SARAN BOYE 75

     Baba malam ma ya kira Yoohan yay masa nasiha da kwantar masa da hankali, tare da faɗa masa yayta addu’a a ransa ALLAH zai sauƙaƙa musu waɗanan jarabawoyi da suka samesu a kusan lokaci guda.

★★★★

       Jami’an tsaro sun cigaba da neman papa, tare da zaƙulo dukkanin abokan harƙallarsa ta ƙarƙashin ƙasa. Harma waɗanda suke a ƙasashen ƙetare. Yayinda zancen yara da ake zargin mafi yawansu ƴan arewacin ƙadar ne ya tabbata. Wasu tun suna yara aka satosu, wasu ko suna a manyansu. An saida wasu ga masu buƙata. Wasu kuwa ana kaisu wasu ƙasashen ƙetare batare da sauran sunsan mi suke yi acan ba.
    Yarinyar da aka tattauna da ita tace, shekararta tara kenan a hannunsu. An satota ne a jihar Jigawa bisa hanyarta ta dawowa daga makarantar islamiyya a wani yammaci ranar litinin. Tana kuka tace, “Wani abu suka shaƙamin, wanda yasa ban sake sanin ina kaina ya keba sai a wannan gidan da kuka ganni a ciki. A randa na dawo hayyacina abinci kawai aka bani naci wani ƙato ya haikemin yaymini fyaɗe. Naga tashin hankalin rayuwa kala-kala a wannan tsakani, dan saida ta kasance kullum sai mutumin nan yayi amfani dani. Bai barniba sai da aka tabbatar da na samu ciki sannan. Sai a lokacin na fahimci ashe duk macen dake gidan hakane ke faruwa da ita. Waɗanan gardawa zasuyita amfani da ke ne har sai ka samu ciki. Ka gama wahalar rainon cikin a randa ka haihu a ranar za’a ɗauke yaron, watama ko ganin fuskar ɗan nata batayi. Kina haihuwa da sati biyu waɗan nan maza zasu koma yi miki fyaɗe har sai kin sake samun wani ciki”.
    Kuka ya sarƙeta ta kasa ci gaba. Sai da tayi sosai wasuma a jami’an tsaron na tayata, harma da ƴan jaridar dake ɗaukar rahoton. Da ƙyar ta cigaba da faɗin, “A shekara tara dana samu ni yanzu haka haihuwata takwas, dan duk shekara ƙa’idane sai ka haihu, a yanzu hakama satina baifi shida dayin wata haihuwarba. Bana tantama kuma ƙila na ƙara samun wanu cikin ma”.
       Ai Yoohan baima san sanda ya fashe da kuka ba, dan tunda yake a rayuwarsa bai taɓa cin karo da makamancin tashin hankali irin wannan ba. Sai gashi wai mahaifinsa shine tushen aikatawa. Abin takaicima harda sanin Momynsa. No wander ta mitsike idonta ta nema yin tarayya da shi duk da shiɗin ɗanta ne. A yanda yakejin zuciyarsa game da waɗannan yaran koshi ya ga Papa da Momy sai ya ɗaukesu ya damƙama hukuma ya rantse da ALLAH kuwa.


      A kano ma dai su Abban Abdallah na cigaba da kasancewa a hannun kulawar likita. Duk da dai jikin nasa kam dai babu ƙyan gani dan gaskiya yanajin jiki, dan har yanzu baya iya gane kowa dake a kansa. Addah ma dai jikin nata wataran yayi sauƙi wataran yayi tsamari. Duk da tsiyatakun da suka tafkama baba malam kuma bai gaza wajen fidda kuɗaɗen da ake kula da lafiyarsuba. Sannan shiketa tausar ƴaƴansu da zantuka masu taushi, tare da ƙoƙarin ganin wannan al’amari ya zama sirri a tsakaninsu batare da sauran jama’ar gari sunsan tushensu ba.
     Abban Mustapha dai ya riga ya saki Addah, sai baba malam ya hanashi faɗa mata ita da ƴaƴanta, sunbar maganar a tsakaninsu su manyan har sai ta samu lafiya kamar yanda baba malam ya roƙa mata alfarma. Dan yanzu bai kamata a haɗa mata zafi goma da ashirinba musamman daya kasance tayi nadamar kurakuranta. Halin datake ciki kaɗai ya isheta tashin hankali mai tsanani ai.
       Aikoda gaske tashin hankalin da Abban Abdallah da Addah ke ciki ko shi kaɗai kam ya ishesu. Dan suna cikin tsananin azabar ciwo da magauta. Duk taurin zuciyarka ka gansu dole ka tausaya musu kuwa.

     Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa. Su Adda ba faman jiyya a asibiti, jami’an tsaro na neman su papa ruwa a jallo. Masu maida yanda akayi na cigaba da tattaunawa da ƙara gishiri da magi akan al’amarin. Yayinda ƙungiyar kiristoci ma ta fito ta nuna cewar bata goyon bayan papa sam, sannan bata tare da shi. Hakama Pastors nata sharhi akan papan da tabbatarma duniya wamnan ba halin kirsata na ƙwarai bane aka samu papa da shi, dama suma ba ƙaramin matsi suke fuskanta daga garesaba ta ƙarƙashin ƙasa.

     Duk wannan cece kuce da ake famanyi suna shiga kunne papa a maɓoyarsa shi da mike, Anthony, Joshua da Solomon, sai madam Chioma. Abinda yasa aka gaza samunsu shine ajiye duk wani layin wayarsu da sukayi, dama duk abinda zaisa a iya bibiyarsu. Godwin da sauran ne ke a hannun hukuma. Duk wahalar da sukesha kuma sunƙi faɗar ina za’a samu su papa saboda basu saniba suma.

    Haka dai kwanaki suka cigaba da shuɗawa har Yoohan ya bar ƙasar saboda aikinsa, Nu’aymah ta cigaba da zama anan Nigeria bisa shawarar da baba malam ya bama Yoohan ɗin. Dan rashin kama su papa ba ƙaramin haɗari baneba. Musamman daya kasance Nu’aymah tana ɗaya daga cikin mutanen da a yanzu haka suke a cikin mummunan ƙudirinsa ita da baba malam ɗin. Yoohan kuwa yaji wannan shawarar duk da baiso yin nisa da iyalinsaba. Itama kuma Nu’aymah taji daɗin haka duk da kewar mujinta na tare da ita. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa cikin rahamar UBANGIJI da jin ƙansa.
       Cikin Nu’aymah ya shiga watan haihuwa, aiko su Umm nashan raki sosai da taɓara, Hajjo taita mata dariya da kiranta ragguwa. Yoohan kansa yanashan nasa shagwaɓan ta waya. Inko yazo ƙasar kuka rurus take tasasa a gaba tanayi wai itadai ta gaji wlhy a cire mata cikin nan. Takan bashi tausayi da dariya, sai dai bayayin dariyar sai yayta lallashinta da nuna nata tayi haƙuri saura ƙiris ai.
       Ai ko zuwan ƙarshe da yayi yay kusan sati ɗaya sannan ya koma, kamar jira Aymah keyi ya wuce washe gari ta tashi da naƙuda. Wayyo zo kaga raki wajen masu haihuwa. Yoohan har ALLAH ya isa sai da yasha a wannan ranar????, takuma rantse bazata sake yarda da wani cikiba dan wannan haihuwa daga ita bazata sake ba. Tun hajjo dake tare da ita a asibiti itada Mama amaryar Abba Musbahu na danne dariyarsu har suka kasa saida sukayi. Baiwar ALLAH tako sha wahala sosai, har dai ALLAH ya sauketa lafiya ta sunkuto jaririnta dake ta faman canyara uban kuka.
        Su Dr Aysha sun gyarata tsaf da bata dukkan kulawa kodan darajar mijin aurenta da iyayenta. Shima yaro aka gyara shi tsaf sannan aka fiddoma su Hajjo shi. Kowa sai ambaton masha ALLAHU yakeyi a baki da zuciya. Yayinda Hajjo ta saka Ahmad ya kira mata Yoohan wai itace zatai masa albishir. Aiko ita dince tai masa dan ya dai gane hausar tata saboda Alhmdllh zuwa yanzun harshensa na ƙara faɗawa. Rikicewa yay gaba ɗaya, dan yasan dai hajjo bazata faɗa masa Nu’aymah ta haihu ba danta zolayesa. Sai kawai ya durƙusa yay sujidar godiya ga ALLAH. Duk da a ransa yaji babu daɗi da sai da ya taho ta haihu. Sauƙinsa ma zai tafi hutun ƙarshen shekarane daman dan al’umar Christians nata shirin bikin Christmas.

