SARAN BOYE 75

      Tone-tone dai kam an yisu a ranar game da sirrikan papa masu ban mamaki da tsoro. Hakan yasa su Jay fahimtar riƙe su Yoohan bazai taɓa saka Papa kawo kansa hannun hukumaba. Dan haka suka sallamesu su koma gida kawai. Dan aikine babba wannan ya wuce wasan yara. Shi dai Gebrail yaji daɗin barinsu da akayi. Yoohan kam gaba ɗaya kansama ba aiki yakeba a wannan lokacin. Dan brain ɗinsa ta toshe.
         Tun a wannan daren ƴan jarida da masu alhakin faɗin albarkacin baki suka fara kayayatu. Inda ƙungiyar catholic tai azamar fara fitowa ta banbanta tafiyarta data goshpower. Sun tabbatarma duniya bada yawunsu ko saninsu yake aikata duk wannan al’amarin ba. Hakama gwamnan jiharsu da manyan ƴan siyasa sun fito sun nisanta kansu da papan kai tsaye.
     Tofa abin magana ya samu lallai da gaske. Dan ƙasar tuni ta ɗauka tare da kafafen yaɗa labarai na televisions da redios. Yanar gizo dama duk wata kafar maida yanda akayi. Videos ɗin da wasu a cikin ƴan ƙauyen sukai ƙarfin halin ɗauka tuni ya fara yawo a yanar gizo. Yayinda ƴan jaridu suka fara tabbatar da cewar mafi yawan yaran da aka samu a gidan nasu papa yarane da aka sata daga arewacin ƙasar. Ƙalilanne a cikinsu suka fito daga kudanci. Tofa magana ta girma.

