SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Turo baki Mahnoor tai tareda Rungume Hannayenta
“Daddy kacema Bro Masroor ya daina Rungumeka shi babba neh”
Zama Masroor yayi akan Kujera suka fashe da Dariya duka, Hararanta yayi
“Lallai baki isah bah, Ai daddy nane”
Idonta ne ya ciko da K’walla ta kara hade rai tace
“Daddy na dai”
K’ara Fashewa da dariya sukai duka. Ganin Sunata mata dariya yasa ta fashe da kuka ta mik’e Tabar wajan tana kuka..

Hararan Masroor Daddy yayi
“Kaga kah koranmin Baby koh, Tho Maza ka tashi ka Lallasheta ta dawo taci abinci”
Turo baki Masroor Yayi yana Kai Loman Abinci
“Daddy kah kyaleta cikin wah Bah nata bah, Karta Cin”
Lekowa Mahnoor tai Tana Share kwalla
“Baza’a kyaleni din bah.”
Guntse Dariya Mami da Daddy sukai dan Yanzu sunayi zasu takalo Rigima..

Rungume Mami tai ta Baya ta shagwabe Fuska
“Mami yanzu bro Masroor baya sona, Bro Yasir ne kawai ke Sona”
Cup din Juice Masroor ya dauka ya kora Sannan ya aje Yana cewa
“Kedai kika sani”
“Ahan ina Kaje dazo baka fadama Yasir bah, yazo nemanka neh kuma nasan din inda zaka tare kuke zuwa”
D’an jim yayi sannan yace
“Eh wannan fitan ni kadai neh, Banda Shi”
Murmushi Daddy yayi cikeda Nishadi
“Koh anje Wajan Sirikan nawa neh”
Suman Kanshi Ya Shafa Yana Y’ar Dariya.
“Aa Daddy”

Mami Itama Dariyan tai
“Ai dama bazaka fada bah, tho bari kaji gwara fa kama fada tun yanzu coz ana gama Hayaniyar siyasan nan Zamuje neman aure”
Turo Baki Masroor Yayi ya mik’e yabar Dinning din…

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 96 to 100*

“Ina sanki Sulthana, zan iyayin komai a kanki. Insha Allahu zaki fita daga k’angin fa kike ciki kwanan nan”
Motanshi ya shiga yabar wajan cikeda tausayin halinda Sulthana take ciki.

Da zazzabi Sulthana ta tashi da asubah, dakyar ta iya mik’ewa ta fito tsakar gidan. Alwala tai ta koma zaure tai Sallah, Tana zaune Baffa ya fito ya tafi masallaci. Kasa shiga tai aikin data saba tayi a cikin gidan har wuraren k’arfe bakwai da rabi, Ameenatu ce ta fara fitowa daga daki ganin ko’ina batsa batsa yasa ta nufi zaure a fusace. Kwance ta sameta tanata rawar sanyi, tsaki Ameenatu tai tana magana cikin daga murya
“Wato dan kin raina mutane yau bazaki je kiyi aikinki bah. Uban wa kikeso ya miki shara da wanke wanke”
d’an dagowa Sulthana tai hawaye na gangarowa a idonta
“Dan Allah yaya Ameenatu kiyi hakuri banida lapia neh”
Duka takai mata dai dai nan Hafsatu ta k’araso wajan tana Murmushin Mugunta
“A’a yaya Ameenatu yau kuma Y’ar son ake duka”

Tsaki Ameenatu ta k’arayi tana nuna Sulthana da yatsa
“Wallahi idan baki tashi kinyi aikin daya kamata bah sai na miki dukan tsiya”
Kallanta hafsatu tai da mamaki, Yau kuma Ameenatu kecewa zata duki Sulthana, Lallai abin babba neh.
Kasa tashi Sulthana tai sai kuka datake Mara sauti, dakyar ta mik’e ta zauna tana k’allan Ameenatu data hada girar sama data k’asa
“Dan Allah yaya Ameenatu kiyi Hakuri”
Ai kamar zugata take nan da nan ta rufeta da duka, Hafsatu taga bati itama ta tayata. Bah abinda Sulthana take in banda ihu. Ihunta ya fito da Mama ta K’araso wajan dasauri..

Dakyar ta kwace Sulthana a hannunsu a fusace tace
“Wannan wanne irin iskanci meh Ameenatu, wai meke daunki me? Metai muku kuke dukanta haka kamar Allah ya aiko ku”
Ameenatu ta hade rai tana huci
“Dan wulakanci tun dazu yarinyan nan batai aikin gida bah, jibi gidan nan sannan ina mata magana tana cemin wani batada lapia”
K’allan Ameenatu Mama ta tsaya yi
“Lallai Ameenatu baiwarki ce ita da zakice dole sai tamiki aiki, ai rashin lapia ya wuce komai sai kuyi mata uzuri”
Hafsatu ta chuno baki
“Haba Mama ke kullum sai ki rinka hana ana hukunta yarinyan nan, Gaskiya..
Saukan Mari Hafsatu taji a fuskanta, a fusace Mama tace
“Wallahi ki kiyayeni Hafsatu, na lura abubuwanki nema suke su wuce wuri”
Nunasu da dan Yatsa tayi tana cewa
“Tho bari kuje, daga yau Sulthana bazata k’ara aikin gidan nan bah ku zakuyi. Meye ku anfanin ku”
Baffa ne ya bankado kyauren gidan ya shigo jin hayaniya, cirko cirko ya samesu a tsaye sai Sulthana dake Zaune a kasa tana kuka duk jini a hancinta da baki..

