SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mikewa yayi ya Fita zuwa Falon Ya Fita A Stirs dinda zai Kaishi xuwa part dinsu Mami yaga Mahnoor tana K’okarin Zuwa side dinshi. Murmushi tai Tana Turo baki
“Bro Masroor tunda ka dawo kah daina tayani Assignment, Kuma kah daina Wasa dani”
Hararanta Yayi da Wasa
“Ai na lura neh yanzu bakida Kunya”
Kara Turo baki Tai Sannan Tace
“Mami toh na K’iranka”
Hannunta Ya Rik’e yana cigaba da Tsokanata Har suka K’arasa Side din Mami, Falon K’asa Suka sauko inda Mami ke Zaune tana Rubuce Rubuce a Wasu Takardu. Zama Yayi Sannan Yace
“Mami gani”
Dago Kai tai ta K’alleshi
“Son Yaya dai is anything Wrong”
Yadan Girgiza kai Yana cewa
“Bbu Komai I’m Fine”
Girgiza kai tai na Rashin Fahimta tace
“Shiknan, Pls akwai Mutane a Waje da Suke bukatar temako”
Kudi ta Dauko Bandir Guda Uku Yan Dubu D’aya ta Mik’amai
“Kah Rabamusu”

Girgiza kai Masroor Yayi Yana Y’ar murnushi
“No Mami zan Basu ki Aje Wannan”
Mik’ewa Yayi ya K’alli Mahnoor data Makaleshi Yana cewa
“Tho Sakeni Naje inda aka aikeni koh”
Turo baki tai tana buga k’afa a kasa
“Nidai muje tare”
Baice mata komai bah Ya Haura sama zuwa dakinshi, Bedside drawer’n dakinshi ya bude yadauko kudi Ya fito. Tsaye ya Samu Masroor Tana jiranshi, Hannunshi ta kama suka Fito farfajiyan Gidan. Ma’aikata neh burjik kowa nata aikinshi, Daga K’ai yayi inda Wasu Maza Masu aikin Gidan Ke Wanke Motocin Daddy. Tsayawa yayi chak yana K’allansu, Su sam mah basu lura dashi bah

Hannun Mahnoor Ya saki ya K’arasa Wajan motocin Y’ana K’allan daya daga cikinsu dak’e wanke Taya Yanata Surutu. Duka Sauran Suk’a zube suna Gaidashi, wanda ke Tsugunen Ya Dago Dasauri Suka Hada Ido Nan da Nan Jikinshi Ya soma Rawa Ya duk’ar dakai yana Raba idanu

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 81 to 85*

Duka sauran suka zube Suna Gaidashi, Wanda ke tsugunen ya dago dasauri suka hada ido nan da nan jikinshi ya soma rawa ya Duk’ar dakai yana raba idanu. Bude Baki Masroor Yayi da niyar magana ya fasa, Juyawa yayi yabar wajan dasauri Cikeda Mamakin Ganin Saurayin nan da suk’e tareda marakunyar Yarinyan datamai Fitsara dazu. Kamar yanda Mami ta Umarta haka yayi, duk dunbin Mutanen dake Wajan saida ya raba nusu dubu d’ayi D’ayi Shida Mahnoor Sannan suk’a Shigo Gida, Saurayin nan ya Y’ara bi da K’allo Sannan Ya nufi Side dinshi ta K’ofar Waje…

K’iran Sallan Asubah ne ya tada Sulthana ta Mik’e dakyar saboda yana jikinta ke mata ciwo, cikin gidan ta shiga tai alwala da sauri sauri ta dawo zaure ta shimfida buhu tai Sallah dan tasan dah Baffa ya fito bah lallai baneh ya barta tai sallah, tana idarwa taji k’aran bude kofan Baffa, Saida yayi alwala sannan ya nufo zauren..

Haskata yayi da torch light Ganinta zaune yasa ya bata fuska yace
“Kindai san bah ruwa a rijiya koh, Maza ki tashi duk inda xaki samo ruwa kije ki samo”
Mik’ewa tai da Sauri har Saida tadan saki Y’ar K’ara, nan da nan idonta ya ciko da K’walla, Jikinta duk Ciwo yak’e mata kuma a haka Baffa yace ta dibo Ruwa. Yana Fita ta koma ta zauna ta fashe da kuka a Hankali, Jikinta take Tabawa tana Kuka Sosai, K’ayanta dake Cikin Poly bag ta fara bincikawa, Wani Zani ta Ciro ta rungume ta k’ara Fashewa da kuka tana Turo Baki
“Umma meyasa Zaki tafi ki Barni, Baffa Baya sona. Nima inaso na mutu nazo inda kike”
Kuka take Sosai, sai bataji Zuwan Mama bah sai hasketa da Torchlight datai

“Sulthana Kukan meh Kike”
Mik’ewa tai dasauri ta share Hawayen Fuskanta,
“Babu komai”
Zanin ta mayar inda yake Ta nufi Cikin Gidan, Bokitin K’arfe ta dauka ta Fita. Abinda Ya daure mata kai bai Wuce K’in Amsa gaisuwanta da Ameenatu tayi bah. Haka ta Cigaba da Tafiya tana Mamaki, Duk Gidan Tasan Masu Santa daga Ameenatu sai Mama, Har ta Nufi Rijiyan Burtsasai sai ta tuna Rijiyansu Sadiya bai K’afewa. Murmushi ne Ya subuce mata ta nufi gidan dasauri..

