SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sallama ta shiga Allah ya taimaketa Baban Sadiya baya nan, saida ta gaida Maman Sadiya sannan ta zaiyana mata duk abinda ke Faruwa, ga mamakinta sai gani tai Maman Sadiya ta washe Baki.
“A’a Sulthana wannan ai abin farinciki neh”
Hannu ta daga ta godema Allah sannan ta k’alli Sulthanan data sake baki tana k’allan Mama
“Ina tayaki murna Sultana, insha Allahu komai ya kusa zuwa karshe. Ni nasan wannan likitan sanki yake”
Gwalalo ido Sultana tai idanunta suk’a ciko da kwalla, Mama ta cigaba da cewa
“Kinga idan kikai aure komai zai zamo tarihi, zaki fita daga cikin wannan wahalan da kike ciki”
Rufe fuska Sulthana tai tana murmushi. Rungumeta Sadiya tai tana cewa
“Iyeh! Amarya”
Dukan wasa Sulthana takai ma Sadiya, kyalkyalewa da dariya Sadiya tai cikeda farinciki.

Mik’ama Mama ledan tai tareda mik’ewa
“Mama idan Baffa yaga wannan kayan dukana zeyi”
Amsan kayan Mama tayi ta hau dubawa, Hadaddun kayane kala kala. Dogayen riguna, Atamfofi da lesuka ready maid. Sai takalma da turaruka. Sakin baki sadiya tai
“Tab ni ban taba ganin irin wannan kayan bah”
Tabe baki Sulthana tai
“Mama kiyi anfani dasu keda Sadiya”
Dago kai Mama tai tana k’allanta, girgiza mata kai tai
“A’a bazamuyi anfani dashi bah Sulthana, na miki alkawarin zan aje miki su har lokacin da kika bukata”
Girgiza kai Sulthana tai tana cewa
“A’a kiyi anfani dasu”
Tsofafin Silifas dinta wari daban daban tasa tace
“Mama na tafi kada Baffa ya fito bai ganni bah”
Sallama Mama tai mata Suka fito tareda Sadiya, kara kyalkyalewa da dariya Sadiya tai
“Amarya knan”
Duka Sulthana ta d’aka mata tana hararanta
“Banaso fah”
Murmushi Sadiya ta rik’e haba tace
“Niko inasan naga wannan saurayin d’an birni”
Turo baki Sulthana tayi tana yatsine Fuska
“Nidai bana sansa”
Sakin baki Sadiya tai batace komai bah, a haka sukai sallama Sulthana ta nufo gida dasauri…

A kofar gidansu taga Ahmad saurayin Hafsatu, K’allanshi tayi da nufin gaidashi ganin ya balla mata harara yasa sum sum ta shiga Gida, kan buhunta ta zauna tai shiru. Haskota akai da torchlight ta mik’e dasauri muryan Hafsatu taji tana cewa
“Gatanan ta dawo”
Gabanta ne ya fadi Dam! Shiknan yau tasan nata ya K’are..

Baffa ne ya kwalla mata kira ta amsa ta shiga cikin gidan jikinta na rawa, Cirko cirko ta samesu a tsakar gidan, Ameenatu sai Balla mata harara take. Tsugunawa tai Sannan tace gani.
Baffa rai bace yace
“Waye Saurayin nan da hafsatu taganku dashi Ranan”
Gaban Sulthana ne ya fadi
Daka mata tsawa Baffa yayi
“Badake nake magana bah”
Muryanta na rawa tace
“Baffa wallahi ban sanshi bah, ranan kudin gyada na zai bani”
Mari Baffa ya dauketa dashi yana huci
“Bazaki fadamin Gaskiya bah”
Kuka Sulthana ta fashe dashi ta soma Rantse rantse
“Wallahi Baffa bansanshi bah”
Ameenatu ce ta amshe da cewa
“Karya kikeyi, wato Sulthana kin Fara kula kulan maza koh? Ai dama tunda naga wannan likitan nasan dan iska neh”
Sai a sannan Sulthana ta gane inda maganansu ta dosa
Daki Baffa ya shiga ya dauko Bulala, Sulthana na ganin haka ta kwala ihu tana kuka sosai

“Dan Allah Baffa kai hakuri Wallahi bansanshi bah”
Hafsatu tace
“Rannan Ahmad yake gayamin ya ganshi, kyaleta nai kawai ban fadaba sai yau kuma ni da idona naganshi Yazo yaba wani yaro katon leda ya kawo mata, shiyasa dana tambayi Mama sulthana ta kawo mata leda tace wani leda”
Tsula mata bulala Baffa yayi ta saki ihu ta fashe da kuka. Tana kururuwa
“Dan Allah Baffa kai hakuri bazan Sake bah”
K’asa magana Mama tai ta koma daki abinda cikeda bakin ciki
Saida Baffa yaga bata numfashi Sannan ya kyalleta Sukai shigewansu daki suka barta nan warwas a tsakar gidan…

