SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar Jiya yauma Bakin K’asuwar Masroor yazo anma baiga Sulthana bah, yaranda ke wajan ya tambayan sukace mai bata zo bah. Hankalinshi ne ya tashi, motarshi ya shiga ya shiga cikin kauyen, duk inda ya kutsa da mota K’allanshi ake bama kaman mata. Tsaki yayi ya kauda kai ya cigaba da driving, ya dad’e yana kewaye Garin kafin ya koma gidah ranshi babu dadi..

Sulthana kuwa tana dauk’ar tallanta tasha ta nufa dan ma k’artaga Wannan dan Birnin, Batako dad’e bah ta saida Gyadarta ta dawo gida cikeda Farinciki. Abu guda keci mata tuwo a kwarya rashin Sake fuska da Ameenatu batamata yanzu, Hakan yasa ta yanke hukuncin ta sameta taji koh wani laifin tai mata. Tana zaune Zaure Baffa ya fita wajan Almajiranshi, tana ganin ya fita ta mik’e ta shiga cikin Gidan, Dakinsu Ameenatun tai Sallama ta Shiga, Kwance ta samu Ameenatun akan Sallaya. Jin muryan Sulthana yasa ta mik’e zaune
“Keh Wacce irin Dabba ce idan anyi Sallama bah bari ake sai mutum yace a shigo bah”
Dagowa Sulthana tai dasauri tana K’allan Ameenatu da mamaki, tunda take da Ameenatu bata taba mata Fada bah sai yau. Idonta neh ya ciko da K’walla ta zauna dabar a Kasa tana k’allan Ameenan daketa cika tana batsewa
“Yaya Ameenatu mai nai miki kike fushi dani, idan namiki magana bakya amsa min”
Mik’ewa Ameenatu tai tana nuna mata k’ofa
“Fita daga dakin nan ko yanzu nai miki dukan tsiya, dah ina ganin laifin Baffa dayake azaptar dake ashe ko da Gaskiyar sa”
Kuka Sulthana ta fashe dashi

“Dan Allah yaya Ameenatu kiyi haquri idan na miki laifi bazan sake bah”
Mari mai rai da Lapia Ameenatu ta dauke Sulthana dashi
“Zaki fita koh saina babbala ki”
Dagudu ta fita ta nufi zaure tana cigaba da kuka, kukanta neh ya fitoda Mama daga daki
“Lapia meke Faruwa Sulthana”
Lekowa cikin gidan tai ta zube gaban Mama tana cigaba da Kuka, Dagota tai tsaye
“Yi Shitu fadamin menene”
Tsagaita kukan tai
“Yaya Ameenatu ne ta mareni bansan menai mata bah”
Da mamaki Mama tace
“Mari?”
Kai Sulthana ta gyada tana cigaba da kuka, Lallashinta Mama tai dakyar tai shiru ta koma zaure ta zauna tareda hade kai da Guyiwa…

Mama ta kwalama Ameenatu kira ta fito tana gungunai,
“Haba Ameenatu mai Sulthana tai miki da zaki mareta, ki tuna fah keh kadai take rab’a tanajin dadi”
Tsaki Ameenatu tai tareda kauda kai
“Mama ni yanzu kawai naji na tsani Sulthana”
Da mamaki Mama ta K’alleta baki bude
“Kinko san Abinda kike fada Ameenatu”
Gyada kai Tai tareda barin Wajan, Abin ya dad’e yanaba Mama mamaki, Tabbas akwai wani abu da Ameenatu ke boyewa..

Bayan isha’i Sulthana na Kwance Yaro ya shigo zauren harda zai shiga cikin Gidan Ya dawo inda tak’e Kwance
“Sulthana ana sallama dake a Waje”
Mik’ewa zaune tai dasauri tareda zaro ido
“Wanene?”
Girgiza kai yaron yayi
“Bansan waye bah, Wani ne dai a mota”
Zazzaro ido take cikeda tsoro, Kaje kace bana nan. D’an jim Yaran yayi sannan yace
“Jiya yazo wajan yaya Ameenatu kila sako zai baki ki kai mata”
Jin haka yasa ta mik’e tadau dankwalinta ta daura ta fito kofar gidan. Zaune yake cikin mota yana latse latse a wayanshi, k’arasawa tayi bakin Motan cikin muryanta mai Sanyi tace
“Ina Yini”
Dagowa yayi ya k’alleta da Murnushi kwance kan Fuskanshi
“Lapia lau Sulthana, Ya gida”
Lapia tace a takaice..

Fitowa yayi daga cikin motan ya tsaya, shiru ne ya biyo baya nadan mintina Sannan ya dago ya K’alleta kanta a k’asa yace
“Sulthana”
Dagowa tai tadan K’alleshi sannan ta maida kai tace
“Na’am”
Ajiyan zuciya ya sauke yace
“Shekaranki nawa?”
Dan Jim tai kamar karta fadamai sai kuma ta dan dago batareda ta kalleshi bah tace
“Sha hudu”
Jinjina kai yayi yace
“Ajinki nawa a makaranta”
K’ara dago kai tai ta K’alleshi tareda girgixa kai
“Bana zuwa makaranta”
Kallanta yayi da Mamaki
“Meyasa?”
Kauda kai tai tareda turo Baki
“Baffa ya cireni”
Kallanta ya tsaya yi, Abinda ya fahimta da Yarinyan shine tana fuskantan kiyaiya a gidan zai iya cewa wajan kishiyar mahaifiyarta kuma abinda ya burgeshi da ita sam batasan wani bare yasan halinda take ciki.

