SULTAAN 5
???? S U L T A A N
Mss Flower????
FITATTU HUƊU????
RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE
FIRST CLASS WRITERS ASSO…
*05*
LAILA POV
Daidai lokacin Amma ta faɗo ɗakin, Abbu na biye da ita da hanzari. Laila wani irin kuka take tamkar wadda ake wa zarar rai sannan ta kifa kanta kan gwiwoyinta tana cewa “ba zan taɓa yafe wannan tozarcin da kuka yi min ba, da saninku ɗanku ya yiin fyaɗe”
Amma wani irin gigicewa ta yi ta jawo mayafinta ta rufa wa Laila tana cewa “don Allah ki yi haƙuri, ki rufa mana asiri”
Share hawayenta ta yi tare da miƙewa ta ce “tabbas an wulaƙantani, bawa ƙasƙantacce ya yi min fyaɗe sannan ki ce na rufa muku asiri!”
Amma haɗe hannayenta biyu ta yi ta durƙusa gaban Laila tana cewa “ki dubi girman Allah kar ki mana sharrin da zai iya jawo mana rashinsa, shi kaɗai ne sanyi garemu, ba za mu iya jure rashinsa ba” hawaye na fita a idonta
Laila cikin wani irin fushi ta ɗauke Amma da mari ta ce “har za ki ce sharri na yi masa, bayan kin tarar da ni a yanayin nan, ke nan da haɗin bakinku dai kan tozarcin da ya yi min”
Sultaan wata iriyar zabura ya yi tare da ɗaukan hannu zai wanke Laila da mari, Amma ta yi caraf ta miƙe tare da riƙe hannunsa, idanunta na fidda hawaye ta shiga juya masa kai
Laila ta saki wani irin shu’umin murmushi ta ce “bar shi ya ja wa kansa da iyayensa bala’i, ƙasƙantacce sakarai kawai!” Ta ce tana ɗaukar rigarta ta saka sannan ta fice bakinta ɗauke da shu’umin murmushi. Tun kafin ta ƙarasa gida ta fara kuka tamkar jiniya wanda ta ja hankulan mutanen da ke wajen, abin ka da ƙaramin ƙauye masu son tsurku wasu suka dinga tambayarta me ya faru sai dai ba ta tanka kowa ba haka ta shige gida, tsaye ta tarar da mahaifanta hankalinsu tashe alamun rashin ganinta a ɗakinta, zubewa ƙasa ta yi tana wani irin gunjin kuka tare da cewa “ya tarwatsa min rayuwata, ya cuceni, bawa ƙasƙantacce ya wulaƙantani, ya yi min fyaɗe!”
Cikin wani irin tashin hankali Ammanta ta ce “wa ya yi miki fyaɗe!, Ya aka yi kika bar gidan nan!” Tana faman girgizata cikin tsantsar firgici
“Ammaaaa!” Ta ja sunan cikin kuka tare da rungumeta
Amman ɗagota ta yi tana cewa “ki min magana, ki min magana!”
“Sultaaaaan!” Ta ce daidai lokacin ta ja wani numfashi tare da zubewa alamun ta suma.
Mahaifinta da fuskarsa ta yi mugun ja ya ce “na rantse da Ubangijin da ya halicceni sai na datse gabansa ko da dukka dukiyata za ta ƙare!”
SULTAAN POV
Jiki babu ƙwari ya durƙusa kan gwiwoyinsa tare da ɗora hannunsa kan Ammansa da ke ta wani irin kuka, gabaɗaya ya rasa nutsuwa don kuka Amma da Halime ke yi, yayin da kana ganin fuskar mahaifinsa ka san yana cikin tsananin tashin hankali.
Amma ta ɗago kai ta kallesa tare da cewa “ka tafi Sultaan in ka kai safiya a garin nan kasheka zasu yi, gara ka gudu da na ga gawarka”
Girgiza kai ya shiga yi, can ya fizgo magana da ƙyar ya ce “ba zan taɓa tafiya na bar ku ba, idan na tafi Lelu fa?, Ba zan iya jure rabuwarmu ba, zan karɓi duk hukuncin da zasu yi min, ina da yaƙinin mai kowa da komai zai fitar da ni”
“Ka tafi, ka sani sarai ko sun bar ka da ranka hukuncin da zasu maka ba za ka ƙara kwanaki a duniya ba, da mu rasaka a doron ƙasa, gara mun yi nesa da kai, ko ba komai za ka kasance a raye cikin tunani da zukatanmu” cewar Halime da ta riƙe hannunsa tana wani irin kuka
“Ka tashi ka tafi!” Cewar Amma
“Babu inda zan je, ba zan taɓa barinku ba!” Ya ce cikin ƙunar rai
“Sultaan! Ka je, Allahn da ya yi mu zai kula da mu” cewar Abbu cikin wani irin rauni.
