Hausa Novels

Lu’u Lu’u 30

*30*

 

A nutse ya k’urawa fuskarshi ido yana kallo yace “Ita d’in ‘yar wasu ce, kuma addininta bai lamunce mata aikata abinda ka so aikatawa da ita yanzu ba, dan ba siyota kayi a kasuwar bayi ba, amma zaka iya neman aurenta hannun iyayenta, dan a gaskiya bana buk’atar wani k’anin wanda aka samu ba ta hanyar aure ba.”

Waro ido yayi yana kallon Umad d’in dake sake k’are masa kallo, a ladabce ya sanyaye yace” Ni zan tafi, lokacin tashin jirginmu ya kusa, sai na dawo.”

Juyawa yayi zai tafi sai kuma ya dakata, ganin kallon da yake masa ne yasa shi fad’in” Mahaifina ka kwantar da hankalinka, babu wanda zai ji maganar nan daga bakina, na san me yake faruwa tsawon lokaci, hakan yasa ban cika son zaman gidan nan, kuma ban ga laifinka duba da halin da mahaifiyata take ciki, takaici d’aya ne kawai yanda ka kasa samun halak d’inka kake bibiyar haram, haram d’in ma wacce ta k’azanta.”

A ladabce ya girgiza masa kai yana sadda kanshi yace” Dan Allah Babana kar ka tilasta mata ta zubar da cikin nan, dan kuskure ne akan kuskure.”

Juyawa yayi a ladabce ya fice a d’akin ba tare da Wudar ya ce komai ba, dan sosai maganganun suka dakeshi, saboda bai tab’a tsammani ba kuma abun ya zo masa a bazata, hakan ya hanashi tambayar ina Umad d’in ma zai je? Dan kunya ta gama lullub’eshi baya jin zai sake d’aga ido ya kalleshi.

 

*Khazira*

 

Ka rantse da Allah mahaifinta kuma sarki Musail bai gargad’eta kan sallah nan ba, domin kuwa la’asar ma a farfajiyar suka yi ta kamar yanda suka yi sallah zuhur.

Suna cikin sallahr nan motar su Umad ta shigo gidan, saidai madadin k’ayatuwar gidan ta d’auki hankalinsu, sai ya zamana sallah ce ta d’auki hankalinsu duba da abu ne da ake yi a b’oye.

Saida suka fito daga motar wani bafade ya d’auko jakarsu k’waya d’aya tak ya nufi ciki da ita, girgiza kai Umad yayi dan yasan wannan kam na daga cikin aikin Ayam.

Bin bayan bafaden sukayi kamar yanda sarki Musail d’in ya umarta a saukesu a babban falo na babban b’angare dan su fara cin abinci, sannan a nan ne zai had’u da Ayam d’in.

Suna kammalawa suka nufi shig ciki sai Juman ta kalleta tace “Ke je ina zuwa.”

Da alamar tambaya tace “Ina zuwa Mah?”

A sanyaye tace “Zan ga mahaifinki ne.”

Jinjina kai tayi ta shige ciki, tana shiga falon suka had’a ido da wata jakadiya, sam bata kula da tsiyarta ba ta taka matakalar ta shiga hayewa sama da sauri.

Sam bata gansu a zaunen nan ba, amma shi tun shigowarta yake kallonta, saidai yanzu kuma da take hawa matakalar sai ya ji gabanshi ya tsiri fad’uwa haka kawai, yanda take hawa da gudu gudu haka zuciyarshi ke harbawa tana dokawa, jikinshi ke bashi kamar da wani abu, hankalinshi ya kasa kwanciya duk da bai ga wani abun zargi ba.

Yanda jinin jikinshi ke tsinkewa yana wani d’add’aurewa yasa shi d’an mik’ewa tsaye, kalonshi Haman yayi yace “Ya dai? Ina zaka je kuma?”

Girgiza kai kawai yayi tare da d’an takawa yana ci gaba da kallonta har ta haye na d’aya ta shiga taka na biyun wanda daga shi zai sadata da d’akin Juman, bata ankara ba, kamar a mafarki, ba zato ba tammani kawai ta ji k’afarta tayi wani k’iiiiiiii, takalminta da a plate ne masu d’amara, tiles d’in kuma irin mai shegen walk’iyar nan ne da sulb’i, hakan yasa duk isa da izzar Zafreen kan ga bata cika anfani da takalmi masu tsini ba, idan ka ga ta sakasu sai ta sauko k’asa.

