SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Jim Mami tai alamar tunani Sannan tace

“Nima ina tunanin haka saidai bah yanzu zamu tunkari Alhaji da maganan bah dan yanzu yayi fushi”

Yasir ya gyada kai ya mik’e tsaye tareda mik’a mata keyn motan Masroor. Amsa tai tamai godiya yabar gidan…

Kuka sosai Sulthana take tana gudu batareda tasan inda zata bah, gashi gari ya fara duhu dan anata kiraye kirayen Sallan Magriba. Bata farga bah Ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya sam bata lura da hadari bah. Cigaba tai da gudun lokaci lokaci tanasa bayan hannunta na hagu tana share hawayen Fuskanta. Hasken Fitilan motane ya haskata ko kamin tai wani yunkuri tuni motar tai ciki da ita ta fadi k’asa sumammiya…

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

   _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

     *Page 156 to 160*

   Dedicated dis page to *Hadiza Ya'u* best fan.. Allah ya bar zumunci

Hasken fitilan motane ya haskata ko kamin tai wani yunk’uro tuni tayi ciki da ita ta fadi K’asa sumammiya. Dasauri ya fito daga motan hankalinshi tashe, Ganin wanda ke wajan yayi baya da sauri da Alamar mamaki. Nunata ya soma y bakinshi na rawa yace

“Su..Sulthana”

A hankali ya k’arasa inda take kwance ya d’auketa yasata a mota ya figi motan xuwa babban Asibiti dake cikin garin Kano inda yake aiki. Shi da kanshi ya shiga bata taimakon gaggawa duk da yanayi jikinshi na rawa zuciyarshi na bugawa, saida numfashinta ya daidaita sannan ya fita zuwa gidanshi kamin ta farka lokacin wuraren k’arfe goma na dare..

Sallah yayi Sannan yayi wanka duk hankalinshi na wajan Sulthana, wayanshi ya jawo ya soma neman layin Sa’ood yakoyi Sa’a yana fara ringing ya d’aga

“Aboki ya Akaine?” cewar Sa’ood

Murmushi Dr Fareed yayi suka gaisa sannan ya zaiyanamai abinda ke faruwa. Shiru Sa’ood yayi nad’an wani lokaci Sannan yace

“Yanzu abinda za’ayi gobe mu hadu a asibitin da safe lokacin ta farka sai mu tattauna”

Tho Fareed yace tareda mai godiya ya kashe kiran. Keyn motanshi ya d’auka ya rufe gidan ya koma asibiti, har yanzu bacci take. kujera yaja ya zauna kusada gadon datake kwance. K’allanta yake yana murmushi, hannunta na dama ya saka cikin mashi yana murzawa a hankali, a haka barci ya d’aukeshi ya d’aura kanshi gefen gadon..

Masroor na Sauka Lagos Airport, taxi ya shiga ya kaishi hotel dinda zai kwana. Yini yayi bah walwala koh abinci ya k’asa ci. Zuciyarshi Sunan Sulthana kawai take kira, Wayanshi ya janyo ya kunna sannan yasata a Fight mode dan baisan a nemeshi. Pictures d’in wayanshi ya shiga, hoton Sulthana ya dubo wanda ita batamasan an d’auka bah tana xaune tana murmushi da alama Gyada akazo siya

Shafa hotan ya soma yi hawaye cike a idonshi

“I love uh my beauty, meyasa kikamin k’arya”

Hawayen dake mak’alle a idonshi suka gangaro ya share tareda mik’ewa ya shiga toilet don watsa ruwa..

Sulthana bata farka bah sao wuraren k’arfe bakwai da rabi na safe. Firgigita ta mik’e zaune, bin dakin da Kallo ta soma yi cikeda mamaki. Ganin kan mutum kusa da ita yasata kwace hannunta tareda sakin ihu, tana k’okarin sauka daga kan gadon..

Farkawa Fareed yayi ya mik’e yana k’allanta da Murmushi

“Meya faru? Y are you shouting”

Drip din hannunta take kici kicin Cirewa tana k’allanshi a tsorace, rik’e hannunta yayi dasauri ganin tana kokarin jima kanta ciwo

“Me kike kokarin yi, ki kwanta bakida lapia neh”

Girgiza mai kai tayo hawaye na fita a idonta dak’yar da budi baki tace

“Ni ka ciremin wannan abin na tafi, ina neh nan? Waya kawoni”

Jin tashin Magana yasa Wata nurse ta shigo dak’in ganin dr Fareed yasa ta koma dasauri tana cewa

“Sorry sir”

Baice komai bah ya maida dubanshi ga Sulthana dake kuka a hankali

“Jiya da Daddare na bigeki a mota shine na kawoki asibiti, ina zaki da daddaren nan Sulthana”