A tsakar gida taga Maman Sadiya da ita sadiyar suna alwala, dagowa sukai tareda amsa sallaman datai cikeda mamakin ganinta a wannan lokacin. Mama na gamawa ta mik’e tace
“Yaki nan Sulthana”
Bokitin ta aje ta k’arasa inda Maman take, Hannunta ta rik’e duka biyu tana haske Jikinta da torchlight, sanin shedan duka yasa ta girgiza kai ta dago ta k’alleta
“Waya dukeki Sulthana”
Shehekan kuka ta soma tana turo baki a hankali
“Baffa neh ya dukeni jiya”
Sadiya ta k’araso wajan itama fuskanta bah walwala
“Sulthana me kika fito yi da asubah”
Bokitin data aje ta k’alla
“Koba Baffa baneh yace naje na dibo ruwa”
Girgiza kai Mama tai cikeda takaicin Hali irin nah Mallan Jamilu, Bokitin ta dauka da k’anta ta diban mata tareda daurata akai ta tafi gida. Sahu tai Yakai Goma daga Gidansu zuwa gidansu Sadiya, Duk sanda taje Mama je diban mata ta kuma Daurata ta nufo Gida. Ana K’arshen Mama ta zaunar da ita taci abinci ta Koshi sannan ta nufi gida Cik’eda murna..

Yauma gyadar ta dafa K’amar kullum, A tray ta juye Tana kici kicin dauka, Ameenatu ce ta shigo cikin gidan da sallama hannunta dauke da leda da alama daga aike take, K’allanta tai tana d’an murmushi
“Yaya Ameenatu dazu na Gaisheki baki amsa bah, Koh baki ji baneh”
Harara Ameenatu ta wurga mata tareda kauda kai, Mamaki sosai Sulthana har ta k’asa boyewa
“Yaya Ameenatu menai miki, dan Allah kiyi hakuri”
Tsaki Ameenatu tai tana nunata da D’an Yatsa
“Keh karna k’arajin kin kira. Sunanan a gidan nan idan bah haka bah wallahi zaki sani”

Bata jira mai Sulthana zatace bah ta bar wajan tana tsaki, hawaye ne masu zafi suka gangaro mata
“Shiknan Ameenatu ta daina santa, yanzu ina zata waiga taji sanyi”
Durkushewa tai ta fashe da kuka mara sauti, Jin k’amar sheshekan kuka yasa Mama ta fito dan ko ba’a fada mata bah tasan Sulthana neh. Durkushe ta sameta gaban Gyadan,
“Sulthana kedai kuka bai miki wuya, mai makon kizo ki gayamin ai dana dauraki”
Mik’ewa Sulthanan tai Mama ta daura mata gyadan tareda mata Kashedin K’arta kula maza, Sannan idan har tasan maza na mata juye tho ta daina. Tho kawai tace ta fita zuwa Bakin kasuwa inda ta daba Zama. Tana Cikin Tafiya taji ta bayanta ana Cewa
“Sulthana bako gaisuwa”
Juyawa tai dasauri, K’allanshi ta tsaya yi nadan Wasu Seconds. Ganin bata ganeshi bah yasa yayi murnushi ya k’araso inda take Tsaye
“Baki ganeni bah koh”
Kai ta gyada mai batareda tace komai bah…

Murmushi ya K’arayi yana k’allanta
“Nine likitan dana dubaki ranan a Chemist”
Sai a sannan ta tuna, idanunta ta sauk’e k’asa tace
“Ina Wuni”
Amsawa yayi yana Mata murmushi, Ganin Tana kokarin tafiya yasa yasha gabanta dasauri
“Ina zaki bamu gama magana bah”
Turo baki tai idonta ya ciko da Kwalla
“Dan Allah kaban hanya na wuce”
Ganin yanda Hawaye ke gangarowa a idonta yasa ya matsa jiki a sanyaye ta wuce, Binta da K’allo yayi harta bace ma ganinshi. Ajiyan zuciya ya sauke, Zuciyarshi ta shiga raya mishi
“Yarinyan nan tana cikin Damuwa”
Kamar zai bita ya Fasa ya shiga mota ya nufi Cikin Garin Kano…

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 91 to 95*

Turo baki Masroor yayi ya mik’e yabar Dinning din
Girgiza kai Mami tai
“Ai kai bakasan Maganan aure”
Mik’ewa Daddy yayi
“Zan Tafi Office daga nan zanje Meeting da Party chairman”
Fatan Alheri Mami tai mai ya fito bodyguards dinshi suk’a budemai Kofan mota ya shiga, Driver yaja Sukabar Gidan Tareda Suran Bodygyards din da Suke a wata motar daban..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button