SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ganin yanda Masroor din ya damu yasa Yasir ya dafashi
“Look friend uh are in love kawai kaidai bakaso ka fadane”
Mik’ewa tsaye Masroor yayi dasauri yana girgiza kai
“No Yasir kawai tausayi neh. Kamasan wani abu?”
Kai Yasir ya gigiza,
“Kasan guy din nan da yake tareda sistern tah a nan gidan yake aiki”
Yasir ya mik’e dasauri
“Kai haba”
Gyada kai Masroor yayi sannan yace
“I’m serious”
Shiru sukai nasamu mintina chan Yasir ya dago ya k’alli abokin nashi
“Ga shawara”
Dasauri Masroor ya zauna yana cewa
“Am all ears”

“Why not mu samu guy din mu biyashi ya fada mana labarin yarinyan, Coz am sure yasan komai tunda yana tareda sistern tah. Daga nan kaga sai mu nemi solution”
Shiru Masroor yayi yana cigaba da shafa sumar kanshi tareda furzar da iska
“No Friend bana tunanin haka zai yuwu, besides banasan yasan wani abu gameda wannan”
“Buh we dn’t have any choice” cewar Yasir
Dago kai Masroor yayi da murmushi dauke a fuskanshi
“Yes! Nasan meh zanyi”
K’allanshi Yasir ya tsaya yi
“Meh knan”
Tasowa Masroor yayi ya dawo kusada Yasir ya zauna
“Zan Hadata da Parrot neh”
Dariya Yasir ya fashe dashi
“Do uh think it wil work”
Gyada kai Masroor yayi yana murmushin jin dadi…

Dukda irin dukan da Sulthana tasha a haka Baffa ya bata gyada ta dafa, da taimakon Mama ta dafa ta juye. Mama da kanta ta daura mata akai tai mata Fatan Alheri ta fito.. Yanke Shawaran ta tafi bakin kasuwa tai, tafiya take ahankali jikinta duk Ciwo yake mata, dakyar ta k’arasa bakin kasuwa ta samu guri inda tasaba zama ta zauna. Tagumi tai ta lula cikin tunanin Mahaifiyarta nan da nan hawaye ya soma gangaro mata, Muryan yarinya taji a kanta ta dago dasauri. Murmushi ta mata tareda
Mik’a mata Dari biyar
“Gashi ki bani gyada”
K’allam yarinyan Sulthana ta tsaya yi, kyakyawa da ita Sanye take cikin bakin dogon Riga mai kyau. Yarinyan bah K’aramin burge Sulthana tai bah, k’asa dauke idonta tai daga k’allan Yarinyan. Har saida Tace
“Bakya jina neh”
Zabura Sulthana tai ta maida dubanta ga kudin tana cewa
“Na nawa zaki siya? Banida chanji”

Saurin Girgiza kai tayi tana cewa
“Ai na duka zaki bani”
Jiki na rawa Sulthana ta soma nema ledan dan dama gyadan bazai wuce na haka nah”
Juyawa Mahnoor tai ta k’alli Masroor dake cikin mota nesa dasu, kai ya gyada mata. Ta juyo ta tsugunna tana taya Sulthana zuba gyadan a Leda
“Menene Sunanki” cewar Mahnoor
Dagowa Sulthana tai tana k’allan Mahnoor da manyan idanunta, Yarinyan ta burgeta sosai. Dan murmushi tai tace
“Sunana Sulthana”
Dariya Mahnoor tayi tareda maimaita sunan
“Woaw nice name, ni kuma sunana Mahnoor”
Kurri Sulthana ta mata itama ta maimaita sunan. Dai dai nan ta juye gyadan a Leda ta mik’ama Mahnoor.
Mik’a mata kudin tai tasa hannu biyu ta k’arba. Mahnoor tace
“Inaso ki zama k’awata”

Dan Dariya Sulthana tai dimple dinta suka lotsa
“Nima haka” cewar Sulthana
Mik’ewa tai tana cewa Shiknan zan tafi gida tunda na siyar. Mahnoor ta turo baki
“Bafa mu gama hira bah zaki tafi”
D’an zaro ido tai
“Kinga yau na saida gyadata dasauri barin tafi gida nasan Baffa idan yaga na dawo da wuri bazai dakeni bah”
D’an Shiru Mahnoor tai sanna tace
“Tho gobe zaki zo?”
Kai Sulthana ta gyada
“Ehmana, Anma inane gidanku”
Shiru Mahnoor tai ta rasa abin cewa har saida Sulthana tace
“A Birni kike ko”
Gyada kai Kawai Mahnoor tai tana y’ar murmushi. Sallama suk’ai Sulthana ta nufi gida dasauri itama Mahnoor ta shiga mota tareda fadama Masroor duk y’anda sukai. Murmushin jindadi yayi
“Dats my Lil Sis am proud of uh”
Itama Murmushin tai suka bar Cikin Kauyen.
Yinin ranar Sulthana tayishi neh cikeda tunanin k’awarta y’ar birni. Tayi murna sosai da haduwa da Mahnoor. K’ullum sai Masroor ya kawo Mahnoor wajan Sulthana idan ta taso School, shaquwa sosai ya shiga tsakaninsu duk da Har yanzu bah abinda Sulthana ta fadama Mahnoor dangane da halinda take Ciki…

Anya kuwa Wannan Shawaran na Masroor mai bullewa ce
Mudaije zuwa..