“Lapia??” Baffa ya tambayi Mama, Hafsatu ce ta koromai bayanin duk abinda ya faru. Nan ko Baffa yahau sababi ta inda yake shiga batanan yake fita bah, Ameenatu ta kalla yana cewa
“Ku cigaba da dukanta ai wannan ma iskanci neh”
Hafsatu ce ta cigaba da dukanta Mama na tsaye tana k’allan Baffa cikeda takaici, batace komai bah ta koma dakinta ranta bace. Itama Ameenatu daki ta koma a fusace, ligi ligi Hafsatu taima Sulthana Baffa na Tsaye. Saida ta duketa san rai Sannan ta kyalleta, Sannan Baffa yasata tai duk aikin Gidan yana Tsaye. Tanayi tana kuka dakyar tai aikin ta gama ta koma zaure ta zauna ta cigaba da kukanta..

Nan da nan wani sabon Zazzabin ya rufeta. Ana Sallan Azahar Baffa ya kwalla mata kira, ta nufi Cikin gidan dasauri, gyada ya mik’a mata. Ta amsa dasauri ta hau wankewa, tana gamawa ta daura a wuta ta zauna bakin murhun ko sanyin datake ji zai ragu. Bata gama bah sai bayan La’asar sannan tadau Gyadan ta nufi bakin kasuwa. Inda ta saba zama ta aje gyadan, zama tai ta hada kanta da guiwa ta fashe da wani sabon kukan, murya taji a kusada ita mai sanyi yana cewa
“Meke damunki Sulthana whats wrong”
Dago runanun idanunta tai duk a tunaninta likitan nan neh, Ganin Masroor yasa ta maida fuskanta ta cigaba da kuka. Runtse ido Masroor yayi ya dunkule Hannayenshi, jin kukanta yake har cikin Ranshi nan da nan shima idanunshi suka chanza launi..

“Sulthana, meke damunki? Tel me pls”
Dago kai tai tana turo baki, ganin yanda take karkarwa yasa ya mik’e dasauri
“Sulthana are you sick?”
Dauke kai tai tana cigaba da turo baki, dakyar ta iya mai magana shima tanayi hakoranta na karo da juna
“Nidai ka daina zuwa inda make, idan Yaya hafsatu taganni zata fadama Baffa kuma dukana zaiyi”
Tsugunawa yayi gabanta cikeda damuwa
“Sulthana fadamin meke damunki, nasan kina cikin damuwa. Me hafsat take miki itada Baffa”
Mik’ewa tai dasauri tana k’akabe Riganta, trayn gyadan ta sunkuya zata dauka yayi saurin rik’ewa
“Please Sulthana ki tsaya ki saurareni, Am here to help uh. Taimakonki zanyi, ki fadamin ko menene nikuma na miki alkawarin zan kawo karshen koma menene”
Tsayawa tai ta tana K’allanshi da Alamar mamaki…

Tho fah ga *Doctor Fareed* Ga *Masroor*
   Shin Fans wah kuka zabarma Sulthana ya taimaka mata?? Nidai nace......

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 101 to 105*

Tsaya tai tana K’allanshi da Alamar mamaki. kai ya gyada mata
“I mean what I said”
Sai a Sannan ya K’alleta da kyau, a rudeyace
“Sulthana maiya sameki a fuska? Wayaji miki ciwo?”
Shafa wajan tai, batace komai bah
Trayn Gyadanta ta fuzge ta daura akai ta soma tafiya. Binta yayi yana mata magana anma ko sauraranshi batai bah tayi tafiyarta. Ranar Sulthana batai ciniki nah hakanan ta koma gida, Duka kuwa saida tasha shi Wajan Baffa. Haka tai kukanta ta gaji ta kwanta, yauma k’amar jiya Yaro ya shigo yace Ana Sallama da ita, turo baki tai tacema yaron yace bazata zo bah haka koh akai, Yaron ya koma yagayama Fareeed Sakon da Sulthana ta bashi..

Baice komai bah ya bude mota ya dauko wani k’aton leda, yaron ya mik’ama wah
“Dan Allah gashi ka kai mata kaji”
Hannu Yasa a Aljihu ya ciro dubu daya ya mik’a ma Yaran
“kai kuma ga naka”
Washe baki Almajirin yayi tareda godiya, ledan ya shiga dashi cikin zauren ya bah Sulthana, zaro ido tai tana k’allan almajirin
“Dan Allah ka maidan mai kada Baffa ya gani kace nace banaso”
Niki niki yaron yadau leda ya koma dashi, yana fita yaga wayam bah motan Dr Fareed. Dawowa yayi ya shaida mata ya aje ledan ya fita, jikinta neh ya soma rawa yanzu idan Baffa yaga ledan nan tasan duka zataci. Sadiya ce ta fado mata a rai ta dau ledan dakyar ta nufi gidansu sadiya cikeda Fargaba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button