SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Gani tai ya mik’e ya shiga motarshi yaja yabar wajan da gudu. Bin motan tai da k’allo ta k’ara fashewa da matsanancin kuka, cikin muryan kuka take magana a hankali
“Shiknan yaya yayi fushi ya barni na shiga uku, meyasa Baffa baka sona? Menai maka??”
Hannu ta daura akai tana kuka wiwi
“Mama meyasa kika tafi kika barni? Kowa baya sona ki dawo dan Allah”
Mutanen dake wajan sun tausaya mata matuk’a jin kalaman datake fada..

Wasu ko basa sha’awar gyadan suna siya dan su rage mata radaddin datake ciki, haka taita bah mutane tana cigaba da kuka harta siyar. Hanyan da Masroor yasaba bi taketa k’allo tana hawaye, ganin bai dawo bah yasa ta mik’e jiki a sanyaye ta kama hanyar gida…

Gudu Masroor ke shararawa kamar zai tashi sama, Ikon Allah ne kawai ya kaishi gida, baiyi wani k’wakwaran parking bah ya fito ya nufi side din Mami idanunshi jawur. Bell ya danna aka bude mai ya shiga, masu aiki sai gaidashi suke anma baiko kallesu bah ya nufi falon Mami. Ganin bata falon sai bak’inta dake zaune suna jiranta yasa ya k’arasa dakinta, knocking yayi a kofar dakin ta amsa tareda tambayan waye
“Masroor” yace atakaice
Bashi umarni tai daya shigo

Yana shiga suka hada ido ta mik’e dasauri ganin yanda idanushi suka rune
“Son whats wrong”
K’asan dakin ya zauna yana cigaba da ajiyan zuciya
Mami ta k’araso kusadashi tareda dafashi
“Son tell me whats wrong pls, meke damunka? Why are you like dis”
Kama hannunta yayi ya ya dago ya k’alleta idaunshi Cikeda kwalla
“Mami som1 wnts 2 snach her from me, I love her, I so much love her. Shes my happiness, I cnt do without ha”

Fashe mata da kuka yayi ya duk’ar da kanshi kasa
Rungumoshi jikinta tai itama hankalinta tashe
“Its ok son, stop crying. Cool down and tel me meya faru”

Kasa magana yayi sai kukan daya cigaba dayi, dak’yar ta ja hannunshi suka mik’e tsaye, hannunshi ta rik’e ta kaishi side dinshi. Bedroom dinshi ta shiga dashi tareda zaunar dashi kan gado, tsugunawa tai ta ciremai cover’n dake kafanshi sannan ta mik’e tana shafa suman kanshi
“Its ok son have some rest, idan kah huta sai muyi maganan kaji”
Kai kawai ya gyada mata, ta fita daga dakin cikeda damuwa…

Masu aiki tasa suka kaimai abinci, anma koh kallan abincin beyi bah..waya Mami ta d’auka ta kira Yasir bai d’au lokaci bah ya k’araso gidan a rud’e. Falon Mami ya fara zuwa saboda tace ya sameta.
Da sallama ya shiga ya sameta zaune tana y’an rubuce rubuce. Zama yayi ya gaidata, ta amsa fuska bah walwala..

Duk abinda ya faru ta zaiyanama Yasir sannan tace
“Yasir nasan kai zakafi kowa sanin wanda Masroor yakeso, baya cikin hayyacinshi dats why ban tambayeshi bah”
Yasir yayi murmushi ya gyara zama yaba Mami labarin tun sanda suka soma ganin Sulthana har zuwa daukota da Masroor yayi da labarin data basu nata. Mami ta share k’walla tace
“Yasir meyasa tuntuni baku fadamin bah? Yarinyan nan bah kalar Masroor bace anma kodan yanda yak’e santa zan hakura kuma nasan Alhaji zai yarda”

Shiru yayi baice komai bah kanshi a k’asa, Mami ta cigaba da cewa
“Ya zamuyi yanzu Yasir? Masroor na dak’i yana kuka”
Jin haka yasa Yasir mik’ewa dasauri ya nufi side din Masroor hankalinshi tashe..

Zaune ya sameshi yanda Mami ta barshi, saidai yanzu bah kukan yake bah. Ya k’arasa ya zauna kusa dashi
“Friend why all this?, uh have to be strong. Komae zai zama normal”
Masroor baice komai bah sai girgiza kanshi dayayi. Dak’yar yasir yasamu yaci abincin ya hada mai ruwan wanka yayi sannan yajashi suka tafi yawo ko hakan zaisa ya rage tunanin dayake…

Washe gari kamar yanda Fareed da Sa’ood sukayi hakan neh ya faru, karfe hudu a kauyensu Sulthana tai musu, bayan layinsu Sulthana sukai parking motarsu, yaro suka samu suka hadashi da sabuwar dari biyar ya musu k’iran Babban Almajirin mallan.

