SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai Masroor ya gyada, daddy ya nisa yace

“Wanene Mahaifinta a garin nan”

Gaban Masroor neh ya fadi jin abinda ya fada, Mami tai saurin amshewa

“Alhaji inace munyi wannan maganan tun achan”

Hannu Daddy ya d’aga mata alamar tai shiru yace

“Ina jinka”

K’ara sunkuyar dakai yayi

“Daddy babanta bah kowa baneh a kauye suke”

Har daddy ya bud’e baki zaiyi magana Mahnoor ta shigo falon dagudu, jikin Mami ta d’ane tana kallan Daddy tana dariya

“Daddy uh welcome”

Murmushi daddy ya mata
“Thank uh my baby, ya school?”

Ta amsa da lapia lau. Hade rai Mami tai

“Tashi min a jiki, bakiga muna magana baneh kin wani shigo bako Sallama”

Zumbure baki tayi ta mik’e zatabar wajan, daddy yace

“Kyalleta zo nan abinki babyna”

Da d’an murmushi ta k’arasa ta zauna kusada Daddy.

“Maminku ta fadamin duk yanda kukai da ita, da kuma yanda zukai da yasir. So zan fara sawa a bincika min Yarinyar da Asalinsu idan har babu matsala insha Allahu she will be ur wife”

Dago kai yayi da Fara’a yana k’allan Daddy

“Daddy dagaske?”

Murmushi Daddy yamai tareda kyada kai. Mahnoor ta k’alli Masroor

“Bro Sulthana?”

Kai ya gyada mata Cikeda farinciki

Tsalle sukaga Mahnoor tahauyi tana murna, Mami da mamaki tace

“Ina kika santa”

Tsagaitawa tai tana k’allan Masroor. Da rarrafe ya matso kusada Daddy ya zauna kusada k’afarshi yanatamai Godiya Sannan ya mik’e yana hararan Mahnoor yabar wajan. Tasan mai yake nufi, murguda baki tayi ta juya tahau bah su Mami labarin zuwanda sukeyi gurin Sulthana..

Mami ta tausaya mata sai taji tanasan yarinyan tun bata hadu da ita bah…

Kwana biyun nan da Masroor baizo bah kullum Sulthana batada aiki sai kuka. Hakan yasa takanje gidansu Sadiya idan tadau tallan dan ta debe mata kewa. Yau tana zaune bakin tasha tayi tagumi tana k’allan hanyar da Masroor ya saba biyowa. Kamar a mafarki taga motarshi ya doso wajan, dasauri ta mik’e ta karasa inda yayi parking. Fitowa yayi yana mata murmushi, zumbure baki tayi ta juya ta koma inda take zaune

Murmushi yayi yabi bayanta, kusa ita ya zauna yana k’allanta. Kauda kai tayi ya juyo da fuskanta. Hawaye ya gani na gangarowa daga idonta

“Omg! Haba Beauty meya faru? Meyasa kike kuka”

Ai kaman jira take ta fashe da kuka harda shesheka, kanshi ya dafa

“Pls stop crying banasan kukanki beauty”

Hankie ya dauko ya soma goge mata hawayen dake fuskanta yana murmushi

“Me aka miki kike kuka?”

Zumburo baki tai

“Bakai baneh ka daina zuwa bah kullum sai nazo nan ina jiranka”

Kallanta yayi da Mamaki

“Kinyi kewana neh?”

Hannu tasa ta rufe fuskanta tana murmushi, shima murmushin yake cikeda Farinciki

“Oh come on! Fadamin kinyi kewana?”

Kai ta gyada mai, murmushi yayi mai sauti

“Nima nayi kewanki beauty, idan natambayeki wani abu zaki fadamin?”

Eh tace tana kallanshi, saida yayi jim sannan yace

“Kina sona?”

Dasauri ta mik’e tabar wajan tana dariya. Shima dariyan yayi kasa kasa, dakyar ya lallabata ta dawo ta zauna yace

“I so much love uh my beauty ina sanki sosai”

Hannayenta biyu tasa ta rufe fuskanta tana murmushi…

Shakuwa mai k’arfi ya k’ara shiga tsakaninsu, har Mami da daddy sun saba da hiran Sulthana da Masroor ke musu kullum. Lokaci nata tafiya, har yanzu bah abinda ya chanza dangane da k’iyayar da Baffa kema Sulthana…

Bayan wata d’aya

Alhamdulillah anyi Election Allah yaba Daddy sa’a yanxu shine gwamnan Jahar Kano, Alhaji shuaibu mahaifin Fareed shine mataimakinshi. Bayan komawansu government house Masroor ya matsama Mami akan zuwa gidansu Sulthana saboda nan da sati d’aya zai koma school, Mami na samun Daddy da maganan yace

“Nima abin na raina mantawa nai ban fada miki bah, gobe in Allah ya kaimu za’aje nema mai aurenta”

*tho fah* anya kuwa?