         Zuwa dare aka sallami su Nu’aymah da ɗan jinjirinta bayan an tabbatar da ingancin lafiyarsu, kai tsaye sashen hajjo aka nufa da Nu’aymah, duk da ita dai a ranta taso zama ne wajen Umm ɗinta. Kafin su kwanta Yoohan ya kirata a waya a karo na kusan huɗu kenan. Dama tuni hotunan ɗansa sun gama cika masa wayarsa. Ganin jaririn nan Abdallah har hawaye sai da yayi, dan da yanzu ɗansane fa Nu’aymahrsa ta haifa masa. Sai dai ƙaddara ta riga fata labarin ya canja daga yanda ya fara. 
         Video call sukayi mai tsaho ita da Yoohan, tana rungume da ɗansu da sai a yanzune ta samu damar zaman masa kallon sosai. Yayinda ran Yoohan ke cike taf da tarin farin cikin ganinta da yaron a jiki, tayi ƙyau sosai ta kuma dace da uwa. Musamman da ƙibar ciki ta sata komawa wata babbat mace. Bai barta ba har sai da ya ga tana hamma. Yasan babu abinda tafi buƙata a yanzu kamar barcin, dan lokacin da cikin ya shiga watan haihuwa bata iya barci sosai. Wani lokacinma kwana take a zaune, sai da rana takan ɗanyi ta rage nauyin ido.
       Washe gari ƴan uwa da abokan arziƙi suka fara isowa gidan ganin ɗan jinjiri. Yayinda tun a farar safiya ta amsa kiran ƴan Abuja su Mama debora, dan har yanzu suna nan a gidan su Yoohan ɗin tare da jami’an tsaro. Tun jiya kuma Yoohan ya sanar musu da haihuwar Nu’aymah harma ya tura musu hoton jariri. Sunso kira tun da daren yace suyi haƙuri sai da safe. Aiko gari na wayewa saiga shigowar kiransu ta hanyar video call.
    Nu’aymah tasha mamaki matuƙa ganin wai harda Joy da Gebrail cikin ƴan murnan haihuwarta. Sun mafi kowa zaƙewar cewar zasuzo kano. Taji daɗin hakan har cikin ranta, dan koba komai dai ba’a canjama tuwo suna. Dole su wannan ɗan nata zai kalla matsayin dangin mahaifinsa. Sune kuma adonsa a cikin al’umma.
       Baba malam shine ya tauna dabino ya bama jin jiri bayan yayi kiran Yoohan ya tambayesa akan yayi masa huɗuba kokuwa zaizo da wuri yayma yaronsa da kansa. Maganar ta bashi kunya sosai sosai. shi ko bama ɗansaba koshi kansa ai Baba malan ya isa da shi. Cikin jin nauyi yace, “Uncle dan ALLAH ka daina neman izinina aka. dukkan abinda ya dace da shi. Kai masa dan kaima ubane a garesa ai. Suna kuma asa masa sunanka, dan ina fatan ya zama mai gadon ɗabi’u da ƙyawawan halayenka da tarin ilimi”.
      Baba malam yaji daɗi sosai da wannan girmamawa. dan haka yayma yaro huɗuba da suna Muhammad Soorajidden. Sai dai ya bar hakan a ransa sai ranar suna idan ALLAH ya kaimu. Ya dai sanarma Umm da hajjo kawai.
         A washe garin data haihu da kwana biyu aka maido su Abban Abdallah gida daga asibiti. Dan baba malam dai da kansa ya roƙa Jay akan a bar maganar zuwa kotun ɗin nan a barsu suji da ciwukan dake tare da su. Badan Jay yaso ba ya yarda da buƙatar ta baba malam aka rufe case ɗin ma gaba ɗaya daga can ofishinsu.  jikin Abban Abdallah yayi sauƙi, sai dai kuma fa akwai matsaloli sosai, dan sakamakon karayar da yayi a kafaɗu wuyansa baya iya zama sam, gashi kansa ya bugu ƙwaƙwalwar sa ta samu matsala daga ciki, matsala irin waddama tafi ta Nu’aymah muni. Baya gane wasu abubuwan yanzu tamkar ƙaramin yaro, ko dubashi kaje yi sai dai ya dinga kallonka kamar wani soko.
      Addah ma dai al’amari ya tsananta a gareta, duk ta rame ta lalace tayi baƙi. Har yanzu da tayi tari kuma sai kaga jini duk da dai ya ragu ba kamar da canba.
     Alƙawarin ALLAH ya cika ta ɗauki gudan jinin Yoohan da Nu’aymah a hannunta. Tai dariya tai kuka abin tausayi. Abban Abdallah kuwa koda aka kai masa jaririn kallonsa kawai ya dingayi amma babu bakin magana, hasalima ba wani fahinta yayi da ƙyau ba sai da Monyn Abdallah tai masa bayani, dan suna nan kano sunma dawo gaba ɗaya. Cikin karkacewar baki ya nuna Nu’aymah ya nuna jaririn yana magana yawu na dilalowa. Yace, “Mamana. Ɗanta?”.
    Kai Momy ta jinjina masa. Hakan ya sakashi yin murmushi mai ciwo sai ga hawaye na zirara masa da gudu. Sosai hakanma da yayi ya bama kowa mamaki, dan baya magana balle nuna fahimtar mutane.
      Ranar dai ansha sabon kuka a gidan, dan komai sabo ya dawo a zukatansu. Sai da baba malam ya sake musu nasiha sannan suka samu nutsuwar zukata.

Previous page 1 2 3 4Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button