SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

        *Page 11 to 15*

Wannan knan..

Kwanaki sunja Sosai, Kullum Sulthana Fuskantar Wahala wajan Baffanta tak’e, sai in baya gida tak’an danji dadi wajan Mama ko Ameenatu.
Zaune Tak’e tana tsince Shinkafa lokaci lokaci takan sah bayan Hannunta tana share hawayen dak’e Gangaro mata, Baffa neh ya fito daga daki yana K’allanta
“Bah Rashin Lafiya bah Allah Yasa mutuwa zakiyi sai kinyi Aikin nan, Dan tsabar iskanci harni zaki duba kice bakida lapia”
Ameena ce ta fito daga bayi hannunta rik’e da buta
“Baffa dan Allah kai Hakuri, na Yarda ni zan mata aikin na yau”
Kini kini yayi darai
“Ban yardah bah kuma ban lamunta bah, Karna Sak’e na ganki kindau Tsinke a cikin Gidan nan. Anfaninta knan Ki Barta tayi”
Bai kara cewa komai bah yayi shigewansh dak’i..

Hafsatu ce ta fito tana dariya mai sauti harda rik’e ciki
“Yaya Ameena knan, menene na takura kanki kan Wannan Kuchakan Yarinyan, Nifa Wallahi na Tsaneta Shegiya sai kyau kamar Aljanna”
Dogon Tsaki Ameena taja batace Komai bah Ta wuce dakinsu, Binta da Kallo Hafsatu tai Sannan ta maida dubanta ga Sulthana
“Yarinya Koh kukan jini zakiyi sai kinyi Aikin nan, kima gama kizo ki wankemin Uniform”
Batace Komai bah ta Cigaba da Tsintar shinkafanta..

Dafa Dukan shinkafa ta dafa Musu, Saida ta zubama Kowa Sannan Ta kankare K’anzon ta juye a Leda Dan Ko kwanukan Gidan Baffa ya hanata Anfani dasu, Zaure ta nufa wanda a yanzu ta maidashi kamar dak’inta, Muryan Baffa taji yana Kiran Sunanta
Dasauri ta Sak’i ledan K’anzon ta nufi wajanshi tareda Durkusawa
Kwano ya ajiye mata a gabanta cike da Gyada Danye
“Maza ki Wanke shi ki daura a Wuta dan Yau zaki fara min Talla”
Dasauri ta Dago ta K’alleshi da Mamaki
A ranta ta maimaita “Talla”
Mama ta Fito Dasauri jin Abinda Ya Ambata
“Haba Mallan, Wallahi kaji Tsoron Allah bai kamata kana irin Wannan bah, dur Arzikin dah Allah ya maka kace kuma zaka Rinka daurama Yarka Talla”
Baice Komai bah Ya Kalli Sulthana
“Zaki dau gyadan ko saina B’aballaki a nan”

Da Sauri jiki na Rawa tadau Gyadan ta Nufi Bakin Rijiya Hawaye na Gangara a Idonta, Runtse ido tai jin Kanta Na Sara mata, Dakyar ta Wanke Gyadan ta Hada wuta ta daura ta koma Gefe tana Dubawa, Jin Zazzabi na neman Rufeta Yasa ta Mik’e dakyar ta shiga dak’insu Ameena gabanta na Faduwa
Tako ci Sa’a Hafsatu Bata Dakin
“Dan Allah Yaya Ameena ki taimakeni da Maganin Ciwon Kai”
Kallanta Ameena tai cikeda Tausayawa
“Kiyi Hakuri Sulthana, Duk Tsanani Sauk’i na nan Zuwa Kinji”
Kai Kawai ta Gyada batare da Tace Komai bah. Maganin Ameena ta bata Da Ruwa Tasha Sannan tai mata Godiya tabar dakin..

Saida ta dafa Gyadan ta Juye Sannan Tayi Sallama dak’in Baffa, Fitowa Yayi
“Yauwa Kin Gama?”
Kai ta Gyada Kanta a Kasa
“Maza ki juye a Faranti ki dauka ki Shiga Gari, Kuma Wallahi idan Kika Dad’e Nida Keh neh, Sannan gwangwani naira Goma”
“Tho” Kawai tace tabar Wajan, Gyadan ta Dauka ta Dau Hijabinta daya Sha Miya da kura tasa Kafanta ko Takalmi babu tabar Gidan. Tafiya kawai take batareda Tasan Inda zata nufa bah dan Talla Bakon Al amari neh a wajanta, Kicibus sukai da K’awarta Sadiya Tana Dawowa Daga Islamiya, Turus tai da Mamaki tana K’allan Sulthana

“Yau Kuma meh idona keh Gani Sulthana, Talla??” cewar Sadiya
Dan Murmushi Kawai Sulthana tai Tana Kokarin Wucewa, Hijabinta Sadiya taja Hakan Yasa Ta Tsaya batare da ta juyo bah, Gabanta Sadiya taje ta Tsaya tana K’allanta
“Sulthana Nice Fah Sadiya yau kuma Hanaki Magana da Kowa akai”
Dakyar ta Iya bude Bak’i Tace
“Dan Allah Sadiya kiyi hakuri ki bani hanya na Wuce, Wallahi Ance idan na dade sai an Dukeni”
Nan da Nan idonta ya cik’o da kwalla..