Sai a Sannan ta tuna koran da Baffa ya mata, wani sabon kukane yazo mata, ta kauda kai gefe tana kuka kamar ranta zai fita. Runtse idonshi yayi ya naushi Iska ya fice daga Dak’in, Nurse dinda ta leko yama magana akan karta bari ta fita Sannan ya fita zuwa haraban asibitin. Motarshi ya hau ya figeta yabar Asibitin

Gidanshi ya nufa saida yayi wanka sannan ya k’arya duk abinda yakeyi jikinshi a mace yake. Wayan Sa’ood ya kira yace su hadu k’arfe tara a asibiti. Yana gama wayan yad’au keyn motarshi ya fice. Gidansu ya nufa batareda dogon bincikeba saboda securitys din sun sanshi aka barshi ya shiga gidan..

Mottoci ya gani kusan guda biyar a haraban gidan cikin shiri, da wasu mata dake gefe da Alama Umma suk’e jira. Side din Umman ya nufa kai tsaye dan yasan yanzu Abba ya fita zuwa Office, Bai sameta ta falo bah sai ma’aikata daketa gyara Falon. Benen dake falon ya hau a nan suk’ai kicibus da ita cikin shiri da Alama fita zatayi

“Good Morning Umma” yace kanshi a k’asa

Tsayawa tai chak sannan tace

“Morning”

Jin tayi shiru yasa yad’an dago suka hada ido

“Fareed Meke damunka?”

Wayancewa yayi

“Babu komai me kika gani”

Hannunshi ta kama suka sauko k’asa. Ma’aikatan na ganin haka sukabar falon dasauri, zaunar dashi tai kan 1seater itama ta zauna ana kusa dashi

“Fadamin meke damunka? Bah haka ka saba zuwa bah”

D’an murmushi yayi

“Bbu komai Ummah i’m fine bah abinda ke damuna.”

Bayaso ta cigaba da tambayatan shi dan haka yace

“Ummah inace ke ake jira a waje”

Mik’ewa tai dasauri

“Eh wallahi, zamuje mu hadu da Matar governor zamuje wani meeting neh”

Kai ya gyada yana y’ar murmushi

“Allah ya tsare, kice ina nan zuwa na gaidata”

Hararanshi tai cikin sigan wasa

“Ni y’ar aikenka ce?”

Dariya yayi k’asa kasa yana shafa sumar kanshi
Sallama tamai ta fita. Shima mik’ewa yayi shima yabar gidan.

Saida ya tsaya yasai mata abinci mai rai da lafiya sannan ya koma asibitin. Patient ya gani burjik sunata jiranshi, saida ya tsaya suka gaggaisa sannan ya nufi dakin da Sulthana take kai tsaye.

Zaune ya sameta kan gado ta hada kai da guiwa tayi shiru. A hankali ya k’arasa kusada gadon yaja kujera ya zauna, zabura tai ta d’ago idanunta da suka runne tana k’allanshi. Harta bud’e baki zatai magana kuka yazo mata ta k’auda kai gefe tana kukan a hankali..

Runtse ido yayi ya bud’e tareda aje mata abincin a kusada ita

“Kici abinci sai kisha magani barin duba patients”

Bai jira mai zatace bah ya bar office din. Kamar yanda suk’ai da Sa’ood k’arfe tara ya k’araso Asibitin lokacin ya gama duba patients dinshi. Fareed ne yama Sa’ood jagora zuwa dak’in, yanda ya barta haka ya dawo ya sameta bata taba abincin bah. Nunama Sa’ood kujera yayi ya zauna shi kuma ya tsaya a tsaye.

Sa’ood ya nisa yace

“Sulthana!”

Kai ta d’ago ta kalleshi shi kuma ya cigaba da cewa

“Ki kwantar da hankalinki bazamu cutar dake bah”

Fareed ya nuna da hannu yana cewa

“Nasan kinsan wannan, ki fadamin meya fito dake jiya da daddare har ya bigeki da mota”

Hawaye ya cika mata ido ta k’auda kai gefe murya chan k’asa tace

“Bah komai”

Murmushin takaici Fareed yayi tana girgiza kai. Sa’ood ya cigaba da cewa

“Karki boyemana komai Sulthana, munsan halin da kike ciki keda Baffanki so ki fada mana meke faruwa? dukanki yayi ko meh?”

D’agowa tai ta kalleshi da mamaki. Murmushi Sa’ood yayi dan ya gane k’allan datake mai

“Kina mamakin y’anda akai muka sani koh?”

Kuka ta saki tana cewa

“Baffa ne ya koreni daga gida yace bashine babana bah wai banida…”

Kukane yaci k’arfinta. Sakin baki su Fareed sukai da mamaki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button