SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Muryan Masroor sukaji a bayansu yana cewa
“Lokaci yayi daya kamata ki fada mana abinda ke damunki, ki daina boyewa dan cutar dake zeyi”
Daga k’ai tai suka hada ido ta mik’e dasauri tana k’allanshi tareda nunashi da yatsa
“Kah daina zuwa inda nake, idan Baffa ko yaya Hafsatu taganmu dukana xasuyi”
Baiji wani d’ar bah ya kama hannunta tana turjewa mutane sai k’allansu suke bayan mota ya sakata ya rufe, Mahnoor ta dauko trayn gyadanta ta saka a booth, sannan ta shiga Masroor ya bar Kauyen a guje..

Ihu kawai Sulthana take
“Sun Saceni, Jama’a ku taimakeni”
Bah wanda yayi yunk’urin taimakonta saima bin motar da ake da K’allo
Gudu yake sosai k’amar zai tashi sama, bai tsaya ko ina bah sai Gidansu Yasir, horn yayi mai gadi ya bude ya shiga yayi parking. Itako Sulthana tunda aka bar Kauyensu tai shiru ta fara rarraba idanu dan tunda take bata taba barin kauyensu bah sai yau, bin titi take da k’allo tana shafa Glass din motan tana murmushi..

Wayanshi ya dauka ya soma neman Layin yasir, yana cikin kira ya fito daga side dinshi yana murmushi.
“Yau suprise akai min”
Karasowa yayi bakin motan, Ganin Sulthana a baya tanata Zare ido yasa yayi turus yana k’allan Masroor daya hade girar sama data k’asa. Sulthana ta dafa Mahnoor cikeda damuwa
“K’awa ina kuka kawoni? Dan Allah karku ciremin kaina ban muku komai bah”
Kyalkyalewa da dariya Mahnoor tai tana cewa
“Mu ai bama cire kai”
Bude Murfin motan Masroor yayi ya fita tareda jan Hannun Yasir, side dinshi suka nufa a falo suka zauna, Yasir ya kada baki yace

“Masroor what do uh think uh are doing?, ka dauko yarinya hakanan kawai. Ko kasanar da Iyayenta neh”
Mikewa Tsaye Masroor yayi cikin daga murya yace
“I Cn’t hold it any more Yasir, inaso na taimaka ma yarinyan nan. I donno why I always think of her, kullum sai tazomin a mafarki”
D’an Murmushi Yasir yayi ya mik’e ya dafashi
“Look at me Friend”
Dagowa Masroor yayi ya kalli Yasir, Murmushi yasir yamai
“Uh are in love Masroor, santa kakeyi. Beleive me”
Girgiza kai Masroor yayi idanunshi sun k’ada sunyi ja. Suman kanshi yaja tareda furzar da iska
“No Friend, forget abt dis lets find solution”
Kamashi Yasir yayi ya zaunar dashi yana cewa
“Abinda kayi bah daidai baneh Friend, bai kamata ka daukota bah. A hankali zakabi komai har kasamu abinda kakeso.”

Masroor baice komai bah saima mik’ewa dayayi yabar falon, mota ya koma yaga Mahnoor a baya kusada Sulthana daketa kuka kamar ranta zai fita. Bude kofan yayi ya janyo hannunta. Ihu ta saki tana turjewa, daka mata tsawa yayi tai gum da bakinta, bai saketa bah saida ya shiga Falon Yasir Mahnoor na biye dasu…

Yasir na ganinsu ya mik’e tsaye
“Masroor whats all dis? Pls ka maida yarinyan mutane. Kada Mum ta dawo ta samemu a nan pls”
Baice komai bah ya zaunar da Sulthana k’an kujera shima ya zauna ana kusa da ita. Murya a sanyaye yace
“Sulthana!”
Dago jajayen idanunta tai jikinta na rawa tace
“Na’am”
Suman kanshi ya shafa Yace
“Ki fadamin meke faruwa dake karki boyemin komai”
Shiru tai nadan mintina, ganin dagaske masroor yake yasa yasir yaja hannun Mahnoor suka bar falon..

Saukowa Masroor yayi daga kan kujeran dayake ya tsugunna a gabanta, hannunshi yasa ya dago fuskanta
“Kiyi min magana Sulthana karki boyemin komai”
Sheshekan kuka ta fara ts fashe da kuka a hankali..

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

     *Page 116 to 120*

“Kiyi min magana Sulthana karki boyemin komai”
Sheshekan kuka ta fara ta fashe da kuka a hankali. Ganin yanda idonshi yayi ja ya hade rai yasa ta fara magana a hankali, labarinta tun sanda tai wayo har izuwa yanzu taba Masroor bah abinda ta boye mai. Saida ta gama sannan ta dago suka hada ido, hawaye ne tagani nabin kuncinshi..