Mamace ta fito jin sun shige daki, kuka ta fashe dashi mara sauti ganin Sulthana kwance. Daki ta koma ta debo ruwa ta yayafa mata, ajiyan zuciya tai ta K’ara fashewa da kuka tana ihu
“Baffa kai hakuri, Wayyo baffa zai kasheni. Yaya Ameenatu ki taimakeni”
Saurin rufe mata baki Mama tai itama tana kukan, Dakinta ta kaita ta dawo ta hada wuta ta daura mata ruwan wanka, ruwan na zafi ta surka ta kai mata ban daki. Da taimakon Mama tai wanka, nan da nan Zazzabi ya rufeta, magani Mama ta bata tasha Barci mai nauyi ya dauketa. Sai gaf da Asubah Mama ta tasheta ta koma zaure gudun kar Baffa yazo fita massalaci bai ganta bah…

A Bangaren Masroor kuwa koda ya koma gida kasa sukuni yayi, Falon k’asa ya zauna yayi shiru, Mami ce ta sauke zuwa falon ganin Masroor zaune ya k’urama tv ido anma daga gani hankalinshi ba’a tv take bah. Zama tai kusa dashi tadan Tabashi, Razana yayi ya juya ganin Mami yasa ya saki ajiyan zuciya.
“Lapia Meke damunka son” cewar Mami
D’an Murmushi yayi yana girgiza kai
“Nothing Mom”
Kauda kai Mami tai gefe fuskanta bah Walwala
“Masroor bakada kamana, ni yakamata ka fadama damuwanka.”
Sumar kanshi daketa kyalli ya shafa yana y’ar Murmushi
“Mami bah komai karki damu”
Bell aka danna, Cikin Maid din gidan ta shigo dasauri ta bude kofan, Mahnoor ce ta shigo dagudu ta wurgama Maid din jakan Makarantan tah tana Murmushi
“Mamina I’m back”
Ganin Mami yasa ta nufeta dagudu ta rungumeta tana dariya
“I Missed you Mami”
Masroor ta k’alla taga sai hararanta yake..

chuno baki tayi
“Mami wai meyasa ya Masroor sai ya rinka eyeing dina”
Sumar kanshi ya shafa
“Mami K’arya take”
Hararanshi Mami tayi
“Banasan Haka fah, ka daina hararan min Y’a”
Baice komai bah yabar Falon..

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 106 to 110*

     *Masoya Littafin Sulthana naga sakonin ku da dama wasu ban samu na karanta bah. Abinda nikeso ku gane a nan shine* _labarin Sulthana ya faru ne dagaske_ *So duk abinda kuka gani a ciki bah k'irkira nai bah abu ne daya faru dagske. Sannan Fans din Masroor da na Dr Fareed kowacce tasa ido taga Yadda labarin zai k'arke, yanda yazo a labari hakan zan baku a rubuce insha Allah. Ina fatan zaku fahimceni*..

     Wannan Shafin Naku neh *Sulthana Fans* Allah yabar k'auna

Hararanshi Mami tayi
“Banasan haka fah, ka daina hararan min y’a”
Baice komai bah yabar falon. Bell aka k’ara dannawa Maid ta fito dasauri ta bude kofan, Yasir neh ya shigo da sallama ya karasa inda Mami ke zaune ya tsuguna har K’asa ya daidata. Da fara’a a fuskanta ta amsa tareda tambayanshi mutan gidan, ya amsa mata da lapia lau. Mutum nashi ya tambaya Mahnoor ta fadamai yana daki, mik’ewa yayi ya hau sama ya nufi side din Masroor..

Kwance ya sameshi kan Three seater cikin hadadden Falon shi yana k’allan celien, Zama yayi k’an 1seater kusa dashi tareda dafashi
“Friend its anything wrong”
K’akaro murmushi Masroor yayi yana k’allanshi
“No I’m fine”
Ajiyan zuciya Yasir ya sauke harya bude baki zaiyi magana aka danna bell din Falon, mik’ewa yayi ya bude kofan, cikin ma’aikatan gidan neh dauk’e da tray cikeda kayan ciye ciye, kan center table din falon ta aje ta fita tareda jawo kofan. Komawa Yasir yayi ya zuna yana facing Masroor da yanayinshi ya chanza..

“Friend tel me something, meke damunka coz bah haka kake bah”
Mik’ewa zaune Masroor yayi yana k’allan Yasir. Bai boyema Yasir komai game dashi kamar yanda shima Yasir din bai boyemai komai. Sumar kanshi ya shafa ya fara magana cikin sanyayar muryanshi
“Kah tuna yarinyan nan da naso bigewa ranan da mukaje kauyen nan”
Kai Yasir ya daga alamar eh, cigaba da magana Masroor yay
“I donno why I always think of her, kullum cikin tunaninta nake. Ina tausaya mata coz alamu sun nuna she need help”
Murmushi Yasir yayi mai sauti har saida Masroor ya kalleshi da mamaki
“Just tel me san yarinyan nan kake”
Saurin girgiza kai Masroor yayi yana cewa
“No friend bah santa nake bah, kawai tausayinta nake. Yarinyan taki tsayawa muyi magana just becoz of dat useless sistern nata”
Jinjina kai Yasir yay
“Nima na lura da haka anma tunda bataso y not kawai ka kyaleta”
Shiru Masroor yayi baice komai bah..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button