SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Bashi ya haifeki bah?” cewar Fareed

Kai ta gyada kanta a k’asa tana cigaba da kuka. Lallashinta Sa’ood ya soma yi dakyar tai shiru, ya mik’e ya kama hannun Fareed suka bar dakin. Wata nurse Sa’ood ya samu budurwa wacce bazata wuce shekara ashirin bah da gani y’ar practical ce yasa hannu a aljihu ya ciro kudi masu tsoka ya mik’a mata

“Inaso ki kulamin da patient din dake dakin chan”

Ya nuna dakin da Sulthana ke ciki sannan ya cigaba da cewa

“Tak’i cin abinci neh inaso kisata taci abinci pls and banaso tana kuka”

Kudin ta amsa tana washe baki

“Bbu damuwa sir za’ayi kamar yanda kace”

Office din Fareed ya shiga ya sameshi zaune yayi tagumi. Sun dad’e suna tattaunawa Sannan Sa’ood ya mik’e tareda mai Sallama yabar Office din.

Saida Sulthana tai kwana hudu a Asibiti kullum tana tareda Nurse dinda Sa’ood ya barma amanarta, Sun saba sosai dan Sulthana batada wuyan sabo har tad’an saki ranta.

Kayan sawa kala kala Fareed ya saima Sulthana, sister Aisha ita ta koya mata yanda ake saka kaya da sauransu. Randa ta cik’a kwana shidda aka sallamesu a nan neh hankalin Fareed ya tashi dan baisan inda zai nufa da Itabah..

 *wai ina labarin Masroor neh?*

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

   _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

     *Page 161 to 165*

Randa ta cika kwana shidda aka sallamesu a nan neh hankalin Fareed ya tashi dan baisan inda zai nufa da itabah. Yanke shawara kawai yayi ya kaita gidanshi dan haka ya juya akalan motarshi zuwa gidanshi…

A bangaren Masroor kuwa kwanashi Biyu a Lagos sannan jirginsu ta d’aga zuwa k’asar turkey. Karatunshi ya cigaba dukda har yanzu san Sulthana na nan mak’ale a zuciyarshi. Mami da Daddy sun kirashi sun mai fada sosai akan rashin Sallamasu da baiyi bah, kullum yakan zauna yayita tunanin Sulthana gani yake kamar bai mata adalci bah daya taho ya barta batareda ya mata Sallama bah.

Yau ya kama sunday yana zaune a gidanshi bayan ya dawo daga supermarket. Waya ya d’auka ya soma neman layin Yasir, bugu d’aya ya dauka suka gaisa. Shiru Masroor yayi nad’an seconds sannan yace

“Alfarma nake nema Yasir”

Batareda bata lokaci bah Yasir yace

“Ok babu damuwa”

Ajiyan zuciya Masroor yayi sannan yace

“Dan Allah Yasir inaso neh kaje min wajan Sulthana, she’s always on my mind. Kullum zuciyana bugawa yake gani nake kamar wani abu ya faru da ita”

Saurin katseshi Yasir yayi da cewa

“No stop saying that, babu komai insha Allah”

Runtse ido Masroor yayi sannan ya bud’e, Yasir ya wuce aboki a wajanshi ya wuce Amini ya zama hamimi. Bah abinda zai iya boye mai, zaiyana mai duk yanda Sukai da Fareed yayi hankalinshi tashe..

Yasir yayi murmushi yana cewa

“Oh friend wani tabbaci kake dashi akan cewa Sulthana ce”

“Naji a jikina itace Yasir, idan har Fareed santa yakeyi bansan yanda zanyi bah I cn’t live witout Beauty”

“Ka kauda wannan tunanin a ranka pls”

Kai Masroor ya gyada kamar yana ganinshi

“Shiknan sai na jika”

Sallama sukai tareda kashe kiran..

