SARAN BOYE 75

       Ƴan Abuja basu sami isowa kano ba sai kwana huɗu da haihuwar Nu’aymah. Ba ƙaramin shan mamakin ganin da gidan da Aymah ta fito sukayi ba, sun sake tabbatar da lallai itaɗin jinin babban gidace. Dan duk da kasancewarsu ba ƙabila ɗayaba, ga abinda mahaifinsu ya aikata daya jawo musu baƙin jini a waje. mutanensu acan anan sai ake nuna musu mutuntawa da girmamawa. Hakan ba ƙaramin sakasu jin kunyar Nu’aymah yayi ba. Mama debora harda kukanta kuwa. Dan batai zaton dangin Aymah zasu amsheau da hannu biyu kamar haka ba kodan cin kashin da taima ƴarsu..
         Washe gari ana gobe suna shima Yoohan ya iso tare da Juliet ɗin Umar da baby Ayisha. Kai tsaye nan kano suka nufo dama. Inda Yoohan yay masauki a hotel da Omar ke jiransu. Juliet dai zuwa dare aka kaita gidansu Nu’aymah. Sunyi farin cikin ganin juna sosai, Juliet nata mamakin Nu’aymah da ɗa. itako dariya ta dingayi tana rungume da Ayisha ɗinta.
     Su kansu Omar da Yoohan kallonta kawai suke. Daga baya Umar da Juliet suka basu guri. Tasowa Yoohan yayi yazo ya rungumeta yana sake godema ALLAH ɗan jaririnsa na jikinsa.
      Tai dariya da faɗin, “Silly boy duk ka wani rikice kai ka zama Baba ko?”.
     Dariya sukayi a tare cike da jin daɗi da farin ciki. Yoohan ya sumbaci goshin yaron da faɗin. “ALLAH ya raya Sheikh to be insha ALLAH”.
     Murmushi kawai Aymah tayi da faɗin amin.

RANAR SUNA

         Washe gari aka raɗama yaro sunansa Muhammad Soorajidden a masalaci. Tare da doguwar addu’a a garesa. Kowa yaji daɗin wannan suna musamman Nu’aymah da taji kamar ta haɗiye Yoohan dan farin ciki. Dan babu yanda batai da shi ya faɗa mata sunan jiya ba yaƙi. Kusan ƙarfe goma na safe kuma sai ga tarin alkairi daga Yoohan. Duk wani al’ada na hausawa a bikin suna sai da yayisa bisa shawarar Ahmad da Hamza manager.
      Kowa kam ya yaba ƙoƙarin sa, baba malam ma ya dinga faɗa hidimar tayi yawa.
       Amaryar jego tasha ƙyau harta gaji. hakama ɗan jinjiri Deen. Da yamma akasha walima a ƙofar gidan. wadda tai sanadin karyar da zukatan su Gebrail da su mama debora da suka fahimci Yoohan ɗinsu ya zama musulmi, basu nuna ƙyamar hakanba ko a ransu, saima yanda tsarin yake gudana da ɗabi’un musulman yasa Momy Destiny kasa yin shiru har sai da ta yaba. Dan har ranta abubuwan sun birgeta gaskiya.
     Bayan tashi da ga walima ƙarfe takwas na dare kuma wani tashin hankali ya biyo baya. Dan sama da ƙasa an nema ɗan jariri Deen an rasa. Kafin kace mi gidan ya hargitse. A take Nu’aymah ta sume musu sai da aka zuba mata ruwa. Yoohan na cikin ɗimuwa shima aka ƙwamushesa. Faruwar hakan a gaban mutane ya sa Omar da Ahmad da Omar ɗin su Nu’aymah, da Abdallah da Naseer binsu a mota. Yayinda Nu’aymah ta faɗa miotar batare da kowa ya fargaba sai da sukai nisa.
    A yau tai niyyar nunama Yoohan hoton papa da wadda suke zargin itace mahaifiyarsa. Sai gashi kuma abinda basuyi zatoba ya auku……

Previous page 1 2 3 4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button