SULTAAN 5

Gorar dumar kawai ya ɗauka yana jin wani irin jiri na neman kwasarsa yayin da bugun zuciyarsa ya kasa daidaita, ya miƙe tare da nufar ƙofa batareda ya kuma duban kowa daga cikin iyayen nasa ba. Halime ta faɗa ɗaki da gudu ta ɗauko asusunta na ƙasa ta yi waje ta bi shi, tafiya yake kamar wanda ke cikin maye tsabar tashin hankalin da ya yi masa yawa, hannunta ta saka ta riƙesa ta ce “ka tafi da wannan, ka biya kuɗin jirgi, watarana za mu gana in sha Allahu!”
Ƙura mata ido ya yi don gani yake tamkar duk abin da ke faruwa a majigi ne. Hawaye na fita a idonta ta rungumesa ta ce “ina sonka Yayana”, ganin kamar ba ya cikin hayyacinsa sai ta kama hannunsa suka yi ta tafiya har bakin ruwa, cikin sa’a sun tarar ana lodin jirgin ruwa da zai lula can wata uwa duniya, ta ɗauki bankin ƙasar ta rotsa a ƙasa, coins da suke amfani da su suka bayyana turmus, ta yi murmushi zuciyarta cike da jindaɗin ganin yawan kuɗin ko ba komai zasu riƙe Sultaan ɗin tsawon kwanaki, biya mai kuɗin jirgin ta yi yayin da ta zuba masa ragowar kuɗin a aljihunsa, ta kama hannunsa ta shigar da shi ciki, sannan ta ɗago kai ta kallesa hawaye na ɗiga a idonta ta ce “watarana za mu gana ko?”
Sai a lokacin tunaninsa ya fara daidaita hawaye suka zubo masa ya riƙe hannunta ya ce “zan tafi don na sama wa Amma farin ciki, zan yi nesa da ku don ka da na jefaku a halaka, zan rayaku a zuciyata a kowacce rana”
Gyaɗa kai take hawaye na fita a idonta, yayin da take kuma sakin murmushi sannan ta fita a jirgin ruwan, don an gama lodi, bakin ruwan ta koma tana ɗaga masa hannu.
Hawaye tamkar mace a karon farko suka kasa tsayawa daga gudana a idanuwansa, wani irin yanayi yake ji a zuciyarsa wanda babu mai iya kwatantawa, a hankali jirgin ruwan ya fara tafiya, yana hango ƙanwarsa da ke zubar hawaye tana ɗaga masa hannu, sharrin Laila bai masa zafi ba, amma furucin Amma shi ya tunzurasa, a hankali jirgin ya fara nisa har ya daina ganin Halime…
DESTINY CALLS
????FITATTU HUƊU????
????SULTAAN # Nml grp ~N~ 300 vip ~N~ 500 via 1401611541 Access bank, shaidar biyanki ta wannan numbern 08167888934
Mss Flower????
TSINTACCIYA
Nimcyluv
Baƙar fata
Autar manya
DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo
Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218
Mss Flower???? 08167888934 For more information????