Hakan ya burgeshi sosai, Muryanta yaji tana cewa zan shiga gida kada Baffa ya fito ya ganni. Bata jira mai zaice bah tabar wajan ta shiga cikin gida. Kurri yana kofar gidan, tausayin Sulthana ke ratsa shi. Runtse ido yayi ya bude a hankali yace
“Ina sanki Sulthana, zan iyayin komai a kanki. Insha Allahu zaki fita daga k’angin da kike ciki kwanan nan”

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 86 to 90*

“Yarinyan nan tana cikin damuwa”
Kamar zai bita ya fasa ya shiga mota ya nufi Cikin garin kano. Zama tai Bakin Bishiyan Data saba Zama, Gyadan ta soma saidawa kamar yanda ta Saba. Atika dake kusa da ita tana saida Rogo ta yafici Ladi tana nuna mata wata hadaddiyar mota datazo wucewa
“Kai Ladi ji Wachan motan, Tafdi! Ni tunda nake ban taba ganin mota mai sama a bude bah”
Kyalkyacewa da dariya ladi tai tana tafawa
“Kai Wallah Motan nan Akwai Kyau, Allah ka bamu irin wanna motan”
Jin Yanda suke zuzuta motan yasa Sulthana ta dago ta K’alli motan, Lallai kuwa motan yanada Kyau, Murmushi ta soma tanabin Motar da K’allo. Duk mutanen dake K’asuwan kowa bin motar yake da K’allo cikeda Sha’awa, Wanda ta gani Cikin motan neh yasa Fara’ar dake Fuskanta yakau, Hijabin Fuskanta ta Turo Gaba ta Rufe Fuskanta dashi..

Zagaye yake yana yatsine Fuska, Waje ya samu yayi Parking Sannan ta fito. Mata sa binshi da K’allo suke harda Mazan, Dan D’an gayu neh na K’arshe. duk gungun Yara masu talla daya gani sai ya tambaya tareda Fadin sunanta anma duk suce basu santa bah, Ganin Yana Kokarin nufosu yasa Sulthana ta mik’e tana K’okarin daukan trayn Gyadan tah k’araf suka hada ido, Dauke kai tai Ta dauki Trayn Gyadan ta Fara tafiya. Binta Yayi tateda Kiran sunanta, Juyowa tai ta Murguda mai Baki
“Kah daina kiran sunana kuma ka daina bina”
Murmushi Yayi yanda ta murguda bakin Saita k’ara mai kyau
“Meyasa zakice na daina binki”
Batareda ta juyoba tace
“Nidai Dan Allah ka daina bina kada Yaya hafsatu ta ganmu taje ta fadama Baffa, Idan ta fadama Baffa dukana zeyi, Jiyama saida ya dakeni”

Tausayi ta bashi Ya sha gabanta yana K’allanta
“Kiyi Hakuri nasan mu muka ja miki dukah koh”
Batace mai komai bah tana k’okarin tafiya, hannu ya daga mata Yana cewa
“Tsaya mana, kudinki na jiya nakeso na Baki”
Kauda kai tai gefe
“Kah barshi, nidai dan Allah ka bani Hanya na Wuce”
Matsa mata Yayi ta soma Tafiya Yana K’allanta, meya tuna ya bita da Sauri tareda shan gabanta
“Tsaya tho kiji”
Tsayawa tai hannunta d’aya a kugu
“Inaso gobe mu hadu a Inda kike saida Gyada kamar wannan lokacin kinji”
Batacemai Komai bah ta cigaba da tafiya abinta. Binta yayi da K’allan tausayi, A Ranshi Yana raya
“She’s Cute n Young, She need help. No matter how Zaki Kasance Cikin Farinciki nan daba”

Motarshi ya nufa dan komawa gida, Yara ya gani Yayyabe da Motan Sunata Shafawa, K’arasawa yayi dasauri ya koresu. Ganin Sunki Tafiya yasa ya Dauko bandir din yan Hamshin ya soma Raba Musu, ai a nan yaga wawaso harda manya. Tausayama Halinda yan K’auyen suke ciki yayi. Motan ya shiga ya tada Yabar kauyen Cikeda Tausayin Sulthana…

Gida Ya nufa Kai Tsaye, Horn yayi masu Gadi Suk’a budemai kofa, Saida yayi Parking Sannan ya Fito. Bodyguards din dadd ya gani a tsakar gidan, Murmushi Yayi
“Wel daddy is back”
Main palour ya nufa tareda Danna Bell, wata mai Aiki ce ta bude Tareda Zubewata gaidashi, Bai amsa bah ya Shiga falon Yana Fara’a Baiga kowa A falon bah. Wani Corridor ya nufa wanda zai sadashi dah Dinning area, a nan ya gansu zazzaune suna Lunch. Sallama yayi ya k’arasa ya rungume Daddy Yana dariya,
“I Missed uh Daddy”
Murmushi Daddy yayi Yana Shafa Kanshi cikeda Zolaya Yace
“Sai Kace nayi shekara kwana biyu fah nai”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button