Girgiza kai ya shiga yi yana cewa “a’a”
A fusace Amma ta miƙe tare da faɗawa ɗaki, babu jimawa ta fito hannunta da wani ƙunshi haɗe da gorar duma, miƙa masa ta yi hawaye na fita a idonta ta ce “ka je Sultaan”
Bai amsa ba, sai ƙuri da ya yi mata yana mai jin raɗaɗin hawayen da take zubarwa har cikin zuciyarsa.
“Ka tafi kar ka bari zuciyata ta fusata na yi aman abin da zai baƙanta maka, mu rabu rabuwa ta har abada!” Ta ce tana kauda kanta daga dubansa ƙwallarta ba ta yanke ba
Cikin rashin kuzari ya ƙarasa gabanta tare da tsugunnawa ya ce “Amma ban san kowa ba sai ku, idan na yi nesa da ku ina zan je?, Zan jure kowani hukunci zasu min, amma ba zan iya jure rashinku ba”
“Hukuncin da zasu yi mana fa?, Idan suka sameka a tare da mu, tunaninka hukuncin zai tsaya iya kanka ne?, Har da mu zai shafa, ko don ba mu muka haifeka ba?, A lokacin da ka so haiƙewa yarinya ba ka yi tunanin hukuncin da zai biyo baya ba, sai da ka gama bajakolinka akanta?” Ta ce ɓacin rai na bayyana a fuskarta
A tsorace ya ɗago kai ya ma kasa magana jin irin furucin da ke fita daga bakin Ammansa duk duniya ya san in kowa zai ce ya aikata zina Amma ta sani ba zai yi ba, yau da bakinta take jifansa da irin wannan kalami, abin da ya kuma ɗaga masa hankali wai ba su suka haifesa ba, cikin rauni idanunsa na ɗigar ƙwalla ya ce “Amma ki daina, na sani ba haka ba ne a zuciyarki, ki daina”
“Na yi danasanin riƙonka Sultaan da na san wannan halin za ka jefamu da tun kana jariri ban yarda na karɓeka ba, ka ɓace min da gani, na tsaneka, na tsani ganinka mazinaci, tsintacciyar mage kawai!” Ta ce tana mai nuni da ƙofa
Wani irin sarawa kansa ya fara kamar zai tarwatse gida biyu, hakan ya sa ya tallabe tare da kai dubansa kan Abbunsa, ƙarin bayani yake nema amma hawayen da ke fita daga idon Abbu ya gama tabbatar masa da duk abin da yake son sani.
Amma ta ware ƙunshin da ke ɗaure cikin baƙin ƙyalle, ta zaro wani tattausan bargo na jarirai wanda da gani kasan ya yi shekara aru-aru, ta cilla shi kan Sultaan ta ce “cikin wannan muka tsinceka, hannunka riƙe da sarƙar da ke wuyanka, na gama faɗin komai, don haka ka tashi ka tafi, bani sake buƙatar ganinka”
Halime ta fashe da wani irin kuka ta ce “Amma don me?, Don me za ki tona sirrin da ku ka binne tun kafin zuwana duniya, don me za ki tarwatsa zuciyarsa don kina son ya tafi bayan tashin hankalin da yake ciki a yanzu, kina son ya tafi amma kin duba in ya tafin a hanya zuciyarsa na iya bugawa?”
Ya ɗago idanunsa da suka rine ya sauke kan Halime, ya aka yi ta san wannan sirrin da shi da aka haifeta a idonsa bai taɓa ji ko gani ba, cikin wani irin rauni ya ce “gaske ne?”
Hawaye na fita a idonta ta matse hannayensa ta ce “gaske ne amma suna sonka sama da soyayyar da suke min Ni wadda suka haifa, da bakinsu suka furta hakan a tunaninsu babu mai ji, komai Amma ta faɗa maka ba haka ba ne, ba su taɓa yi maka kallon wanda ba jininsu ba, kar ka yadda da zancenta, ka tafi don tseratar da rayuwarka amma ba don nisanta da mu ba”
Ya rintse idonsa yana fata ina ma mafarki ne yake yi, da ya ji daɗi ƙwaran gaske da wannan baƙar gaskiyar.
Abbu ya dafa kafaɗarsa ya ce “ka je ko don mu ma mu tsira, Allah Ya yi maka albarka ya kuma haɗa fuskokinmu da alkhairi”
“Ya halatta bawa ya gujewa ubangidansa ne?” Ya fizgo maganar
“Kai ba bawansu ba ne, don ba ni ne mahaifinka na jini ba, ka je da ƴancinka!” Cewar Abbu
Idanunsa ya maida kan Amma da idonta ke a rufe ya ce “Ammaaaa!”
“Ba na son buɗe idona na ganka, ka cutar da mu Sultaan, abu na ƙarshe da zan nema a wajenka shi ne ka sha abin da ke cikin gorar nan idan har ka bar cikin garin nan, alfarmar da za ka min ke nan ladan ɗawainiyar da na yi da kai” ta ce cikin sanyi