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

     *Page 131 to 135*

“Bro Fareed zakaje dani wajan Umma”
Rik’e baki Mami tayi tana kallan Mahnoor
“Mahnoor da yawo, sae kace taci kafan kare. Tho schl din fah”
Zumbure zaki tayi ta juya baya,
“Mami kinga fah sai bro fareed ya rink’a kaini”
Kanta fareed ya shafa yana y’ar murmushi
“Sis ki bari idan akai hutu da kaina zanzo na daukeki kinji”
Kai ta gyada ta mik’e tabar wajan tana gungunai..

“Likita bokan turai aure fah?”
Sosa kai yayi kanshi a k’asa
“Mami na kusa, kiris ya rage”
Gyada kai Mami tai tana murmushi
“Gaskiya kah kyauta kaga wadannan”
Ta nuna Yasir da Masroor
“Sunk’i aure suna nan sai gantali”
Dariya mai sauti Yasir keyi ya dafa kafadan Masroor
“Mami ai shagwababen naki ya kusa, hmm zan baki labari anjima”
Dukan wasa Masroor yakai mai
“Mami k’arya fah yake”
Tabe baki tai ta kauda kai kudai kuka sani..

Fareed ya mike yana cewa
“Mami zan tafi, dama na shigo ne mu gaisa inada patients a asibiti”
Mami itama ta mik’e da Fara’a
“Kah gaidamin dah hajiya sai nazo, wallahi duk hidimar campaign din nan neh ya hanani zuwa”
“Ai itama bata zama kullum bata nan itama dai campaign din neh” cewar Fareed
Yasir yace
“Inafa zama wajan matan governor dana duty governor”
Dariya sukasa duka, Masroor da Yasir suka raka Fareed har Bakin motarshi, sukai Sallama ya tafi…

Lokaci nata tafiya, shakuwa sosai ta shiga tsakanin Sulthana da Masroor harda Yasir, kullum a bakin tasha suk’e haduwa da Masroor suyita hiransu har tayata Saida gyadan yake taitamai dariya wai bai iya badawa bah. A bangaren Dr Fareed ma yakanzo lokaci zuwa lokaci wajanta watarana ta fita wata rana bata zuwa, santa yake bana wasa bah. Yanke hukunci yayi kawai zai samu mahaifinta da magananta ko Allah zai dace.
Tareda abokinshi Sa’ood sukaje gidansu Sulthana, a k’ofar gida suka samu Baffa xaune yana koyarda Almajiransa. Suka karasa inda yake, yana ganinsu ya soma washe baki ganin zankadediyar motar da zukayi Parking.
“Sannunku da zuwa karku zauna a wannan tabarmar yara duk sun bata” cewar Mallan

Gida ya shiga jikinshi na rawa ya dauko sabuwar tabarma ya shinfida bakin kofa sannan yace
“Bismillanku ku zauna”
Zama sukai, Mallan ya mik’a musu hannu dan suyi musbaha, mak’e hannu sukai yaxe
“Aa mu gaisa mata ya haka”
Dak’yar Fareed ya mik’a mai hannu suka gaisa
Mallan yace
“Ban shaidaku bah”
Sa’ood neh ya duk’ar dakai yace
“Sunana Sa’ood sai Abokina Fareed” ya nuna Fareed daya duk’ar dakai yana murmushi
Sulthana ta fito gida rik’e da kofin silver, slippers dinta ta cire ta tsugunna
“Ina wuninku”
Sa’ood neh ya masa yana kallanta,
D’an dagowa Fareed yayi suka hada ido tai saurin dauk’e kai ta aje Kofin tabar wajan..

Sa’ood ya cigaba da Magana
“Mu y’an cikin garin Kano neh a gwanma ja, Mahaifinshi d’an siyasa neh, shike neman mataimakin Gwamna na wannan jaha. Shi kuma cikakken likita neh”
K’ara washe baki Mallan yayi

“Aa Madallah sannunku da zuwa, ina fata dai lapia”
Sa’ood ya k’ara duk’ar dakai
“Abokina nah neh Yaga y’ar wajanka yanaso shine mukazo mu nemi izini”
Mallan ya k’ara gyara zama
“Kai Madallah nayi farinciki da jin wannan maganan, tho wacecce daga ciki hafsatu koh Ameenatu”
Murmushi Sa’ood yayi yace
“A’a Sulthana”
Nan da nan fara’ar fuskan Mallan takau ya hada girar sama data k’asa. Jin Mallan yayi shiru Yasa Fareed yad’an dago ya kalleshi, ganin yanda ya murtuke fuska yasa yasha jinin jikinshi
“Sae dai kuyi hakuri dan na riga nama Sulthana miji”
Dago kai Fareed yayi da sauri yana K’allan Mallan
Sa’ood yace
“Tho shiknan bbu damuwa mun gode Allah ya saka da Alkhairi. Allah kaimu ya basu zaman lapia”
Ameen Mallan Yace atakaice

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button