “aljanu?”

 Dariya tai jin yanda yai maganar, tace “a’a ni kaina bansan menene ba, saboda hakan ansha min duka.”

 Duka? Ya tambaya tare da dan kallanta.
Tana wasa da hannunta tace “eh yaya, kayi hakuri.”
Idanunta ne suka ciciko jiyai tausayinta ya kara kamashi, yace “ya isa hakanan bansan yawan kukan nan.”

 Share hawayenta tai da sauri tace “nadaina, duk abinda bakaso bazan sake yi ba.” Tai maganar tana girgiza.
 Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yace “to.”
Wani dadine ya kamashi a kasan ransa, yau gashi shine yake bada umarni ya saba a komai sai dai shi a bashi.


********
Ganin jikin Abba ya dawo daidai yasa Khalid ya fito yai ma Umma sallama akan sai ya dawo, kallanta yai yace “zan tambaya in za’a iya biyana da wuri inyaso sai na baki saboda yin abinci ga yan kananan kudadanen da ake amfani dasu a asibitin.”

 Tace “To khaleed, sannu Allah ubangiji ya daukaka ka, ya baka damar da zaka taimakemu.”
Yace Ameen.
Asiya ya kalla yace “in na dawo Umma zata koma gida dan haka kije gidansu Salmanu, kafin nan, ko kuma ni nace yazo ya zauna a dakina kafin na dawo.”

Umma tace “yazo din yafi sauki sauki.”
Yace to, sai na dawo.

 Fitowa yai ya dau hanya, bai tabajin dadin aikinsa ba irin yau, a da ya dauki aikin ne akan rashin abinyi, sai dai taimakon data mai yau tabbas yass ya kara girmamata a idansa, haushi ne yadan kamashi da ya tuns ba yanda zaiyi ya kama wannan mutumin.

 Haka ya isa station din har lokacin fitowarta yai.
 Zainab na fitowa ta hango motarta, karasawa tai ta shiga tare da ajiye kayan dake hannunta.

 Khalid ba tare da ya juyo ba ya dan kalleta ta madubi kadan, gaba daya yanayin damuwa ne karara a fuskarta, daurewa yai yace “Nagode sosai da sosai.”
Kallansa tai tadanyi murmushin yake tace “is okay.”

 Shiru yadanyi kafin yace “jikin nashi da sauki.”
I know, abinda tace kenan ba tare da dogon nazari ba.
Khalid yace “kin sani?”
Shiru tai cikin waskewa tace “tunda kaje asibiti i will assume that.”
Oh yace sannan ya tada motar, shiru tai ta zubawa window ido, yauce rana ta farko dayaga bata aiki a cikin mota, da alama an bata mata raine, ko mutumin nan ne? Abinda ya fado mai kenan, shiru yai yana tunanin yanda zaiyi ya tambayeta, daurewa yai yace “wannan ya sake kira?”

 “Wa?”
Daga yanayin tambayarta ya fahimci baisake ba, shikenan.
Jin yace haka yasa ta fahimci yanayin da take, juyawa tai ta dau tab dinta tana dubawa duk da dai ba wani abu take ba amma batasan ya fahimci tana wani halin.

 Yana sauketa ta wuce ciki, Goggo na zaune a falo tana waya da alama wannan bikin daya ishemu shi take magana akai, wanda mu kanmu mun kosa asabar tayi wato jibi a gama bikin nan mu huta.

 Zainab bata tsaya a falo ba wucewa kawai ciki tai, Goggo ta bita da kallo, Sadiya dake daki a kwance ma batasan ta dawo ba.

 Adam ta gani kishingide yana kallo a laptop dinta, yana ganinta ya taso da sauri yace “Honeyyy….”
Ya bude hannayensa alamar rungumeta, hannun tadan ture ta wuce toilet, tana fitowa ta ganshi a inda ta barshi ya shagwabe yace “Honeyyyy….” ya kara bude hannu.

 Murmushi tai sannan ta shiga jikinsa ya rungumeta, dagowa tai ta kalleshi sannan ta canza kayanta, yace “Honney su Nabila sun isa?”
Ta kalleshi tace a’a kawai, fitowa falo tai ta nufi kitchen.

 Sadiya wacce ta fito dan cin abinci itama suka hadu da Zainab, Kallanta Zainab tai cikin mamakin ganin kayanta a jikinta.
Sadiya ce ta kalleta tace “Aunty menene?”
Zainab tace bakomai, flask din ta rufe ba tare da ta zuba abincin ba, Sadiya ta fahimci me ta gani hakan yasa yace “Aunty nagode Yaya ya ban kaya inji ki.”

 Zainab ta kalleta kawai tai murmushi ta wuce ciki.

 Goggo ta bita da harara tace uwar mijinki na zaune amma ko gaisheta da gida bazakiyi ba, in dazu kin shigo ina waya yanzu fa.

 Zainab na shiga ta kalli Adam tace “yaushe ka ba Sadiya kayana ban sani ba?”

 Kallanta yai da sauri yace “Honey dama naga zata skul ne batada abinda zata saka shiyasa.”
Meyesa baka fadamin ba to? Kafi kowa sanin bazan hana kanwarka abu ba amma at least nasan meke faruwa.”

 Adam ya jawo hannunta yace “Am sorry Honey, gani nai da abuna da naki dayane.”

 Shiru tai kafin tace “meyasa in ina cikin wani hali baka taba ganewa harsai na fadama?”

 Cikin mamaki yace “‘menene?”

 Kallansa tai tace “baka kula da yanayi na ba tunda na dawo?”

 Murmushi yai yace “ai kin saba wani sa’in haka kike shigowa a gajiye, zo kiga na nuna miki nawa mukaci a ball din da akai yau.”

 Baki ta bude kamar zatai magana sai ta fasa.

 Fitowa tai ta wuce dakinsu Nabila ta rufe, zama tai a kasan carpet ta sa kanta akan cinyoyinta…….

Goggo ta girgiza kai a kufule, Sadiya ce ta kalli Goggo tace “Aunty bata kula damu bane hala.”

 Goggo tace “ina fa tsabar iya iskanci ne.” Taja tsaki.

Zainab tai shiru…..
Abinda ya faru a shekarun baya ne suka dawo mata…………….

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button