Labarai

Najeriya Ta Bukaci Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Gwamnatin Tarayya ta bukaci Rasha ta da gaggauta janye sojojinta da suka shiga kasar Ukraine da yaki.

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, ya bayyana wa taron sirrin da Najeriya ta yi da jakadun kasashen G7 cewa Najeriya ta yi Allah-wadai da abin da Rahsa ta yi wa Ukraine, yana mai jaddada kira ga Rasha da ta janye dakarunta.

“Zaman lafiya da hanyar diflomasiyya su ne abin da ya kamata bangarorin biyu dauka; Muna goyon bayan duk matakan da aka dauka na taka wa Rasha burki da kuma ganin sojojinta sun koma kasarsu,” inji Onyeama.

Aminiya ta rawaito cewa a lokacin taron da ya gudana a Abuja ranar Juma’a, Ministan ya bayyana damuwar Najeriya kan sabon rikicin na Rasha da Ukraine, sannan ya jaddada kiran Najeriya na  a sasanta rikcin ta hanyar diflomasiyya.

Da yake zantawa da ’yan jarida bayan taron, Jakadan Jamus a Najeriya kuma daya daga shugabannin kungiyar G7,Birgitt Ory, ya jinjina wa kungiyar Tarayya Afirka (AU) game da matsayin da ta dauka a kan rikicin na Rasha da Ukraine.

Ory, ya yaba wa matsayin da Najeriya ta dauka a game da rikicin, a matsayinta na mai fa-a-ji a kungiyar AU.

Ya ce a bayyane yake cewa mambobin Majalisar Dinkin Duniya sun yi ittifaki wajen yin tir da matakin sojin da Rasha ta dauka kan Ukraine.

Ory ya kara da cewa Kwamitin Tsaro da kuma Hukumar Kare Hakkin Dan Adam da Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya, wadanda Najeriya ke da kujera a ciki za su cin-ma matsaya kan abin da Rasha ta yi wa Ukraine.

Mahalarta taron sun hada da Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard; takwarata ta Birtaniya, Catriona Laing; Sai kuma Jakadan Tarayyar Turai ga Najeriya da ECOWAS, Samuela Isopi.

Akwai kuma wakilai daga ofisohoin jakadancin kasashen Japan da Kanada a Najeriya.

 

 

 

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *


The reCAPTCHA verification period has expired. Please reload the page.

Back to top button