SUDESS COMPLETE HAUSA NOVEL

SUDESS COMPLETE HAUSA NOVEL

SUDESS COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sorry tazuru yanzu ni ne babba tunda harna a jiye iyali,sai ka yi hakuri ka ɗauki kankantar,ai na fahimci baka tausayin kanka,amma idan aka yima auren dole to bamu san lokacin da zaka rike matarka ba,muma Momy ta huta da dafa maka abinci” ya ida maganar yana yimai dariya.Ganin haka yasa SUDESS mikewa yana cewa “Maman Boy ni na wuce saina dawo”ya fice ba tare da ya kara kallan inda Mujaheed ya ke ba.Da Allah kiyaye ta bishi tana mayar da kallanta ga Jemima da take ta faman kallansu saboda bata gane Yaren Hausa.
Kama hannunta tayi suka nufi ciki tana cema Mujaheed “Dan Allah Hubbi ka kyale bawan Allah nan,kaga ka ɓata mai rai,kada ya yi fushi”.

 "Kyale shi Hubbi ai na fahimci idan ba haka aka yimai ba,to shi bai ki ya karasa rayuwar sa a haka ba,a ce mutum kusan shekara Arba'in amma yaki yin aure,anjima zan kira Uncle Hasan na haɗa mai bom".

Ita dai Hindatu jan hannun Jemima ta yi suka wuce ciki ta kaita ɗakin da zata zauna,ta nuna mata wasu abubuwan kafin ta koma kitching dan ɗora girkin rana”.
Shima Doctor Mujaheed asibitin shi ya nufa,da zummar da ya dawo zai kira Uncle Hasan su tattauna.
A yinin ranar hakanan SUDESS ya yi shi a Company ba tare da walwala ba tun bayan maganar da Mujaheed ya faɗa mai,yasan halin Uncle Hasan mutum ne mai zafi,ko last year dakyar ya samu suka hakura akan magar auren shi,yanzu kuwa yasan idan tsautsayi yasa aka tado da maganar to yasan ko shawara bazasu yi mai ba,shi kuma tsakanin shi da Allah yanzu idan aka haɗa shi da wata ai an takura mai bazai iya kula da ita ba,tunda shima Momy ce take kula da shi to ina zai iya,da wannan tunanin suka ta shi kafin suka wuce gida.

A bangaren Mus’ab kuwa sosai suke sheke ayar su shida Meema ba tare da tunanin komai ba,ya sakarmata kuɗi kamar ba gobe,tunda ya yi kwana ɗaya a Hotel ɗin Dady ya kira shi akan cewar duk inda ya ke ya zo gida,saboda baya so suna kwana a wani wuri idan har ba aiki ne ya kai su ba,badan ya so ba haka ya hakura ya ke kwana a gida,da rana idan ya ta shi daga aiki saiya wuce wurin Meema.

A ranar dai SUDESS tunda ya dawo daga aiki bai samu damar zuwa gidan Doctor Mujaheed ba,saboda a gajiye yake saida dare Mujaheed ya kira shi akan meyasa bai zo ba,anan ya sanar mai da ya ga ji,to anan ma dai saida suka yi faɗan da suka saba kafin aka rabu.

Yau kwanan Jemima biyu a gidan su Doctor Mujaheed,hankalinta kwance komai na bukata tana samu,sun siyamata sabbin kaya masu kyau da kayan kwalliya.Haka suke zama da Hindatu suyi ta labari idan Mujaheed ya fita wurin aiki.Matsalar guda ɗaya ce idan Hindatu ta tambaye ta ina iyayen ta ba amsa sai dai ta saka kuka,dole tasa ta kyaleta.
Ta faɗama Mujaheed yadda suka yi ya ce ba matsala a bita a hankali zata sanar masu.
A ranar da SUDESS zasu koma Abuja shida Salisu around 8 yana bacci ya ji ringing ɗin wayar shi,cikin magagin bacci ya janyo wayar ko duba mai kiran baiyi ba ya yi picking yana ajeta gefen pilwo.
Muryar Mujaheed ya je ya ce “Gaskiya ne dole kake bacci da nasari,to karka bar garin nan sai ka zo ka ɗauki yarinyar nan,yanzu na kara tabbatar da bazaka iya kula da mace ba,tunda ka ki zuwa”.

