SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaro ido tai tana k’allan kudin
“Aa bazan amsa bah nidai kaban kudina kawai”
D’an murmushi yayi yana k’allan dimples dinta dake k’ara mata kyau
“Tho nawane kudin naki?”
Turo baki tai cikeda shagwaba tace
“Bah dari bakwai baneh”
Baice komai bah ya k’irga dari bakwai ya mik’a mata, ta amsa ta irga sannan tadago tana murmushi tace
“Nagode”
Kwaikwayan yanda tace nagoden yayi, ta d’anyi murmushi ta juya zata tafi, Hannunta yayi saurin rik’ewa ta juyo tana k’allanshi da Alamar mamaki
“Bah ko sallama sai ki wani wuce”
Batace komai bah sai turo baki datai tana k’okarin fizge hannunta, sakin Hannun yayi yana mata murmushi.
“Tho shiknan sai da safe koh, gobe ina nan ina jiranki kinji”
Batace komai bah ta juya ta fara tafiya tanayi tana waigenshi, hannu ya daga Mata tad’an saki murmushi itama ta d’aga masa hannu, bai bar wajanbah saida ya daina ganinta. Phone dinshi neh ya hau ringing, motan ya shiga ya zauna sannan yadau wayan yana cewa
“I will be on my way, na maidata ai”
Shiru yad’anyi sannan yace
“Saidai nazo kawai” ya kashe kiran. Motan ya kunna ya bar wajan dasauri direct gidansu Yasir ya nufa, motar Mum daya gani yasa yayi murmushi ya nufi side dinta, zaune ya sameta a falo tana k’allo. Ya k’arasa yana cewa
“My one and only mum”
Dagowa tai da fara’a dan bah wanda ke ce mata haka sai Masroor, hararanshi tad’anyi tana cewa
“Idonka knam Masroor”
D’an dariya yayo ya k’arasa kusada ita ya zauna yana cewa
“Zuwana na biyu fah knan yau dazu nazo bakya nan”
Gyada kai tai
“Eh tho nayau na yarda dan bana gida tun Safe”
Hira suka cigaba dayi shida mum din Yasir. Sunyi hira sosai sannan ya mata sallama ya wuce Side din Yasir
Zaune ya sameshi a falonshi yana shan lemu hannunshi rik’e da remote yana chanza tasha, dariya masroor yayi mara sauti
“Gaskiya friend kanajin dadinka”
Murmushi kawai yasir yayi ya mik’e yasauko cup ya zubama Masroor sannan ya mik’a mai..
Amsa yayi yana cewa
“Yadai kake nemana”
Cup din hannunshi ya aje yana k’allan Masroor
“Friend kayi ganganci dazu, mai zaisa kah dauko yarinyan nan a wannan halin da ake ciki. Dnt uh knw zai iya bata siyasan Daddy”
Shiru Masroor yayi yana shafa sumar kanshi
“Yes uh ryt, bt bazan k’ara haka bah”
Gyada kai Yasir yayi ya kurbi Juice din yace
“Yah kukai da mutuniyar taka”
Tashi Masroor yayi daga inda yake ya dawo kusada Yasir ya zauna yana cewa
“Friend she’s Cute, friendly, nice and…”
Saurin Katseshi Yasir yayi
“Hmm I wll kip on telling uh san yarinyan nan kake, bt tunda kace Aa watarana da kanka zaka ban labari”
Yatsine fuska Masroor yayi yadau car key dinshi yace
“Nidai na tafi”
Har bakin mota ya rako shi sukai Sallama ya nufo gida cikeda fargaban tambayoyin Mami..
A bangaren Sulthana fah..
Mu tara page na gaba dan jin yanda Sulthana zata kwashe da y’an gidan nasu
Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????
By Ummy Abduol
*Page 121 to 125*
Har bakin mota ya rakoshi sukai Sallama ya nufi gida cikeda fargaban tambayoyin Mami..
A bangaren Sulthana kuwa tafiya take sauri sauri duk inda ta bi k’allanta ake wasu kuma nunata. abin bah Karamin daure maka kai yayi bah, kanta a k’asa ta karasa gida. Da Sallama ta shiga ciki bah kowa a tsakar gidan dan haka ta aje trayn Sannan ta leka dakin Mama, zaune ta sameta k’an sallaya. Mama najin Sallamanta ta mik’e dasauri
“Sulthana ina kikaje? Ance anga wasu sun turaki mota”
Gabanta ne ya fadi ta fashe da kuka
“Wasu neh suka saceni”
D’an zaro ido Mama tai ta shiga jujuya Sulthanan tana dubata
“Basu dai miki komai bah koh”
Kai ta gyada tana cigaba da kuka a hankali..
