SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Mallan muna jinka”

Abinda Mallan ya fadane yasa ni Ummy Abduol na mik’e dasauri har saida Wayata ta fadi garin fargana

A Gaskiya banine uban Sulthana bah, Sulthana shegiya ce batada Ubah

Tabdi Jam!…

Kuyi Managing wannan

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

   *DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

     *Page 151 to 155*

“A gaskiya banine uban Sulthana bah, Sulthana shegiya ce batada ubah”

Mikewa Yasir yayi dasauri yana nuna Mallan da Yatsa

“Mallan k’iyayar da kakema y’arka har takai haka? Kace bakai ka haifeta bah”

Alhaji tanimu ya had’e rai yana k’allan Yasir

“Wanne irin rashin hankali neh wannan? Wayasa bakinka a maganan nan”

Zama Yasir yayi yana huci ranshi bace. Alhaji tanimu ya maida dubansa ga Mallan fuskanshi bah walwala

“Tho Mallan tunda kace bakai baneh ka haifeta, tho ina mahaifinta yake”

Mallan ya yatsine fuska

“Bansan inda Mahaifinta yake bah, kawai dai ni rik’onta nake”

Mikewa Alhaji ilyasu yayi, Alhaji tanimu ma ya mik’e yana cewa

“Mun gode Mallan mu zamu tafi”

Baice musu komai bah suka kakkabe babban rigansu suka shigaa mota Yasir yajasu suka bar kauyen kowa ransh b’ace..

Yanmacin ranar Sulthana tadau gyadanta kamar yanda ta saba, Bakin tasha ta nufa ko kamin ta k’arasa ta hango motar Masroor pake a inda suka saba zama, da sauri ta k’arasa tana murmushi. Ta mirrown motan ya hangota zuwa ya fito dasauri ya nufeta yana huci

“Dama labarinda kika fadamin duk k’arya neh Sulthana? Ke ashe shegiya ce bakida uba”

Trayn kanta neh ya fadi ta k’walallo ido tana kallanshi da Mamaki, cigaba yayi da Magana cikin kakkausan Murya

“Kin cuceni Sulthana, dama duk abinda kika fadamin k’arya neh? Duk sanda nake miki? Duk lokacinda na bata akanki”

Tsugunawa Sulthana tai ta fasa ihu tareda daura hannu aka

“Yaya Masroor waya fadama wannan maganan? Wallahi k’arya neh Baffa shine Babana”

Ranshi b’ace ya juya Mata baya
“Shi Baffan zai miki Karya neh? Haba Sulthana Kinsa Mahaifina dani munji kunya, why Sulthana why?? Nasan baki sani bah Mahaifina neh Gwamna mai ci yanzu Alhaji Aminu”

Dagowa tayi da Mamaki tana K’allanshi

“Danasan Abinda zai faru knan daban bari Aminan mahaifina sunzo bah. Yanzu da wani ido zan kalli Daddy nah?”

Kuka sosai Sulthana take Hankalinta tashe

“Dan Allaha yaya Masroor karka gujeni, kai kad’ai ke sona kake tausaya min. Idan ka tafi ya zanyi”

Tsugunawa Yayi kusada ita zuciya na cinshi

“Sulthana Bazan iya bah”

Bai jira mai zatace bah ya shiga mota ya bar wajan a guje. Kuka ta k’ara fashewa dashi kamar ranta xai fita, hakanan ta d’au trayn gyadan ta nufo gida tana cigaba da kuka.

Zaure ta zauna ta cigaba da kukanta, saida tai mai tsarta Sannan ta mik’e rai bace ta shiga cikin gidan. Zaune ta samu duka y’an gidan a k’atuwar tabarma da Alama iska suk’e sha. Karasawa tai ta aje trayn a gaban Baffa ta tsugunna akan tabarman k’anta a kasa ta fara magana

“Baffa mai nai maka ka tsaneni baka sona? Idan na maka laifi neh kai hakuri. Meyasa kace bakai ka haifeni bah”

Da mamaki Mama ta k’alli Mallan Gabanta na faduwa

“Mallan Abinda Sulthana ta fada Gaskiya neh”

Tsaki yayi tareda kauda kai

“Hakaneh mana, bazai yuwu bah ace d’an gwamna guda yazo neman aurenta batareda na fadamai abinda ke faruwa bah. Tho yau ku shaida zan amayar da Abinda yake cikina”

Hafsatu ta mik’e dasauri tareda dafe k’irji

“Dan gwamna”

Daga kai Mallan yayi yana k’allan Hafsatu

“Kwarai kuwa”

Hankalin Ameenatu neh ya tashi tace

“Baffa muna jinka me kace zaka fada”

Sulthana ya nuna da Hannu yana cewa

“Sulthana bah y’ata bace, Shegiya ce batada uba. Cikin Shege uwarta tai ta haifeta”