Cikin muryar bacci SUDESS ya ce “Pls Doctor wai meya faru,kai dai baka so hankalina ya kwanta,dan Allah ka kyale ni na ji da ayyukan gabana”.ya ida maganar yana juya kanshi gefe ɗaya”.
Daga can Doctor Mujaheed ya ce “wallahi sai ka zo ka tafi da yarinyar nan,ko na kira Uncle Hasan kuma kasan abinda zai biyo baya”.

Cikin jin haushi SUDESS ya ce “Wait malam wai me kake cewa?wata yarinya kake nufi?”.

“Innalillahi wa’innailaihirraju’un” ya ji Mujaheed ya rafka salati.
“Yanzu SUDESS ka kawo yarinya gidana yau kwana huɗu,amma ka ce ka manta,gaskiya ina ga baka rasa aljanu a kanka,amma karka damu nasan maganin ka”.

Sauke ajiyar zuciya SUDESS ya yi kafin cikin muryar wasa ya ce “Afuwan very sorry my bro wallahi kaina ya ɗau zafi,kasan bazan yima haka da gangan ba,wallahi ayyuka ne sun sha kaina,amma yanzu kasan idan na je da wannan Girls ɗin akwai matsala,kasan halin goggo rigima ce zata barke,ka lallaba yarinyar ta faɗi unguwar su da gidan iyayenta ka mayar da ita kawai,ni ina ganin wannan ne hanya mafi sauki ko?”. Ya karasa maganar cikin muryar tausayi dan yasan halin bro ɗin nashi da tausayi,idan ba haka ya yi ba to ba makawa ya dawo mai da yarinyar nan,shi ko wallahi ya manta da ya kai ajiyar ta.haba ina dalilin wannan tashin hankalin a haka ake cewa ya yi aure,sanadin hawan jini ya sameshi.

Jin ya yi shiru ya kara cewa “Pls bro kasan kai ne dole na,ba yadda zan yi” cewar SUDESS.

“To kana ji kafin ka tafi Abuja ka zo mu tattauna yadda za’a yi,amma wallahi idan har ka tafi baka zo ba saina kawota Abuja,dan Nasan halinka kamar yunwar cikina”.
Yar dariya SUDESS ya yi jin abinda Doctor Mujaheed ya ce,nan take ya ɗan ji san yi a ranshi,dan shi harga Allah bazai iya tafiya da yarinyar nan ba,zata tadomai fitinar kannan mahaifan shi na sai ya yi aure.
Daga haka suka katse kiran,harya juya yana gyara kwanciyar shi dan bacci yake ji sosai,ya kara jin karan wayar a karo na biyu.Har zai katse ya ga Nomber Uncle Hasan dammmmmmm ya ji gaban shi ya bada wani sauti dan yasan ba magana mai daɗi ba ce idan yaga kiran wannan Uncle ɗin na shi.

Chakwakiya iya chakwakiya ???????? to wai ya zata kaya ne da rayuwar SUDESS?”.

Pls masoya kada ku manta wnn Book ɗin na kuɗin ne

            *By*

  *AUTAR AREWA*


 ✍️✍️✍️✍️✍️✍️.

???????? SUDESS????????

         *Written story*


                 *By*

 *AUTAR AREWA*

Paid Book ne akan farashi mai sauki ₦500 kacal za ki sha krt cikin kwanciyar hankali.Ta wnn Account Nomber 3125654602 Rukayya Idris first Bank, ki turo shaidar biyan ki ta wnn Nomber 08162385196,ko hoton katin MTN pls banda VTU ???? idan kinsan ba ki shirya ba karmu ɓatawa juna time.

Bismallahi Rahamir Rahim.

Free page 5️⃣

Pls banyi editing ba.

????................Sororo ya yi yana kallan call ɗin har Saida ta katse bai motsa ba,wani kiran ne ya kara shigowa still dai Uncle Hasan ne,cikin sanyin jiki ya katse kiran kafin ya kira shi.Ringing ɗaya ana biyu Uncle Hasan ya ɗaga.Da sauri SUDESS ya ce "Assalamu Alaikum Uncle barka da safiya,Ina kwana,ya iyali?".

