
???????? SUDESS ????????
*Written story*
*By*
*AUTAR AREWA*
*Godiya ta tabbata ga Allah S W A wanda ya bani ikon rubuta wannan Book,ina rokon Allah ya bani ikon rubuta abinda yake daidai.Allah ya hane ni rubuta abinda zai zama silar wargaza tarbiyyar musulmi,Allah kara daɗin tsira ga fiyayyen halitta cikamakin Annabawa wato Annabi Muhammad S A W* ????
*Gargadi*
Please wannan labarin kirkirarre ne ban yarda a juyamin shi ba,Idan ya yi shige da rayuwar wani to arashi ne,banyi dan cin zarafin kowa ba.
_Ina yima masoya_ _albishir ga duk wanda_ _bai samu krnt Book_ _ɗin_ _DR MUHSEEN ba_ , _to ya garzaya_ _Wattpad_ _domin samun_ _nishaɗi,But_ _wannan Book ɗin da zan_ _fara na siyarwa_ _ne_
Ina mika sakon gdy ta
ga yan'uwana
marubuta
musamman na kungiyar
AREWA
WRITTERS Allah yabar
zumunci
. ????
Paid Book ne masoya akan farashi mai sauki ₦500 kacal ????za ki sha krt cikin kwanciyar hankali,ta wannan Account 3125654602 Rukayya Idris First Bank,ki turo shaidar biyan ta wnn nomber 08162385196,Ko hoton katin MTN pls banda VTU ???????????? Idan kinsan ba siya zaki yi ba kada mu ɓatawa juna time.
Bismallahi Rahamir Rahim
Free page 1️⃣
????……….. KATSINA STATE
ON SONDAY
5:00 PM
Jamvaly Hotel nearest Liyafa Hotel,Da yamma misalin ƙarfe biyar manyan motoci ne birjik a harabar saban Hotel ɗin.Wurin ba hayani sai sassanyar iskan dake kaɗawa,mai cike da ni’ima sakamakon girgijen hadarin da yayima sararin samaniya rumfa.Hakan yasa garin ya yi luf ga dukkan alamu akoda wane lokaci ruwan sama yana iya sauka.Wata ƙatuwar Toyota land cruiser Prado naga ta shigo harabar wurin,fara ce kal sai faman kyalli da ɗaukar ido take yi.Wurin da aka tanada dan adana motoci naga motar ta nufa,cikin slow mamallakin motar ya yi parking.Kasancewar glass ɗin motar tintex ne shiyasa bana iya hangen mai motar har saida ya fito.An ɗauki tsawon 10 minutes kafin naga an buɗe mazaunin driver,wani siririn matashin saurayi naga yayi saurin fitowa cikin azama ya buɗe back sit yana matsawa gefe ɗaya.Kafa ɗaya ta fara zirowa kasa sanye da halp cover white color mai adon Stone a jiki irin na sarakuna.Cikin lokaci ƙalilan ya fito da gangar jikinsa,saurin dubanshi na yi ina furta “Masha Allah”.Dogo ne sosai amma yana da ɗan kauri,jikin shi a murje yake alamu na yana cikin hutu da jin daɗi,yana da hasken fata amma ba sosai ba.Farin yadin boyal ne a jikin shi mai dauke da kananun zane,wanda ya sha ɗinki irin na samarin zamani,sai Black agogo daya ɗaure a tsintsiyar hannun shi na dama,a jikin siraran fararan yatsun shi kuwa ya saka white ring mai kyau a karamar yatsa.kanshi bai saka hula ba sai bakar sumar shi data sha gyara gwanin sha’awa kamar ɗan India.Abinda ya fi ɗaukar hankali a kyakkyawar face na shi manyan dara-daran eyes balls ɗin shi masu kamar madara.
A hankali naga ya rufe manya eyes ɗin shi yana sauke ajiyar zuciya.Tare da furzar da iskar bakin shi.Manyan wayoyin shi dake rike a hannu ya kalla ga dukkan alamu kira ne ya shigo.Ɗan siririn tsaki ya ja,wanda idan ba kana gaf da shi ba,ba lallai ka ji ba.Cike da taku irin na zaratan maza ya fara taku yana nufar cikin hotels ɗin.Da sauri drivern ya ɗauko wats ƴar karamar jaka,ɗauke da system ɗin shi haɗi da takardu.Take mai baya yayi suka kusa cikin saban Hotel ɗin.
A resption suka tsaya inda suka kama room,wani kati naga an mikama drivern kafin suka wuce ciki.Room 140 suka tsaya drivern ya kara katin jikin kofar nan take naga kofar ta buɗe,a tare suka shiga room ɗin mai ɗauke da Italiyan bed sai wasu kananun kujeru guda biyu,haɗi da karamin table.Akwai komai na bukata a ciki kama daga kayan elctrics,grass capet sai cotten masu taushi,komai na ɗakin white color ne.Fita yayi drivern sai ga shi ya dawo ɗauke da yar madaidaiciyar trolly ya aje,harya juya zai fita ya ji Muryar ogan na shi yana yana cewa “Pls salisu ka barmin motorn,anjima zan shiga gari,idan kana bukatar zuwa around 9 ka zo mu je”.
Da “To” wanda aka kira da Salisu ya amsa kafin ya fice daga room ɗin.Direct mai Napep ya tsayar ya shiga yana faɗamai unguwar da zai kai shi.Bayan fitar Salisu driver a hankali SUDESS ya shafi gefen fuskar shi mai ɗauke da ɗan madaidaicin saje irin na cikakkun samari,wanda ƴan’mata suke kira da quater million,yana lumshe dara-daran eyes ɗin shi,a galabaice ya kwantar da bayanshi jikin kujerar yana yana kara shafo lafaffen cikin shi wanda yake kamar takalmi.Can kasan makoshi ya furta “washhh!! Oh my God!!”