Jin kamar magana daga dakin Mama yasa Hafsatu da Ameenatu fitowa daga dakinsu, dai dai nan Sulthana ta fito zata koma zaure, Hafsatu ce ta kada baki tace
“An dawo yawon dandin yawon iskanci, ai dama nasan bah wani saceki da’akai”
Tsaki Ameenatu tai tareda rik’e kugu
“Kuma bai wuce Wannan likitan nifah na tsaneshi, dan na lura dan iska neh. Koda yake ai yar uwa ya samu”
Mama tafito dasauro ta daka musu tsawa
“Kul! Ameenatu karna k’ara jin wannan maganan a bakin ki, wai meke faruwa neh? meyasa Ameenatu duk kika chanza”
Juya kawai tai ta shiga daki, itako uwar marasa kunya Hafsatu cigaba tai da Aibanta Sulthana har saida Mama tayo k’anta Sannan tabar wajan a guje..
Kuka sosai Sulthana take a inda take tsaye, karasowa Mama tai ta dafata
“Ki daina kuka kinji, wata rana sai labari”
Kai Sulthana kawai ta gyada batace komai bah
“Maza dau buta kiyi sallah kizo kici abinci” cewar Mama
Bah musu tadau butan ta dibi ruwa ta shiga bayi..
Sai Bayan isha’i Baffa ya shigo gidan, tun yana waje yaga shigowan Sulthana, baice komai bah ya shiga dakin Mama, Sannu da zuwa tamai Sannan ta kawo mai Abinci. Yanaci tanamai Fifita tace
“Sulthana ta dawo, kaji saceta akasoyi”
Tsaki Baffa yayi
“Ina ruwana, dama an saceta na huta”
Kallanshi Mama tai baki bude
“Mallan kakosan abinda kake fada”
Baice komai bah saima Sulthana daya soma kwalama Kira, tana gefen rijiya tsugunne tanacin Abinci taji kiran. Amsawa tai ta nufi dakin dasauri, Saida tai sallama Sannan ta shiga…
Hannu Baffa ya mik’a mata, tasan me yake nufi dan haka ta ciro kudin a gefen zaninta ta mik’a mai. Amsa yayi yana duba kudin tareda k’allan Mama wacce itama kudin take K’allo
“Kindai gani da idonki koh? Sababbin kudi gar haka”
Girgiza kai Mama tai ta kauda kai gefe. Tab’e baki yayi ya k’alli Sulthana wacce kanta ke kasa tana jiran hukuncin da Baffa zai yanke a kanta, ga mamaki sai taji yace
“Tashi ki bani guri, abinda zan gaya miki shine kada ki sake ki kawomin Cikin Shege gida”
Hawaye ya ciko idonta ta fita daga dakin ta nufi zaure ta fashe da kuka mai sauti.
“Haba Mallan wannan wanne irin abu neh da kanka kaita aibanta y’arka kana mata baki”
Dogon tsaki Baffa yaja ya wanke hannu cikin roban dake kusa dashi ya mik’e yabar dakin..
Kuka mai isarta tai Sannan ta sulalle a wajan ta kwanta, tunanin abinda ya faru dazu tai, Yau data fadama wani halin datake ciki har tadan samu sauki azuciyarta. Lumshe ido tayi ta bude a hankali tareda sakin Murmushi
“Yau naje birni” ta fada a hankali tana cigaba da murmushi Lol oh bakauyiya
Da shirmen tunane tunanen tah barci ya dauketa..
Yauma kamar kullum Bakin Kasuwa taje kamar yanda ta saba, mutane sai mata jaje suke itadai saidai tai murmushi idan sukace Allah kyauta na gaba bata amsawa a ranta kuma fadi take bah Amin bah kujimin Sulthanan nan fah haha
Yau da wata benz yaso bakin Kasuwan, chan bayan wajan yayi parking ya tura yaro ya kiramai ita. Tana zaune yaron yazo yace
“Wai kije ana kiranki”
D’an zaro ido tai tana k’allan yaran
“Wah?”
Girgiza kai yayi yana cewa
“Bansan sunanshi bah, wani neh a k’atuwar mota”
Bata kawo komai bah ta mik’e ta tabo Murja dake kusada ita
“Dan Allah murja ga tsaron Gyadata ina zuwa”
Tho murjan tace ita kuma Sulthana tabi hanyar da yaran ya nuna mata. Motan ta hango tayi slow ta tsaya tana k’arema motar kallo dan bah karamin burgeta yayi bah. Ta mirrow ya hangota ya fito yana mata murmushi, wajan motan ta k’arasa ta manna k’anta jikin windown tana K’allan ciki. Dagowa tai tana turo baki
“Ina K’awata”
Sumar kanshi ya shafa Yana y’ar murmushi
“Yau kam k’awarki bata nan suna biki”
Hannu ta rungume tana cigaba da turo baki.
Kurri Masroor yayi yana k’allanta, ganin hawaye cike a idonga yasa ya k’araso gabanta ya riko hannunta suka zauna bakin bishiyan dake wajan
“Karkiyi kuka kinji, gobe na miki Alkawari tare zamu zo”
K’ara tunzure baki tai ta kauda kai, d’an dariya yayi
“Dama haka kikeda rigima? Lallai akwai aiki”
Juyowa tai ta k’alleshi murya K’asa k’asa tace
“Yaya”