SUDESS COMPLETE HAUSA NOVEL

SUDESS COMPLETE HAUSA NOVEL

SUDESS COMPLETE HAUSA NOVEL

kada ku manta wnn Book na kuɗi ne ????

         *By*

*AUTAR AREWA*


  ✍️✍️✍️✍️✍️

???????? SUDESS????????

    *Written story*


               *By*

  *AUTAR AREWA*

Paid Book ne akan farashi mai sauki ₦ 500 kacal za ki sha krt cikin kwanciyar hankali. Ta wnn Account Nomber 31256540602 Rukayya Idris first Bank,ki turo shaidar biyan ki ta wnn Nomber 08162385196,ko hoton katin MTN pls banda VTU ???? idan kinsan ba ki shirya ba kada mu ɓata time.

Bismallahi Rahamir Rahim

Free page 4️⃣

   ????.................Tana sakin murmushi mai cike da jin daɗin abinda yake yimata,a hankali ya ke tafiyar da ita na irin gogagun mazan nan da suka san takan mace,itako meema sosai ta ji daɗin wannan kasancewar ta su,dan ji take yi tamkar bata taɓa sanin wani ɗa namiji ba,sun shafe sama da awa biyu suna sha'aninsu kafin suka tsagaita badan sun gaji  ba,sai domin nemawa jiki hutu.Wanka suka yi kafin suka kimtsa zuwa lokacin ƙarfe ɗaya saura.Mus'ab janyo wayar shi yayi yana duba irin kiran da aka yi ta jeramai lokacin ya lula duniyar daɗi,kiran Ya SUDESS ya gani tuni ya ji gaban shi ya faɗi,yana so ya bi kiran amma ya kasa saboda ganin dare ya yi,daga haka suka sakama cikin su abu marar nauyi kafin suka kwanta rungume da juna tamkar zai mayar da meema cikin shi.

A bangaren SUDESS kuwa koda ya kira wayar kanin na shi ya ji bai ɗaga ba ya kyale shi,amma yana tunanin hali irin na kanin na shi,ya rasa ya zai yi da shi,amma kullin yana yimai addu’ar Allah ya shirya shi,daga haka ya kwanta bayan ya yi addu’o’in neman tsari.
Saida SUDESS ya shafe tsawon kwana biyar kullun suna zarya Campany idan suka fita tun 10 sai dare suke dawowa,lokutta da yawa mantawa yake da yarinyar nan sai idan Salisu ya tunamai,abincima sai Salisu ne yake kaimata,gaba ɗaya kan SUDESS ya ɗau zafi sai fama yake yi,waya ma da yan gidan su sai jefi-jefi yake samun time su gaisa. A cikin rana ta shida ne da dare bayan ya kimtsa ya nufi ɗakin da Jemima take yana addu’ar Allah yasa ta faɗamai unguwar su ya mayar da ita. Yana tura kofar ya jita a rufe knowking ya fara yi yana jin haushin kanshi.cikin magagin bacci ta ji kamar ana buga kofa ta buɗe idonta,kofar ta tsirawa ido tana nazarin ko wanda yake kawomata abinci ne,to amma idan shi ne ai ya kawomata tun ɗazu,agogo ta kalla ganin karfe goma saura yasa ta yi saurin ziro siraran kafafunta tana jin wani jiri,bakin kofar ta tsaya ba tare data buɗe ba.Ji ta yi an kara bugawa,kafin ta saka fararen yatsunta ta murɗa kofar bayan ta cire key ɗin.Ganin shi ta yi a tsaye sanye da brown jallabiya ya zuba hannuwan shi cikin aljihu ,sosai ta kuramai ido ganin ya ɗan rame idon shi ya kara fitowa. Cikin yaren turanci ta ce “Good evening”tana ja da baya ganin zai shigo cikin room ɗin.
A hankali ya zauna saman karamar kujerar dake passing bed ba tare daya amsa ba. Jemima ta yi tunanin bai ji ba ta kara maimaitawa kafin ta tsugunna gefen kafafun shi tana tsurama yatsun kafar shi ido.
A hankali ya amsa cikin yaren turanci ya ce “Ya jikin na ki” amsawa ta yi “Da sauki”
“Allah ya sauwake” ya ce yana picking call na Doctor Mujaheed “Hello Doctor barka da dare?”.
A ɗayan bangaren Doctor Mujaheed saida ya kalli matar shi yana murmushi kafin ya ce “Lafiya lau gauro,shugaban gaurayen Katsina da Abuja”. Sosai SUDESS ya murmusa har fararen haƙoran shi suka baiyana ,yar yalwatacciyar sumar shi ya shafa yana jin nauyin maganar kafin ya ce “Uhmm tau sarkin surutu ina maman takwarana?”ta can Doctor Mujaheed ya ce “Gata nan kusa da ni,takwaranka kuma ya yi bacci,ya jikin wannan yarinyar ta warke ko?” Ya yi tambayar yana ɗora kanshi bisa kafaɗar Hannatu.
“Ta ji sauki,but ina so gobe na mayar da ita gidan su,kaga bai kamata ta yi ta zama anan ba,Ni kaina bana iya kula da kaina ballanta ita,na ga ji Doctor Mujaheed,jibi zan koma gida insha Allah” Ya kai karshen maganar yana langabar da kanshi gefe ɗaya alamar ya kosa da maganar.
Ita dai Jemima jefi-jefi take ɗagowa ta kalle shi saboda ta kasa fahimtar wane irin yare ne yake yi.
Daga can Doctor Mujaheed ya ce “Ayya sorry tazuru gobe ka kawo ta nan Hindatu zata kula da ita,tun farko na yi tunanin ka mayar da ita shiyasa,kada ka damu gobe Salisu ya kawo ta before ku fita kada hakurin ka ya kare ka kwamishe yar yarinya”Ya ida maganar yana saka dariya dan yasan yanzu zai katse call ɗin.Haka ta kasance kuwa cike da bacin rai SUDESS ya katse kiran yana jan dogon tsaki ya furta “That man is not easy”. Jin ya katse call ɗin Doctor Mujaheed ya kalli Hindatu yana kyalkyala dariya, “Uhm Dear ka kyale SUDESS ya huta,na fahimci ka takuramai shiyasa baya san kiran ka”cewar Hindatu,”Kyale shi ɗan iska ne saiya rika nuna shi bai san wani felling ba danya raina mu,dan dai nasan yana da tarbiya,amma ina jiyemai kada ya fara neman mata, SUDESS fa ya fini a haife amma kinga kusan shekarar mu biyar da yin aure,saika yimai maganar aure ya rinka wani lumshe maka eyes saboda tsabar iya shege,barni da shi dole ya nemi matar aure ko zai kara samun natsuwa” ita dai Hindatu bata kara cewa komai ba ya ci gaba yimata hirar SUDESS. A bangaren SUDESS kuwa
Ta kasan ido ya kalleta kafin
ya mike ya fice daga ɗakin.
Jemima tana ganin ya fita ta mike tana taɓe ɗan madaidaicin bakinta ta haye bed.
Yana komawa ɗakin shi kiran AUTAH yana shigowa wayar shi,katsewa ya yi kafin ya kirata,cikin siririyar muryarta mai daɗin sauraro ta ce “Assalamu Alaikum Ya barka da dare,hope kana lafiya?”.
Murmushi ya saki tamkar yana gabanta kafin ya amsa da “Lafiya lau little,ya rashin jin magana?kin daina ko?”ya tambaye ta cikin hosy voice irin na mai jin kasala.Yar dariya ta yi suka ɗan taɓa hira kafin ya katse call ɗin.
Wani iri yake jin jikinshi tamkar mai zazzaɓi,magani ya sha kafin ya kwanta bayan ya turawa Salisu sako akan da safe ya zo ya kai wannan yarinyar gidan Doctor Mujaheed.