Jan Hannunta Sadiya tai duka koma Gefe
“Kiyi Hakuri Sulthana, Banajin Dadin Yanda Nak’e Ganinki, Inasan Zuwa wajanki Anma ina tsoron Kar Baffa yamin Fada koya Dak’eni, Kinsan meh?”
Kai Sulthana ta Girgiza Alamar Aa
Kullum da Daddare Zan Rinka kawo Miki abinci a zaure ko in Rinka turo Sani yana kawo miki
Murmushi Sulthana tai Wanda Saida Dimple dinta Masu K’ara mata kyau suka Bayyana
“Nagode Sadiya”
Itama Murmushin Tai, A Haka Suka Rabu Cikeda Kewar Juna.
Rasa Inda Zata Nufa Tai, Yanke Shawara tai ta Nufi Bakin Kasuwa da Gyadar, Cikin Ikon Allah Nan da Nan koh aka siye ta dawo gida. Baffa ta mik’a mah kudin Yanata Washe bak’i
“Yauwa haka Akeso, Gobe mah zak’i sake dafawa”
Mama na gefenshi sai K’allanshi tak’e Cikeda Takaici.
Koh hutawa batai bah Ta daura Aikin da yakamata tai na yanma, Bata Gamaba Saida Aka Fara Kiraye kirayen Sallan Isha’i. Alwala tai Ta koma zaure tai Sallanta tana zaune Hafsatu ta shigo Gidan Tana Wani Girgiza tana Waka
Mama dake tsakar Gida Ta K’alleta da Alamar Mamaki
“Hafsatu daga ina Kike? Tunda Akai Sallan Azahar kika Fita Gidan nan sai yanzu kike gadaman Dawowa”
Turo Bak’i tai ta Turo dan kwalli Gaban Goshi
“Haba Mama ni shiknan banida Yancin Kaina Duk inda Naje Sai aita Tambaya nah”
Ameenatu ta Fito daga dakinsu Sanye da Hijabi da Alama Sallah ta Idar
“Hafsatu Ashe Bakida Hankali, Yanzu Mama kike gayama Irin Wannan Maganan??”
Batace Komai Bah Tadau Buta Tayi Shigewanta Bayi tana Magana K’asa K’asa

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

        *Page 16 to 20*

Batace Komai bah tadau buta tayi shigewanta bayi tana Magana Kasa kasa. Girgiza kai kawai mama tai batareda tace Komai bah, Wuraren Karfe tara na safe Lokacin Baffa ya shiga gida Sadiya ta shigo zauren dauke da kwanon Abinci. Da fara’a Sulthana ta tareda suna dan hira K’asa kasa Tanacin Abincin
“Sulthana kin daina zuwa makaranta, bah Islamiya bah Boko Kullum sai Mallamai sun tambayeni keh”
Dan murmushin takaici Sulthana tai
“Baffa ya hanani zuwa makaranta, ko dah chan dama umma ce keh biya min”

Hawaye ta share tana cigaba da kallan Sadiya
“Bansan menai ma baffa bah, Ni kadai a Garin nan nake shan wuya bansan menai bah”
Kuka neh yaci karfinta, Sadiya ta rungumota K’irjinta ta shiga Lallashinta
“Kiyi Hakuri Sulthana, ko kin manta Karatun dah Mallan Dauda ya mana, Innallaha Ma’a Sabirin, Allah yana Tareda masu hakuri”
Shiru Sulthana tai tana cigaba da kukan K’asa kasa
“Ki daina kuka kinji, Kinsan menene?”
Kai Sulthana ta girgiza Alamar Aa
“Gobe idan Kikaje Gaida Baffa ki kara mai magana akan Makarantan ki, idan Allah ya dauraki a kanshi zai yarda”
Kai Kawai Sulthana ta daga batare da tace komai bah..

Mikewa Sadiya tai,
“Zan tafi gida kinga dare yayi gobe ma zan dawo kinji”
Kai Sulthana ta daga mata tana murmushi, Sauran Abincin da ta rage ta juye a kwano ta mik’a mata kwanon
“Nagode Sadiya ki gaida Goggo”
Zataji cewar Sadiya ta Fita daga zauren Cikeda Tausayin Kawar nata..

Washe Gari ana Sallan Asubah tahau Aikin Gida, Baffa na dawowa ta Karasa kusa dashi ta gaidashi, Bai amsa bah saima tsaki dah yayi ya bar wajan ya shige dakinshi. Komawa tai ta cigaba da Aikinta kamar yanda ta saba, da wuri Ta gama ayukan tah tana zaune bak’in murhu dan lokacin ana dan sanyi
Hafsatu ce ta fiti daga daki tana mik’a
“Keh Sulthana, Maza dauramin Ruwan wanka”
Tho tace ta mik’e dan Daurawa jin Muryan Amina tai tana cewa
“Karki sakeki daura wani ruwa, Idan bazata daura da kanta bah tah bari”
Da Mamaki Hafsatu ta Kalli Ameena
“Haba Yaya Ameena, Makaranta fah zani ki kyalleta ta daura min mana”
Murnushin takaici Ameena
“Hafsatu ki tausaya mah yarinyan nan mana, duk aikin gidan nan ita tak’eyi yakamata ki tausaya mata”
Tsaki Hafsatu taja
“To ni ina Ruwana, Ai bani kesata aikin bah, Baffa neh dan haka ni bah ruwana”
Jin Hayaniya a tsakar Gidan Yasa Baffa ya fito
“Lapia meke faruwa neh naketa jin hayaniya”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button