__★★

        Baba malam ne ya fara cin karo da wannan babban al’amari a labaran ƙarfe goma na dare da yake kallo. Sai ga Nu’aymah data shigo kawo masa shayin da rabi ta dafa masa dan baya iya cin abinci sosai itama ta ganema idanunta.
     Da ga ita har baba malam ɗin kasa magana sukai, sai tv da suka zubama idanu da tsananin mamaki da al’ajabi. Ganin tayi tsaye ta kasa zama baba malam yace ta zauna saboda ba ita kaɗai bace. Zama tai a kujera jikinta har rawa yake saboda ganin yanda aketa bata kashin ruwan harsasai a ƙauyen su papa da aka nuna. Idonta bai ganar mata Yoohan ba sai lokacin da akaje family house ɗinsu. Anan kuma Umm ma ta fito ta samesu. Duk da batajin ƙarfin jikinta itama saita zauna zaman kallo.
       Can sai ga Hajjo a rikice itama ta shigo tana ƙwalama baba malam kira. Sai da Rabi ta sanar mata yana falonsa sannan ta nufo nan. Tunkan ta shigo ta fara faɗin, “Ɗan malam kaga kuwa tsiyatakun da aka tono yau na surikinka?”. Tana ida shigowa taga suma abinda suke kallo kenan ta shiga tafa hannu da jera salati. A kusa da Nu’aymah ta zauna suka cigaba da kallon tare.
       Kafin kace mi sai ga kiraye-kirayen waya sun fara shigoma Baba malam a wayoyi. Yasan kwanan zancen, dan haka yaƙi ɗaga wayar kowa. Kansama gaba ɗaya sai ya ƙara ɗaukar zafi. duk da yasan papa riƙaƙen ɗan harƙalla ne baiyi xaton al’amarin ya kai haka girma ba. Dan yasan papa ne shekaru ashirin da takwas da suka shuɗe a jami’ar ƙasar France, lokacin yana haɗa degree ɗinsa na biyu a can. Shima papan yazo ne wani course na wata tara. Tunda yazo makarantar a tantirinsa yazo dama. Dan karatunma asha ruwan tsuntsaye yake masa. Duk wasu abokan banza zaka samu papa da su, dan adalilin takurama wata yarinya mai suna Sadiya ƴar ƙasar Niger da papan yayi akan dole sai tayi soyayya da shine ya zama sanadiyyar sanin juna da sukai da baba malam ɗin. Kasancewar baba malam shine shugaban mss na makarantar a lokacin duk da ba wani ƙarfi ne dasu ba sai yay tsaye a kan lamarin papa da Sadiya. yayma papa gargaɗi sosai akan ya fita harkar yarinya ya barta tai karatunta. Idan ba hakaba kuma zai ɗauki mataki a kansa. A lokacin papa baice komaiba sai dariya da suka shiga sheƙawa shi da yaransa suna busama baba malam hayaƙin taba da suke sha. Baba malam dai ya ja musu gargaɗi ya kama gabansa. Ba’a rufa wata ɗaya da wannan al’amari ba tsakanin papa da baba malam sai baba malam yaga wai papa  ya zama Pastor. Harma yana kula da church ɗin cikin jami’ar. Abin ya ɗaure kan baba malam sosai, dan ya fahimci lallai da biyu goshpower ya samo wannan muƙamin.
      Baba malam dai baice komaiba, dan sunama haɗa kwanaki sama da takwas basu haɗuba kasancewar kowa da sabgar gabansa. Sai dai tunda Goshpower ya zama Pastor a cikin jami’ar ƴar tsama mai ƙarfi ta shiga tsakaninsa da baba malam. a kuma lokacin akaima Sadiya fyaɗe tare da kasheta. Wannan al’amari yayi masifar girgiza baba malam dama sauran musulmai da suke a jami’ar. Dan kowa yasan goshpower ne zai iya aikata hakan ga sadiya. Su baba malam sun kai ƙararsa ga hukumar makaranta, an kuma amshi ƙorafinsu a zahiri, amma babu alamar za’a ɗauki wani mataki. Hakanne ya harzuƙa zuciyar baba malam yaje ya samu Pastor goshpower da kausasan maganganu. Amma abin mamaki ko ɗar papa baiyiba. Hasalima da bakinsa ya sake jaddadama baba malam cewar shine yayma Sadiya fyaɗe ya kuma kasheta. Tunda taƙi yarda ta bashi kanta da arziƙi shiyyasa ya ƙwata da ƙarfi dan yana ƙwaɗayinta sosai. Kasheta kuma da yayi yayine dan yaga mi baba malam ɗin ya isa yayi?.
       Baba malam akwai zuciya, hakan yasa a take ya fara dukan goshpower da iya ƙarfinsa. Kafin kace mi makaranta ta ruɗe da ihun ɗaliban dake ta wajen da abin ke faruwa. Kowa yayi mamakin yanda baba malam ke dukan goshpower. Dan babu wanda yay tsammanin zaiyi wannan ƙarfin. Musamman da ake ganinsa shiru-shiru baida kwaramniya sam a cikin ɗalibai. Hasalima ko ƙwaƙwaran aboki baida shi. Jina jina baba malam yayma papa a wannan lokacin, dan da ƙyar security ɗin makaranta suka amshi goshpower a hannun baba malam. Harma wasu na tsammani da zaton papa ya mutu.
     Kwana biyu da yin wannan rikici abin mamaki sai ga takardar sallama baba malam ya samu daga hukumar makaranta. Babu wanda yay kiransu ya zauna dasu domin neman ba’asin yanda akayi? Musulman ɗalibai dake makarantar hankalinsu ya tashi akan wannan rashin adalci da akaima baba malam. Amma sai shi baba malam ɗin ko a jikinsa. Dan dama koda basu koresaba yayi alƙawarin bazai ƙarasa karatunsa a wnann makarantarba, tunda har za’a iya kashe rai suƙi nutsuwa suyi ƙwaƙwƙwara bincike akai su gano mai laifi su yanke masa hukunci. Tunda baba malam ya baro jami’ar France bai sake haɗuwa da goshpower ba sai a sanadin Yoohan. Wannan shine dalilin da yasa yay matuƙar mamaki akan papa bai isa haihuwar Yoohan ɗin ba sam. Sai dai kamar da Yoohan ke ɗanyi dashi ya sakashi yin shiru da tunanin ko acan wajen yima ƴaƴan jama’a fyaɗen ya samosa. Sai dai zuciyarsa sam bata yarda da wannan tunaninba. Musamman da yaga yanda Yoohan ke da ƙyawawan halayya abin koyi. Sai gashi a hankali ya fara fahintar akwai wani ɓoyayyen al’amari dake a tsakkiyar papa da Yoohan, daga hakane ya fara burin saka ido aka lamarin papa ta hanyar Nu’aymah da wasu ɓoyayyun hanyoyi nasa. To binciken nasa bai gama kaiwa inda yaso ɗinba Jay yazo masa da tambayoyi akan Yoohan ɗin shima. sai dai shirin nasu akan binciken papa ɗin bai ƙarasa kaiwa can ɗinba gashi ɓoyayyun halayen papan sun fito a idon duniya.

        Tun a dare Nu’aymah ta shiga neman Yoohan amma ta gagara samunsa sam. Sai washe gari tana idar da sallar asuba ta kuma gwadawa anan ta samesa. Hankalinta ya tashi dajin muryarsa. Ta tabbatar masa ita dai zatazo abujan tunda taji kamar baida lafiya. Amma sai ya lallasheta akan tai haƙuri ta cigaba da zama a kano dan gidansu bazai zaunu a garetaba yanzu kodan halin da take ciki. Bazai yuwu taita ganin tashin hankaliba. Jin yanda yaketa lallashin natane yasa taɗanjin sassauci. Daga haka ta kira Umar dan ta ɗan ƙarajin bayanai. Shine ya tabbatar mata da karta damu Yoohan ɗin yana cikin ƙoshin lafiya damuwar abinda ya faruce kawai. Hakan kuma dolene a garesa tunda al’amarin yazo masa a bazata.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button