SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannu Fareed yasa a aljihu ya ciro bandir din y’an dari biyu ya ajema Mallan.
“Gashi bah yawa”
Washe baki yayi ya taba kudin
“A’a ayi haka”
Sa’ood yayi murnushi
“Babu komai ai”
Ganin suna k’okarin tafiya yasa yace
“Nace bah”
Fareed ya dago dasauri yana k’allan Mallan, cigaba da magana mallan yayi
“Akwai yaninta su biyu da hafsatu da Ameenatu, duk wacce yakeso ai sai abashi”
Fareed ya yatsine fuska
“A’a Mallan mun gode, zamu tafi”

Mik’ewa sukai Mallan ya rakosu har bakin mota yanata godiya, sukaja mota suka bar k’ofar gidan cikeda takaici. A hanya Sa’ood ya nisa yace
“Doctor akwai wani abu danai observing”
Fareed ya juya kadan ya kalli Sa’ood sannan ya maida dubanshi ga titi,
” kamar na meh fah?”
Naga k’iyaiyar yarinyan nan a idonshi, bakaga k’allanda yake mata sanda ta kawo ruwan nan bah..

Murmushin takaici Fareed yayi
“Na dad’e da gano akwai matsala a gidan, yarinyan tak’i bani hadin kai naji damuwanta”
Sa’ood ya gyara zama
“Ga shawara”
Parking Fareed yayi ya juya yana k’allanshi
“Mai zai hana mu samu wani ya bamu labarin yarinyan?”
Lallausan Murmushi Fareed yayi
“Yes! Uh ryt, y not gobe sunday sai mu dawo”
Sa’ood yace
“Haka za’ayi”
Haka suka kama hanyan gida suna tattauna yanda zasu bulloma Alamarin..

Rai bace Mallan ya shiga gida, baiga Sulthana a zaure bah, ya k’arasa gidan ya soma kwallama Sulthana kira da k’arfi rai bace. Jin yanda yake kiran yasa Ameenatu ta fito itada Hafsatu dan idan sukaji wannan kiran to bah lapia bah. Jiki na rawa Sulthana ta fito daga bayi ta aje butan ta k’araso wajan, Mama ta fito tana tambayan lapia. Nuna Sulthana yayi da yatsa ranshi bace Idanunshi sunyi ja..

“Indai ina raye tho ki sani bake bah aure, keh kina tunanin akwai mai abinda zai rabaki da gidan nan? Sai dai mutuwa”
Mama tace
“Lapia Mallan wai meke faruwa neh”
Zayyana musu duk abinda ya faru yayi, hankalin Ameenatu ne ya tashi, dama likita d’an babban gida neh? Hafsatu koh tabe baki tai tana cewa
“Ai Baffa duk sune suke fita da ita, dama ka kyaleta anyi auren kwana biyu neh ya sakota”
Kunnen Sulthana baffa ya kama
“Idan na K’ara jin an ganki da likitan nan, keh ko kallanshi kika karayi balle har ki gaidashi saina kasheki a gidan nan”
Gyada kai Sulthana tai hawaye nabin kuncinta,
“Tashi ki bani waje”
Mikewa tai jiki na rawa ta nufi zaure ta saki matsanancin kuka..

“Abinda kakeyi Mallan baka kyautawa, tunda bakasan ka bude ido kaga yarinyan nan a gidan nan bah saikai mata auren bah tunda ta samu wanda ya fito yana santa”
Jin haka yasa hawaye ya zuboma Ameenatu ta shige daki ta fada kan gadonsu ta fashe da kuka.
Tsaki Baffa yayi
“Likita babba, wanda mahaifinshi ke kokarin hawa babban matsayi shi zan dau wannan dabban naba? Ina! Tunda abin yazama haka cikin Almajiraina zan aura mata kuma anan zasu zauna tare dani ta cigaba damin bauta dan shi yafi dacewa da ita”
Shekewa da dariya hafsatu tai harda tafawa
“Gaskiya neh Baffa haka yayi”

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

   *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

       *Page 141 to 145*

K’arfe hudu a kauyensu Sulthana tayi musu, bayan layinsu Sulthana sukai Parking motarsu, yaro sula samu suka hadashi da sabuwar dari biyar ya musu k’iran Babban Almajirin Mallan. Sai washe baki yaron yak’e dagudu ya nufi runfar Almajiran, yakoyi Sa’a ya sameshi zaune shi kad’ai a dakinsu yana karatu. Tare suka k’araso wajan sannan yaran yabar gurin cikeda murna..

