SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

           *SULTHANA*
        ????????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

          *Page 1 to 5*

Yarinya ce da bazata wuce shekara sha uku bah rak’ube jikin katanga cikin duhun dare sai rawar sanyi take, bata ankara bah ruwa ya tsuge kamar da bak’in kwarya. Dasauri ta koma zauren gidan ta samu guri ta k’ara rakubewa dukda zauren yana zuban ruwa hakanan ta zauna tana matsar kwalla a hankali..

Ruwan sama ake tsugawa a garin kamar da bak’in kwarya, dakyar ta sulale k’asa ta kwanta tana Cigaba da rawar d’ari, Haka barci ya dauketa.
Kiraye Kirayen Sallan Asuba taji, a hankali ta gyara kwanciya saboda sai lokacin ta samu barci sosai, bata gama gyara kwanciyar bah taji tokari. Koba’a fada mata bah tasan Baffa neh, dasauri ta Mik’e zaune tana soshe soshe tana k’ara kallan Baffa dak’e tsaye ya hasketa da tochila.
“Dan Uwarki kinaji ana kiran Sallah bazaki tashi bah, waike Wacce irrin dabba ce zaki tashi koh saina mangareki”
Dasauri ta mik’e ta shige cikin gida tana cigaba da soshe soshenta.

Mama ta hango bak’in rijiya tana jan ruwa, ta k’arasa dasauri ta rik’e gugan
“Mama kawo naja mik’i”
D’an murmushi mama tai
“Aa Sulthana barshi, dauko butta na zuba mik’i kiyi Alwala”
Bah musu ta dauko buta ta k’araso bakin rijiyan, dai dai nan hafsatu ta fito daga dak’in barcinsu tana sosa kai dagowan dazatai taga hango mama na zubama Sulthana ruwa a buta
“Lallia ma Sulthana, dan tsabar iskanci mama ce baiwar ki?? Har tana jawo ruwa tana zuba mik’i a buta”

Nan da nan jikinta ya soma rawa dan tasan halin hafsatu sarai, yanzu ta kamata taimata dukan tsiya
“Haba Hafsatu, menene dan nazuba mata ruwa, yanzu tazo zata amsa na hanata”
Saurin K’arasowa wajan Hafsatu tai
“Haba mama ya k’ike irin wannan maganan, Baffa ya gaya mata duk aikin da zata rink’a yi a gidan nan ciki kuwa harda jan ruwan nan, Anma saboda iskanci tak’iyi saike zaki ja.”
Hade rai mama tai tana cigaba da kallan hafsatu
“Banasan iskanci, ki wuce kije kiyi Alwala”
Zumburo bak’i tai ta juya ta kalli Sulthana dak’e tsaye kanta a kasa tayi kwaffa tabar wajan..

Mama ta maida dubanta ga Sulthana
“Ga ruwan maza jekiyi Alwala kamin Baffanku ya dawo”
Amsa tayi ta shiga bayi ta kama ruwa ta fito tai Alwalan, dai dai itama mama ta gama nata Alwalan
“Sulthana shigo dak’ina kiyi Sallan kafin Baffanku ya dawo maza ki hanzarta”

dasauri sauri ta sauya kayan jikinta zuwa wata kod’adiyar Atampha dogon riga, Hijabin mama ta sanya ta tada Sallah. Tana Cikin sallan taji sallaman Baffa, Hanjin Cikinta neh ya k’ada dakyar ta k’arasa idar da Sallan ko Addua bata tsaya yi bah ta fito daga dak’in. Hangoshi tai a Bukkan tumakin shi yana zuba musu Abinci, dagowan da zaiyi yaga ta fito daga dakinshi tana yan Rabe Rab’e kanta a k’asa..

“Sulthana! Daga wani dak’i naga kin fito yanzu”
Inda Inda ta soma yi chan sai mama ta fito sanye da hijabi da Alama Sallah ta idar
“Sallah nace tazo tayi”
Mugun kallo Baffa yabi mama dashi
“Sau nawa Saratu zan fada miki ki fita harkar Yarinyan nan anma Kink’i”
Sakin Bak’i mama tai da mamaki tana cigaba da k’allan Baffa
“Haba Mallan sai kace bakai ka haifeta bah, baka tsoron hakki. Yarinyan nan Amanace fah a Wurinka mai yasa Kake ha..”

“Dallah rufemin baki”
Maida Dubanshi yayi ga Sulthana dake tsaye har lokacin kanta a Kasa da Alama kuka take
“Keh kuma tsayuwa kikai kina Karemin Kallo bazakije kiyi aikinda Yakamata bah”
Dasauri tabar wajan ta Nufi kicin dinsu, kwanonin datti ta soma fitowa dasu tana kaiwa bak’in Rijiya tana Ajewa, lokaci lokacin takan share hawayen dak’e gangaro mata a fuska…

Shin anya kuwa Baffa mahaifin Sulthana neh?”
Ku biyoni dan jin Cigaban Labarin

*Ummy AbduAbduol✍????