Abun ne ya had’u yayi yawa, hakan yasa ta kasa rik’e kanta yanda bata da wata dabara daya wuce ta rintse idonta ta anbaci “Ahhhhhhh.”

A k’asan zuciyarta kuma Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un take furtawa, saidai firgicin ya hanata fito da shi, dan ba kad’an ba silb’in nan ya ja ta.

Bata yi k’asa a gwiwa ba wajen fara mirginowa daga kan matakalar, da wani irin sauri ya ma matakalar hawa biyu a na uku ya had’e da ita tana neman k’arasa durkowo, cak yasa hannayenshi da wata irin zummar cimmawa ya d’auketa cak a jikinshi.

Tabbatarwa da tayi ba’a k’asa take ba, sannan ta ji a jikin mutum take bayan wuntsilawar data fara yi, ga kuma k’amshin daya daki hancinta wanda a jikin mutum d’aya ta san shi, da kuma yanda shi ma ya wani k’amk’ameta sai kawai ita ma tayi luf a jikinshi ta sake rik’eshi sosai, idonta kuma har yanzu suna rintse, inda ta shiga sauke numfashi tana fad’in “Oh Allah, Oh Allah na, Alhamdulillah.”

K’am k’am ya ci gaba da mak’ale mata kamar wata wacce za’a k’wace masa, shi ma idonshi a lik’e suke inda gabb’an jikinshi ke karb’an sak’onnin da zuciyarshi ke wadatuwa da su, sai ya ke jin kamar wata masoyiyar daya jima bai had’u da ita ba ne, sai ya ji kamar namijin da aka tura yak’i ne ya dawo da ranshi ya kuma samu iyalinshi lafiya, wata irin kewar wacce yake rumgume da ita ya ji tana lullub’eshi, bugu da k’ari ga wani yanayi da wani shauk’i da ya d’ebeshi kamar ya daure ya sumbaceta.

Yanda siririyar muryarta ta karad’e gidan sanda tayi wannan ihun yasa duk wanda ke b’angaren saida ya ji kuma ya fito har da Zafreen dake kwance a d’akinta tana danna waya.

Haka ma duk da ihun a kad’an ya shiga dodon kunnenta, amma abunka ga mahaifiya sai Juman ta juya tare da furta “Ayam.”

Da gudu ta fice a fadar ba tare data fad’i me take son fad’a ba, sarki Musail daya shiga kid’imar abinda ta fad’a masa na batun gubar da aka zuba musu shi ma da wani irin sauri ya sauko daga kujerarshi ya bi bayanta kamar zai ruga shi ma, hakan uasa fadawan duk suka rufa masa baya Khatar da Dhurani suna mai fatan a ce ta mutu daga ihun nan da suka ji.

Shigowarsu a hargitse yasa su saurin dawowa hayyacinsu, raba jikinsu sukayi da sauri suka kalli juna kamar an firgitasu, Ayam ce hakan ya firgita ta har tace “Kai ne? Yallab’ai?”

Da sauri Juman ta matso kusanta tana duba jikinta tace “Me ya sameki Ayam? Ihunki na ji?”

Da sauri sarki Musail yayi kanta yana d’aga hannunshi alamar zai dafa kanta yace “Me ya sameki? Kina lafiya ko?”

D’aga kai tayi alamar e sannan tace “Lafiya ta lau Pah.”

Juman ce ta sake fad’in “Me ya faru to? Wani ne ya miki wani abu?”

Girgiza kai tayi alamar a’a tana satar kallon Umad, hakan ne ya b’ata ran sarki Musail yace “Ana magana kuna ji kunyi shiru, a cikinku babu wanda zai fad’a mana me ya faru ne?”

D’aya daga cikin hadiman dake kawo abinci ne tace “Ranka sho dad’e muna kawowa bak’i abinci, shi ne muka ji ijunta daga sama, kafin mu farga silb’i ya jata ta fad’o daga…”

Hankalinshi a matuk’ar tashe yace “Daga saman nan?” Ya fad’a yana nuna saman, a sanyaye hadimar ta jinjina kai, sake kallon Ayam yayi ya fara takawa zai tunkareta, kamar kuma an tsikareshi saiya dakata tare da basarwa, a wani gadarance ya kalli Umad dake kallonshi yana son tabbatar da abinda idonshi ke hango masa a game da sarki Musail d’in.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button