A dakile Uncle Hasan ya ce “Lafiya, ina maganar da muka yi da kai,kasan yau saura sati biyu ya rage wa’adin da ka ce a baka ya cika ko?ina fatan baka manta ba?”.
Daman nasan karshen maganar kenan,kai wannan mutumi baya san na zauna lafiya cewar SUDESS a cikin ranshi.
Maganar da Uncle Hasan ya Kara yi ita ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula.
“Kana jina ko?”

“Eh Uncle ina jinka,ban manta ba insha Allah kafin time ɗin zan yi abinda ya kamata”
Cewar SUDESS yana kara sunne kai tamkar yana gaban shi.

“To to hakan dai zai fi,dan wannan karin idan ka kawo mishkila to zaka ga abinda zai biyo baya”
Ya ji Uncle Hasan ya faɗa kafin suka yi sallama ya katse kiran yana dafe goshin shi daya ji yana saramai tamkar zai faɗo.A hankali ya mayar da kan shi jikin pilo yana sauke ajiyar zuciya.Agogon da ke like jikin bangon ɗakin ya kalla ganin tara saura mintuna ya yi saurin ta shi ya nufi toilet yana sake-sake a ranshi na yadda zai ɓullowa wannan matsalar guda biyu,dan ya fahimci wannan karin ba zasu kara yimai uziri ba.

   Karfe 10:20 daidai ya fito parlon shirye cikin blue shadda mai adon baƙin zaren ulu a gaban rigar sai bakar madaidaicyar hula daya ɗora saman kanshi sai tashin kamshin turaren Uhud yake yi fuskar shi fes gwanin sha'awa .saida ya zauna saman doguwar kujera kafin ya ɗaura agogon shi na silver mai kyau,wayar shi ya ɗauka yana niyyar kiran Salisu ganin har yanzu bai fito ba,sallamar shi ya ji daga bakin kofa haka yasa ya fasa kiran.karasowa Salisu ya yi yana gaishe da ogan na shi,amsawa ya yi yana cewa "Pls salisu time fa yana kurewa,bana so muyi tafiyar dare fa saboda kasan hanyar sai a slow.bedroom Salisu ya wuce ya ɗauko trolyn kayan ogan na shi da tarkacen system ɗin shi ya kai cikin mota,basu tsaya yin break ba suka fita,direct gidan Doctor Mujaheed suka nufa.cikin mintunan da basu haura sha biyar ba suka iso kofar gidan,saida suka yi horn kafin aka wangale masu gate suka kutsa hancin motar su cikin harabar gidan.Salisu yana daidaita parking SUDESS ya nufi cikin gidan,door bell ya danna cikin two minutes aka buɗe mai kofar falon.Cikin natsuwa ya shiga da sallama ɗauke a bakin shi a tsakiyar kujerun ya samesu saman capet suna break ya karasa bisa kujera mai cin mutum ɗaya ya zauna yana cewa "washhh Allah na,na ga ji sosai,ku bani abinci na ci ina jin yunwa".

Da sauri maman Sudess (jenior) ta tashi ta fara haɗamai tea mai kauri da soyayyar doya sai yar miyar jajjage ta ɗanyun kayan miya da aka soyata da kaɗaɗɗen kwai sai kanshi ke ta shi.

A fakaice Doctor Mujaheed ya kalli SUDESS kafin ya ce “Wallahi bro tausayi kake bani,yanzu da kana da mata duk inda zaka je ka tafi da ita kafin ka shirya an haɗama abinci mai rai da lafiya,amma yanzu duk ka zama sorry”.

Shidai SUDESS ko kallan shi bai yi ba,kasan capet ɗin ya sauko ya wanke hannun shi a cikin wata faffaɗar roba kafin ya yi bismalla ya fara cin soyayyar doya,a hankali yake ci yana kurɓar ruwan zafin.Sai da ya ɗan ci sosai,kafin ya dubi Hannatu yana cewa “Pls maman Jenior Salisu yana wace,ku ba shi abinci”.
Da “To”ta amsa kafin ta fara haɗama Salisu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Leave a Reply

Back to top button