Musabaha suk’ai Sannan Sa’ood yace
“Sunana Sa’ood sai abokina Fareed, mu yan cikin garin kano neh. Munzo akan maganar wata yarinya Sulthana munasan musan labarinta dan gwamnati na buk’atar a taimaka ma yara masu irin shekarunta”

D’an jim yayi Sannan ya dago yace
“Ni sunana Sani kuma Almajiri neh ni, kuyi haquri bazan iya fadan wani abu dangane da cikin gidan Malamina nah”

Hannu Fareed yasa a Aljihu ya ciro bandir din y’an dari biyar ya mik’a mai yana cewa
“Kah taimaka, ka fada mana munaso neh mu taimaka mata”

Jim Sani yayi yana tunani Shi kanshi bayasan abinda akema Sulthana a gidan, yanke shawara yayi kawai ya fada musu dan haka yace

“Kuzo ga Bakin bishiyar chan akwai inuwa sai mu zauna”

Bah musu suka nishi suka zauna, nan Sani ya soma basu labari tiriyan tiriyan iya abinda ya sani. Kuka neh kawai Fareed beyi bah anma idanunshi sunyi jah, shi kanshi Sa’ood hankalinshi bah k’aramin tashi yayi bah. Sa’ood neh yayi k’arfin halin cewa

“Mallan Sani anya kuwa Mallan neh ya haifeta”

Dagowa yayi dasauri yana k’allanshi da Mamaki

“Shine mahaifinta mana”

Girgiza kai Fareed yayi fuskansh bah Annuri

“No bashi ya haifeta bah, dan mahaifi bazai taba muzgunama D’anshu haka bah”

Sani yayi murmushin takaici Yace

“Mallan jamilu shine ya haifi Sulthana, duk kuma wanda zaka tambaya a kauyen nan abinda zai fadama knan”

Fareed neh ya mik’e dasauri yana k’arkade rigan jikinshi, Sa’ood ma ya mik’e yana k’allan Sani

“Mungode sosai Sani, zamu tafi idan bukatar k’ara ganinka ta taso zamuzo mu sameka”

Shima mik’ewan yayi ya basu hannu sukai musabaha

“Bbu komai ai ina maraba da dawowanku matukar za’a san yanda za’ayi a taimaka ma Sulthana”

Kudin Fareed ya mik’a mai, ya nok’e yaki k’arba

“Kubar kudinku, Allah dai ya baku sa’an niyyan da kuka dauka”

Ameen sukace suk’a k’arami godiya. Kasa driving Fareed yayi Sa’ood ya amsa keyn motan suka bar wajan kowa da abinda yak’e sakawa a Ranshi..
Fareed yayi ajiyan zuciya yana k’allan Sa’ood

“No mattet how hard the situation will be, no matter how bad. Sai na fitarda Sulthana daga k’angin nan datake ciki, koda kuwa zanyi asarar dukiyana da matsayina matsawar zata kasance cikin farinciki da Annashiwa”

Girgixa kai kawai Sa’ood yayi baice komai bah har suka k’arasa gida..

Ala ala Mami tak’e Daddy ya dawo, bai dawo gidan bah sai wuraren k’arfe goma da rabi na dare. Saida yaci abinci ya huta sannan Mami ta sameshi a office dinshi dake cikin gidan, zama tai kusa dashi
“Sannu da hutawa”

Da Fara’a yadan juyo yana k’allanta

“Sannu uwargida sarautar mata”

Murmushi tayi Sannan tace

“Alhaji inaso neh muyi magana dakai kuma naga kamar kana busy”

Takardun hannunshi ya aje ya matsar da system din dake gabanshi

“Ina jinki”

Jim tai tana k’allanshi Sannan tace

“Akan Maganan Masroor neh, yana daki tun dazu yak’i cin abinci sai aikin kuka yake, saima danai ma Yasir..”

Saurin katseta Daddy yayi hankali tashe

“Meke damunshi? Meyasa yake kuka?”

Nan Mami ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar dashi Sannan ta fadamai yanda sukai da Yasir .

Baice komai bah yadau waya ya soma neman layin Masroor, yana dauka yace

“Kah sameni a falona”

Bai jira mai zaice bah ya kashe wayan sannan ya mik’e yana k’allan Mami

“Muje falona”

Koda suk’a karasa falon sun sameshi zaune akan Carpet kanshi a k’asa. Daddy ya zauna kusada shi yana k’allanshi

“Son meke faruwa? Karka boyemin fadamin damuwanka”

Baice komai bah k’anshi na k’asa, k’ara magana Daddy yayi Sannan ya d’ago jajayen idanunshi yana k’allan Daddy

“Daddy inada wacce nakeso but..”

Shiru yayi ya kasa k’arasa maganan

Daddy yayi murmushi

“Go on ina jinka”

Masroor ya sunkuyar dakai sannan ya cigaba

“Sunanta Sulthana ina santa daddy kuma babanta yace zai aura mata almajiri”

Daddy ya k’alleshi da mamaki

“Almajiri”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button