Washe gari da wuri ya shirya ya fito palor yana ɗaura agogo.saman one seter ya zauna saiga Salisu ya shigo ɗauke da kayan break,saida ya aje kafin ya gaishe da ogan na shi,na Jemima ya ɗauka ya nufi bakin kofar ɗakinta,harya kusa kaiwa daidai kofar ya ji Muryar ogan shi ya ce “Kada ka shiga”. Da “To” Salisu ya amsa kafin ya yi knowking.saida ta buɗe ya mika mata kafin ya sanar da ita sakon ogan na cewar ta shirya za su fita. Amsawa ta yi da “Ok” ta koma ciki.
Palorn Salisu ya dawo shima ya yi break kafin ya fita. Ita ko Jemima kaɗan ta ci arish ɗin da wainar kwai ta goge bakinta, rolling mayafinta ta gyara kafin ta saka plant shues ɗinta ta nufo palorn.A hankali ta tsugunna tana gaishe da shi.can kasan makoshi ya amsa kafin ya mike ta biyo shi baya.har bakin motar suka karaso ya Salisu ya buɗe mai front sit ya zauna,kafin ya buɗe ma Jemima ta shiga shima ya zagaya mazaunin driver bayan ya aje kayan ogan na shi ya tayar motar,mai gadi ya buɗe gate suka fice daga gidan.
Wajen government House suka nufa anan gidan Doctor Mujaheed yake,ba tare da ɓaga lokaci ba aka buɗe masu gate suka shiga,a wurin parking suka tsaya,kafin ya kira wayar Doctor Mujaheed time ɗin suna break ya ga kiran abokin na shi kuma ɗan’uwan shi.Ɗagawa ya yi jin sun karaso ya ce “Ku shigo mana” ya aje wayar yana cema Hindatu kinga harsun kara so.
Fitowa SUDESS ya yi yana cema Jemima “Zo mu je”.Sauka ta yi tana bin shi a baya kamar jela, tas ta karem halittar shi kallo ganin yadda yake da murjewar jiki kamar na mazan India.
Suna shigowa palorn Hindatu ta taso da sauri ta rungume Jemima tana shafa kyakykyar fuskarta ta ce “Your welcome Dear”. Ganin haka yasa itama Jemima ta saki murmushi tana gaisheta.Zaunar da ita ta yi kafin shima SUDESS ya zauna,nan take Hindatu ta fara haɗamasu abinci,amma SUDESS kin ci ya yi ya ce ai sun yi break a gida.Bayan sun kara gaisawa ta kalli SUDESS ta ce “Am gsky Yayanmu ina ka samo wanna little ɗin,irin wannan kyau haka kamar ita ta yi kanta”shidai SUDESS murmushi ya yi bai ce komai ba.
Sai Doctor Mujaheed ya ce “Uhm kin gani ba abinda nake faɗa maki,sai anyimai magana ya rinka wani lumshe ido kamar wani jarumi,to wallahi wannan week ɗin zan je Abuja saina Kunno maka wuta wurin Uncle Hasan,kuma kasan halin shi tsaf yake iya yima auren dole,kai baka tausayin kanka,sai faman zafin neman kuɗi amma ka kasa samun abokiyar rayuwa”ya karashe magar with compidens.
Danda nan SUDESS ya ɓata rai ya kankantar da ido ya ce “wallahi Mujaheed ka fita a idona,kasan me kake cewa kuwa,Ni ba yayanka ne ba”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button