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

   *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

     *Page 146 to 150*

   *Masroor Fans* Wannan shafin naku neh... fatan Alheri gareki *Hajiya Fateema* kinfi kowa san littafin ina godiya da soyaiyarki gareni.

“Nima abin na raina mantawa nai ban fada miki bah, gode in Allah ya kaimu za’aje nema mai aurenta”
Dad’i sosai Mami taji ai dasauri ta fita ta k’ira Masroor a waya Tareda fadamai Albishir. Murna wajan Masroor ba’a magana suna gama wayan ya kira yasir ya sanar dashi lokacin shi yana hanyar zuwa wajan Fareed dan kwanakin nan da akai election tare suketa shige da fice hakan yasa suka k’ara sabawa sosai..

Yana isa Asibitin yamai waya ya sanar dashi isowarsa. Fitowa Fareed yayi yana murmushi

“Old friend na d’auka fah wasa kakemin”

D’an dariya Masroor yayi yana shafa suman kanshi

“Ai nafika zumunci”

Hannu Fareed ya mik’a mai suka tafa suna dariya

“Kaji talle kema audi gori, duk bah wannan bah friend. Naga sai annashuwa kakene fadamin meya faru?”

K’ayattacen murmushi Masroor yayi

“Gobe in Allah ya kaimu za’aje nema min aure”

“Woaw” Fareed yace cikeda farinciki

“Who is dis lucky beb”

Masroor ya girgiza kai

“Sunanta su…koda yake zaka ganta wata rana da kanta zata fadama sunanta”

Hannu Fareed ya mik’a mai

“I’m very happy 4 uh Friend, Allah ya kaimu musha biki”

“Ameen, tho kaifa yaushe ne nakan?” cewar Masroor

Ajiyan zuciya Fareed ya sauke

“Nikam bah yanzu bah”

Da mamaki Masroor ya kalleshi

“Why?”

Juyowa Fareed yayi yana fuskantan Masroor

“Wata yarinya na gani shes young n beautiful. Saidai yarinyan na cikin Matsala infact namadai je naga mahaifinta yak’i amincewa”

Gaban Masroor neh ya ya fadi. Zuciyarshi ta shiga zargin kodai shine wanda sulthana take fada mishi likitan dayaje nemanta. Dagowa yayi da Alamar damuwa

“Y’ar wacece aina take?”

Murmushin takaici Fareed yayi yana girgiza kai

“Bah y’ar kowa bace, a kauye ma suke.”

Kan Masroor neh ya soma sara mai, juyawa kawai yayi fareed ya matso yace

“A’a Old friend bamu gama hiran bafa ina kuma zaka?”

Da hannu ya nunama Fareed kanshi dak’yar ya iya cewa

“Gida zani kaina ke ciwo”

Bai jira mai fareed din zaice bah ya figi mota yabar Asibitin da sauri ya nufi gida…

Hankali tashe ya k’arasa gida, side dinshi ya wuce kai tsaye bai kuma fitowa bah har washe gari…

Safiyar Ranar lahadi da wuri Abokanan daddy su biyu suka shirya Yasir ya musu jagora zuwa k’auyensu Sulthana. Kasancewar bai taba zuwa bah da kwatance Suka gane gidan, a kofar gidansu sukai Parking motarsu. Mallan na ganin Katuwar mota ya mik’e dasauri ya fito daga runfar Almajiransu..

Yasir ne ya fito ya k’arasa suka gaisa da Mallan sannan ya fada mai tareda baki suke. Nan da nan Mallan yahau washe baki ganin mutanen da suka fito daga motan daga gani bah k’ananan mutane baneh..

Tabarma ya dauko ya shimfida suka zazzauna, Mallan ya soma gaidasu suka amsa, d’aya daga cikinsu ne ya fara magana

“Sunana Alhaji ilyasu sai kuma abokina Alhaji Tanimu, daga Cikin Gari muke. Alhaji Aminu Datty gwamna maici yanzu shine ya turo mu dan mu naima ma d’anshi auren Y’arka”

Nan da nan Mallan ya rud’e,

“Anya bayin Allah ni kuwa Mallan Jamilu?”

Alhaji Tanimu yayi Murmushi ganin Yanda ya rud’e

“Kwarai kai”

Gyara zama yayi jikinshi na rawa

“Wacce daga ciki Ameenatu koh Hafsatu?”

Yasir dake gefe yace

“Sulthana”

Had’e rai Mallan yayi baice komai bah, ganin yanda ya sauya fuska yasa Alhaji ilyasu cewa

“Koh Akwai damuwa neh”

Dagowa yayi ya kallesu d’aya bayan d’aya sannan ya bud’e baki ya fara magana

“A gaskiya bazan cuceku bah, saboda d’an babban gida kaman wannan bai kamata na rufeshi bah”

Shiru yayi na wasu lokuta, Alhaji tanimu yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button