Motsin dah Masroor yaji a bakin kofa neh yasa yasa hankie ya goge hawayen fuskanshi Sannan ya dago, Yasir ya gani idanunshi sunyi ja dah ala yaji duk labarin dah Sulthana taba Masroor, Cikin falon ya shigo ya zauna yana k’allan Masroor
“Akwai wani abu a k’asa, bt uh knw what?”
Kai Masroor ya girgiza Fuskanshi bah walwala
“Take her home”
Bah musu Masroor ya mik’e
“Tashi na maidake gida”
Juyawa yayi ya nufi hanyar fita,
Mik’ewa tai jiki a sabule tabi bayanshi, a mota suka tarar da Mahnoor tana game da wayan Masroor, dah kanshi ya bude mata kofan motan ta shiga shima ya zagaya ya shiga suk’a bar gidan..

A garinsu Sulthana fah, labari meh ya k’arada garin nah an sace Sulthana, Baffa dake kofar gida wajan almajiransa wani makocinshi ya k’araso tareda bashi hannu sukai musabaha, Mak’ocin nashin mai suna Mallan Bala yace
“Wani mummunan labari nake tafe maka dashi”
Baffa yadan zaro ido
“Tho Mallan Bala meya faru”
D’an dukar dakai Yayi sannan yace
“Dazu muna bakin kasuwa wata mota hadaddiya mai kyau, ta shigo wani saurayi neh ke tuka motar. Yana zuwa yaja y’ar wajanka Sulthana ya tura cikin motan ya tafi a guje”
Ga mamakin Mallan Bala sai ji yayi Baffa yace
“Ah! Ai na dauka Y’ayana Ameenatu da Hafsatu kake magana, yoh indai Sulthana ce bai wuce samarinta ne da suk’e fasik’anci tare”
Da Alamar Mamaki Mallan Bala ya k’alli Baffa har ya kasa boye Mamakinshi Yace
“Haba Mallan Jamilu, bai kamata wannan furucin ya fito daga bakinka bah. Na dade inajin labarin abubuwan dake..”
Saurin katseshi Baffa yayi inda yake shiga bata nan yake fita bah, ganin abin na k’ara gaba yasa Mallan Bala barin wajan sum sum…

Haka labari ya dinga zuwa kunnen Mallam jamilu anma ko a jikinshi, su Mama suma sunji barin, anma Hafsatu da Ameenatu bah wanda ya nuna alhininsa saima cigaba da safgoginsu da sukai, Mama ce kawai ta nuna damuwanta harda y’ar kwallanta. Su Maman Sadiya da sadiya duk sun shigo gidan jaje, Sadiya sai kuka take dakyar su Mama suka lallasheta ta koma gida…

Driving Masroor yake hankalinshi a tashe, gidansu ya nufa yayi horn masu gadi suk’a bude mai gate, Parking yayi nesa da inda ake parking motocin gidan, Mahnoor ya k’alla yana cewa
“Ki tafi ciki, idan Mami tah tambayeki ni just tl her bakisan inda zani bah”
Kai kawai ta gyada ta bude kofan ta fita tana d’agama Sulthana hannu wacce sam batama luraba sai Haraban gidan datakebi da kallo cikeda sha’awa..

Reverse yayi ya fita daga gidan yadau hanyan k’auyensu Sulthana, fashewa da kuka tai tana turo baki
“Dan Allah karka maidani wallahi Baffa dukana zeyi gashi ban saida gyadan bah”
Baice mata komai bah sai ma idonshi daya runtse da k’arfi ya bude, Wasu tarin Almajirai yagani a bakin titi, yayi parking yadauko trayn gyadan ya raba musu Sannan ya dawo ya cigaba da driving..

Kuka kawai Sulthana take tanabin hanya da k’allo har suka fara shiga cikin k’auyensu lokacin an fara kiraye kirayen sallan magriba, bakin kasuwan yayi parking Sannan ya juyo ya k’alleta
“Its ok Sulthana, ki daina kuka kinji”
Kai ta gyada mai tana share hawayen daya gangaro mata da bayan hannu. Ajiyan zuciya ya saki yana bin K’asuwan da kallo
“Kinga anata kiran Sallah, yimin kwatancen gidanku na kaiki coz dare ya farayi”
Girgiza kai tai dasauri tana zaro ido,
“Aa nidai kawai ka budeni na tafi idan Baffa ya ganka ni duka”
Fitowa yayi ya bude mata itama ta fito tadau traynta, Hannu yasa a aljihu ya ciro bandir din y’an hamsin guda hudu ya mik’a mata..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button