????????????????????????????????
????????????????????
SULTHANA
????????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

          *Page 6 to 10*

Lokaci lokaci takan share hawayen dake gangaro mata a fuska. Saida ta wanke kwanukan tas sannan ta share tsakar gidan tareda daura abin kari. Bayin gidan ta wanke ta Fito tadau Tsintsiya ta nufi dak’insu Hafsatu. A Kwance ta sameta tana barci gefenta kuma ameena ce zaune kan sallaya tana karatun alkur’ani, dan Rusunawa tai
“Ina kwana yaya Ameena”
Saida ta kamalla sannan ta juyo ta k’alleta da murmushi akan fuskanta
“Lapia lau Amal, kin Tashi Lapia”
Kanta na K’asa ta amsa da Lapia Lau.

Shiru ne ya biyo baya na wasu mintina, dakyar amal ta bude baki tace
“Dan Allah Yaya Amina ki tayani tashin yaya hafsatu inaso nai shara”
Batare da tace komai bah ta shiga tashin hafsatu, dakyar ta tashi suka bata waje ta gyara musu dak’in tsaf. Bata gama ayukanta bah sai wuraren karfe bakwai da rabi na safe, baffa ko sai masifa yak’e tak’i ta gama abin karyawa ga yara naso suje makaranta. Koko ta dama ta dafa musu dankalin Hausa, saida ta zubama kowa ta kaimai Sannan ta dau nata ta nufi zaure dashi.

Hafsatu da Amina suk’a leko dak’insu baffa bayan sun gama karyawa
“Mama, Baffa mun tafi”
Da Fara’a yak’e kallansu Tareda sa hannu cikin Aljihunshi, kudi ya Ciro naira Dari biyu
“Gashi ku raba”
Amsa sukai tareda mai godiya Suka wuce. Mama ta Kalleshi Fuskanta bah Walwala
“Mallan Idan nace inajin Dadin Abinda Kakeyi nayi K’arya”
Kallanta yayi da Mamaki
“Meh kuma nayi?”

Shiru tai dan Tasan Halin baffa Yanzu ya zazzage ta dah Masifa
“Keh nake sauraro”
Ta maza tai ta Kalleshi
“Haba Mallan, Baka gudun surutun mutane?? Koda yake surutu ni nake shanta bah Kai bah”
Kallanta yayi da Alamar mamaki
“Ki fito fili kiyi magana bah kwana kwana bah”
Akan Maganan Sulthana mana Mallan, Yarinyan nan batakai shekarunda zata Rink’a wadan nan Aikin bah, Sannan kuma ka hanata zuwa makaranta. Haba Mallan sai kace bakai ka haifeta bah”

Dogon tsaki yaja tareda mik’ewa
“Ina K’ara gaya miki ki fita Akan harkan Yarinyan nan Bah ruwanki”
Itama Mik’ewan tai tana kallanshi da damuwa
“Haba mallan wanne irin bah ruwana, yarinyan nan fah y’arka ce, jininka ce duk inda na zaga kallona ake ana nunani ana zagina akan ina cizgunama yarinyan nan, kowa laifina yake gani”

Gidon tsaki yaja yabar dakin a fusace, a tsakar gida yayi kicibus da Sulthana shigowanta kenan cikin gidan tana tattara kwanukan da aka ci abinci. Dasauri tabar wajan dan k’aramin aikinshi ne ya duketa batamai komai bah. Kwafa yayi ya fita daga cikin gidan a fusace..

     Wanene Baffa?

Dan Asalin jahar kano ne a kauyen karaye. Cikakken Sunanshi Mallan Jamilu dan Mallan, mahaifinshi Mallami neh mai tara Almajirai. Shi kadai mahaifinshi ya haifa, bayan rasuwan mahaifinshi ya cigaba da kula da Almajiran mahaifinshi kasancewar shima yanada Ilimi sosai. Ya gaji gado mai tarin yawa wanda idan ana lissafin masu kudin kauyen zai zo saahu na biyu ko na uku.
A Haka Allah ya hadashi da Rabiatu yarinyar wani buzu da sukazo Cirani nigeria, Shida Rabi sunyi auren soyaiya da Kaunar juna. Sun shafe shekaru masu tarin Yawa har Mallan Jamilu ya sak’e Aure inda ya auri saratu, aurenta da shekara daya ta haifo Amina, bayan Shekara biyu ta K’ara Haifo Hafsatu. Rabiatu da Saratu sunyi zaman lapia sosai wanda ba wanda kejin Kansu duk da kuwa bah Gida daya suke zaune bah. Hafsatu nada Shekara biyar Rabiatu ta Samu Ciki, Cikin Ikon Allah ta Haifi Yarta Ranar Suna Ita da Kanta tasa mata suna Sulthana wato (Sarauniya)

Sam Mallan baiyi Farinciki da Haihuwan nan bah, Tun a Sannan Rabiatu ta fara Fuskantan Wulakanci da Cin Mutumci gurin Mallan, Sulthana nada shekara Sha Biyu mahaifiyarta Allah ya mata Rasuwa ta sanadin Ciwon zuciya wanda Mallan Yak’i kula da ita har Allah ya dauki rayuwarta. Bayan Rasuwan mahaifiyarta Mallan ya dawo da ita gidan d’ayar matarshi Saratu, inda Ya hana sauran yayanshi kowane aiki sai Sulthana, mama wato Saratu na matukar tausayama halinda take ciki itada Aminatu. Mallan Ya cireta a makaranta wanda dama ummanta ce ta sata, ya hanata Hulda da kawayenta, Gashi yan uwan mahaifiyarta bah a kasan suk’e bah..
Wannan knan…..

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button