Ihu Sulthana ta saki ta mik’e Dasauri ta daura hannu a kai ta fashe da kuka, rasa inda zatasa kanta tai ta dawo gaban Mallan ta tsugunna tana kuka sosai

“Baffa kai hakuri karka ce haka, ni yarinyanka ce haka Umma tace”

Tsaki yayi

“Karya umman naki takeyi, niba ubanki baneh”

Mutuwar Zaune Mama tai itada Ameenatu, Hafsatu ko cewa take

“Ashe gado tai, shiyasa itama take bin maza. Lallai gwara Baffa daka fadamana”

Kamar mahaukaciya Sulthana ta zama a cikin gidan, ihu kawai take tana kuka kwi kwi. Mama tai k’arfin Halin cewa

“Tunda nake ko a tarihan da mahaifana suka bani ban tabajin inda Uba yakema Y’arshi hakaba sai kai. Kaicona da aurenka Mallan”

Mik’ewa Mallan yayi yana huci

“Ni kike jifa da irin Wadannan Kalaman?”

Kauda kai Mama tai Ranta bace. Baffa ya dakama Sulthana Tsawa yanacewa

“Tunda abin naki ya zama haka maza ki tattara inaki inaki ki tafi ki nemi ubanki. Kada ki kuskura na fito daki na ganki a cikin gidan nan”

K’ara rushewa da kuka Sulthana tai ta rungume Mama tan kuka kamar ranta zai fita

“Dan Allah mama kice Baffa yayi Haquri ni y’arshi neh. Kadaya koreni dan Allah, wayyo Allah na”

Ameenatu ta rarrafo inda sulthana take rungume da Mama itama tana hawaye

“Kiyi haquri Sulthana, Baffa shine Babanki. Kada…”

Muryan Baffa dataji a kanta neh ya hanata k’arasa Maganan datai niya

“Kul! Karna k’araji Sam bah y’ata bace. Maza ki tattara ki bar min gida”

Dorinan daya fito dashi ya d’aga Sulthana na gani ta mik’e dasauri ta fice Zuwa zaure da gudu tana cigaba da kuka..

Mama ta shiga Dak’inta tadauko Mayafinta tana cewa

“Allah wadaranka Mallan, bazan iya cigaba da zama dakai a gidan nan bah”

Takalmanta tasa ta fice daga gidan tana kuka…

Gudu sosai Masroor yake yana kuka kamar K’aramin Yaro. Gidan da suk’a baro ya nufa wanda yanzu shine gidanshi, yana shiga ko k’wakwaran Parking beyi bah yahau hada kayanshi a Trolley yana cigaba da kuka. Waya yama Yasir akan su Hadu a Airport, dama Tun kwana biyu da suka wuce visan shi ya fito. Yana gamawa ya fitoda Akwatin yasa a mota ya kulle gidan ya nufi Airport..

Yana zuwa Yasir na K’arasowa, fitowa yayi daga nashi motan ya dauko Akwatinshi ya k’araso inda Yasir ke tsaye yana k’allanshi da Mamaki

“Friend meye haka?”

Hawayen idonshi ya share yana kallan Yasir

“Sulthana betrayed me, bazan iya cigaba da zama a k’asan nan bah.”

Hannunshi Yasir ya kamo Cikin sigan Lallashi

“No Friend, Ni inaji a Jikina Sulthana nata yaudareka bah. She’s young and batada wani ilimin da zata fadama K’arya, think of dis”

Girgiza kai Masroor yayi hawaye na gangara a idonshi

“I love her so very much Yasir, meyasa zatamin haka? Ni nasan Mutumin nan bazai mata k’arya bah”

Hannunshi Yasir yaja

“Pls Friend be strong muje gida mu tattauna”

Kai Masroor ya girgiza, duk yanda Yasir yaso Masroor ya hak’ura fafur yak’i yarda dole hakanan ya hakura ya barshi yahau jirgi zuwa lagos shi kuma ya tuk’a motar masroor din ya nufi government house jiki a sanyaye

Bayan dogon bincike Aka bari ya shiga gidan, nan ma kamin ya samu ganin Mami sai da akayi bincike Sosai Falonta datake ganin bak’i aka kaishi. Jin Yasir neh yasa batad’au wani lokaci bah ta shigo falon tana fara’a

“Idonka knan Yasir, tun bayan election ban k’ara ganinka bah”

Duk’ar dakai yayi fuskanshi bah Annuri, ganin haka yasa Mami ta zauna a sanyaye

“Yasir meke faruwa?”

Labarta mata duk yanda sukai da Masroor yayi cikeda damuwa. Mami ta girgiza kai rai bace

“Lallai Masroor ka kyalleshi ai dai ba’achan zai xauna kwatakwata bah koh? Zai dawo ya sameni”

D’agowa Yasir yayi

“Mami Masroor nasan yarinyan nan sosai, ni ina tunanin tsabar k’iyaiya ce kawai da Mahaifinta yake mata yasa yace haka”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button