Cikin natsuwa ya fara kokarin cire rigarshi,ya rage da shi sai singlet ba takalmi sai santaleliyar farar kafarshi data bayyana ya nufi kofar da zata sada shi da toilet.ABDALLAH MUSA MASANAWA KENAN wanda ake kira da SUDESS.
BABBAN BIRNIN TARAIYYA NA NAJERIA WATO ABUJA
GARKI AREA 11 QAUTERS
Kowa yasan babban birnin Nageria,mai cike da mutane iri daban-daban,Kama daga musulmai,Ibo,Fulani,yaren barebari,da sauran yarika daban-daban.A wani bangaren kuwa ta haɗa manya-manyan yan siya waɗanda suka ci suka tada kai da Naira,da attajiran yan kasuwa,Manyan masu muƙamin gwamnati da masu ɗamara,harma da wasu daga cikin talakawa masu zuwa neman na kansu.A daidai wannan lokacin cikin wannan babbar unguwa da take tsit tamkar babu halittun mutane a ciki,sai manya-manyan gidajen dake shimfiɗe tamkar a kasar Landon,gefen hannun damana na kalla inda yafi ɗaukar hankali na.A yadda na lura duka cikin layin gidan yafi kowanne tsaruwa.Yana ɗauke da gate guda huɗe duka iri ɗaya,tun da ga irin gate ɗin zaka san cewa masu gidan ba kananun mutane ne ba.ga wasu manyan shuke-shuke da aka zuba masu ɗaukar ido.fentin gidan kalar white and ash color ne,gate ɗin glass ne domin kana hangen jikinka,idan ka shiga ciki kuwa kana ganin abinda ke faruwa ta waje.
Cikin harabar gidan kuwa ga wurin swimming pool nan sai kagan lambu daga gefe mai cike da shuke-shuken kayan marmari.Akwai tazara sosai daga bakin gate suwa parts na cikin gidan,bayan ka wuce boss quters.
Cikin part ɗin da ya fi kowanne girma na nufa,Tun a falon gidan nake jiyo karan kiɗa yana tashi tamkar an kunna dije.wata matashiyar yarinya ce take rawa tana kallan wayar data tsayar jikin ring light,haka yasa na gane Tiktok ne take yi.Cikin murmushi ta idar da vedion tana huci tamkar wacce ta yi gudin tsere.Sosai take murmushi tana posting,Cikin harshen turanci ta ce “Uhmm saina tarwatsaku da salona,Nasan yanzu zanga ruwan like da comments”.
Turo kofar da aka yi yasa tayi saurin duban kofar tana sauya fuskarta daga farinciki zuwa bakin ciki.
“Yanzu zaheeda ba Yayanku ya hanaku wannan shirmen raye-rayen ba,amma ke baki jin magana ko?,to ki ci gaba ai ba daɗewa zai yi ba,kuma kinsan halinsa”. Dattijuwar matar ta idar da maganar cikin bacin rai.
Yarinyar da aka kira da zaheeda cinno ɗan karamin bakinta ta yi tana ɓoye wayar a bayanta.
“Ina AUTAH”?.
Dattijuwar matar ta sake jefomata tambayar.
Kame-kame ta fara yi irin na marassa gaskiya kafin ta ce “uhm ta je part ɗin Ya Jabbar”.
Jin haka yasa dattijuwar matar fita daga ɗakin tana jinjina kanta.
“Uhmmmm” Zaheeda ta sauke ajiyar zuciya tana cigaba da karanta Comments ɗin da follwers ɗinta suke ta faman yi.hakan yasa ta ji wani farinci ya rufe ta.
Night around 9:00 pm cikin Katsina hanyar studiom,a hankali motar SUDESS take tafiya kasancewar titin ba yawaitar motoci.Sosai SUDESS yake kallan garin abubuwa da yawa suna dawowa kanshi wanda suke kara tunamai rayuwashi ta baya lokacin suna zaman Katsina.Harsun gota wani karamin titi SUDESS yasa salisu ya juya kan motar suka shiga ta cikin unguwar.Farkon layin ba gidaje sosai yasa ya ji tsarin unguwar ta yi mai.Garammmmmmmmmmmm ya ji motar su ta yi karo,cikin tarin tsoron abinda zai faru ya ɗago manyan eyes ɗin shi yana duban gabansu.
“Innalillahi wa’innailaihirraju’un,sorry sir” Ya ji Muryar salisu.
“Subahallah”ya furta a hankali yana tasbihi ga Allah da yasa lamarin ya tsaya iya haka.
Cikin sauri Salisu ya fita,ganin yarinyar yashe cikin jini yasa yayi saurin lekawa mazaunin ogan nasa yana cewa “Sir yarinyar kamar ta suma fa”
Jin haka yasa SUDESS fitowa yana nufar gaban motar inda yarinyar take.
Cikin tsoro ya ce “Innalillahi that girl……….”
*By*
*AUTAR AREWA*.
✍️✍️✍️✍️✍️✍️
AREWA WRITER’S ASSOCIATION
????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????
???????? SUDESS????????
*Written story*
*By*
*AUTAR AREWA*
Ina yima masoyana albishir ga duk wanda bai samu krnt Book ɗin DR MUHSEEN ba, to ya garzaya Wattpad domin samun nishaɗi,But wannan Book ɗin da nake yi mai suna SUDESS na kuɗi ne .