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

     *Page 111 to 115*

Shaquwa sosai ya shiga tsakaninsu duk da har yanzu bah abinda Sulthana a fadama Mahnoor dangane da halinda take ciki…
Yauma kamar kullum tana dawowa daga makaranta taci lunch tai Sallah, side din Masroor ta nufa knocking tai a bakin kofan falonshi taji shiru, ta dad’e tana knocking jin shirun yayi yawa ta juyo ta koma side dinsu. Tana k’okarin Saukowa k’asa taci karo da Mami ta fito dak’i, tsaya tai tana k’allanta da Mamaki
“Wai Mahnoor na tambayeki”
Gyada kai kawai Mahnoor tai, Mami ta cigaba da cewa
“Kullum da kuke fita din nan keda Masroor ina kuke zuwa?”
Turo baki tai dan Masroor ya jamata kunne K’ar ta sake ta fadama kowa. Mami tace
“Badake nake magana bah”
Harta bude baki zatai magana sukajiyo Muryan Masroor ta bayansu yana cewa
“No mami bafa wani guri muke zuwa bah, just ina wanke lefuka na neh danai kinsan fushi take dani wai tunda na dawo bama zuwa yawo”

Gizgiza kai kawai Mami tai dan Tasan k’arya ya fada
Mahnoor ta K’alla tana cewa
“Zo ki daukomin wannan abin” ta juya ta shiga dakinta, matsowa Masroor yayi ya sassauta murya yace
“No matter now karki fada mata”
Gyada kai Mahnoor tayi ta shiga dakin Mami da sallama shikuma ya dauko k’asa..

Zaune ta samu Mami bakin Katafaren Gadonta, kusada ita mami ta nuna mata
“Zo ki zauna nan”
Bah musu taje ta zauna, Mami ta fara magana cikin sigan Lallashi
“Mahnoor ina kuke zuwa”
Chuno baki tai
“Nifah Mami bafa wani guri muke zuwa bah yawo kawai yake kaini”
Jinjina kai Mami tai
“Mahnoor bakya min k’arya meyasa yanzu kika fara, tunda bazaki fadaba Shiknan”
Ajiyan zuciya tai sannan ta cigaba
“Uh should be very careful kina jina?”
Kai ta gyada ma Mami ta mik’e tana Kakkabe skirt dinta
“Mami bye sai mun dawo”
D’an murmushin yak’e Mamin tai
“Ai bari Daddynku ya dawo zance ne Islamic Lesson teachern ki ya daina zuwa bayan isha’i ya koma zuwa bayan Asr. Sai muga yanda za’ai a rinka fitan”..

Bubbuga k’afa Ta fara ta fita daga dakin tana gungunai, a cikin Hadad’iyar doddge dinshi ta hangoshi zaune, k’arasawa tai ta shiga ya tada suka bar gidan..

Yau Masroor yaci Alwashin koma mai zai faru saidai a faru anma dole sai Sulthana ta sanar dashi halin datake ciki. suna cikin tafiya a mota Mahnoor tace
“Bro Masroor ka tsaya nasai ma friend chocolate da ice cream”
D’an murmushi yayi
“Kinada kudi neh”
Turo baki tai
“Tho bah kai kanada shi bah”
Baice komai bah ya juya k’an motan, tare suka shiga ta zabar ma Sulthana k’ayan ciye ciye k’ala kala suka fito suka nufi kauyen..

Yau abin mamaki bah Sulthana bah alamar tah, dasauri Mahnoor ta k’alli Masroor idonta cikeda k’walla
“Bro Friend bata nan”
Shiru Masroor yayi yana k’allan wajan cikeda damuwa. Kamar ance ya dago ya hangota tafe da trayn gyada akai tana matsar kwalla, dasauri ya bude motan ya fita Mahnoor tabi bayanshi..

Zama Sulthanan tai inda ta saba zama tana cigaba da matsar k’walla, mahnoor ce ta k’araso wajan ta zauna tana cewa
“Friend meyasa kike kuka”
Jin muryan k’awarta y’ar birni yasa ta dago dasauri tasa hannu tana share kwallan daya gangaro mata. Murmushi tama Mahnoor
“Bah komai k’awa”
D’an turo baki Mahnoor tai
“Nifah Friend dinki neh, kifadamin waye yake dukanki”
Murmushi Sulthana ta k’arayi
“K’awa bah kowa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button