A kauye kuwa Mama na fita Ameenatu ta bita a guje tana kuka bako hijabi, hannun Mama ta rik’e

“Dan Allah Mama karki tafi, idan kika tafi dawa zamu zauna”

Kuka itama Maman keyi

“Ameenatu bazan zauna bah, duba fah abinda Mallan yayi yanzu kina kallo, wannan wanne irin k’iyaiya neh?”

Ameenatu ta share hawayen idonta da bayan hannu

“Kiyi haquri Mama karki tafi dan Allah, nasan Sulthana batai nisa bah zan dubota nidai ki koma gida”

Hannunta ta kama suka koma cikin gidan, dakinsu ta shiga ta samu hafsatu zaune kan gado tana nunke kaya

“Hafsatu komenene ya faru Sulthana K’anwarmu ce, kada ki daka ta baffa dan abinda ya fada bah gaskiya bneh. Ki natsu kiyi tunani kada rud’in duniya ta kwasheki, ranar danasani nake gudan miki Hafsatu, ranar da batada wani anfani”

Dagowa Hafsatu tai tana K’allan Ameenatu fuskanta bah walwala da Alama magananta ya fara tasiri. Ameenatu ta zauna kusada ita ta rik’o hannun hafsatu tana hawaye

“Hafsatu ke k’anwata ce kamar yanda Sulthana take kanwata. Haka kema Sulthana kanwarki ce, bai kamata muk’i yar uwarmu bah jinnin mu ce ki tuna”

Hawayen idonta ta share tana jan magina

“Kinyi karatun Addini daidai gwargwado akwai hadisi da manzo Allah tsira da Aminincin Allah su tabbata a gareshi yake cewa imanin d’ayanku baya cika har sai kasowa d’an uwanka abinda kakd soma kanka. Kiyi tunani cikinmu bah wanda yakeso ya kasance cikin rayuwar da Sulthana take ciki bama muba har y’ayanmu”

Hawaye ne suka gangaro daga idon Hafsatu

“Haka neh ya Ameenatu, tho menene dalilin Baffa na cewa Sulthana bah y’arshi bace”

Girgiza kai Ameenatu tayi

“Ki cire wannan Maganan a ranki, bah gaskiya baneh wannan”

Hafsatu ta mik’e tana share hawayen Fuskanta

“Yaya Ameenatu yanzu ya zamuyi? Gashi Baffa ya koreta”

Itama ta mik’e tana cewa

“Zamu fita neh nemanta ta dawo gida mu zauna mu nunama Baffa rashin Amincewan mu akan abinda yake mata”

D’aukan Hijabi hafsatu tai suk’a fito tsakar gidan, a nan suka samu Mama zaune tayi tagumi, basuxe komai bah suka fita suka soma nemanta.

Duk inda suke tunani Sulthana zatace bah inda basu jeba anma duk maganar d’aya ce batazo bah. Hankalinsu bah k’aramin tashi yayi bah, koda Suka samu Mallan sani Aminin baffa da maganan bah K’aramin Mamaki yayi dajin abinda Baffa Yayi bah.

Sadiya sai kuka take jin k’awarta ta bata, haka ma Mamanta ta shiga Cikin tashin hankali sosai. Ganin hadarin dake garin yasa suka dawo gida duk’ansu jikinsu a sanyaye. Tun daga nesa suke hango Almajirai tsaitsaye a kofar gidansu, dasauri suk’a karasa aka matsa musu suka shiga cikin gidan. Nan ma mutane suka gani zagaye, Hafsatu ce ta k’usa ganin Baffa tayi kwance kan tabarma yana numfashi Sama sama Mama na kusa dashi tana kuka..

Hankali tashe Hafsatu ta shiga tambayan meya faru, Mama ce ta bata amsa da cewa

“Wai a bakin Masallaci ya fadi shine aka kawoshi gida”

Ameenatu ta k’araso wajan ta tsugunna kusada Baffan itama tana hawaye

“Allah gamu gareka, idan Laifi mukai maka Allah ka gafarce mu. Mun tuba, Mun tuba..”

Kuka take sosai tana k’allan Baffa dake kwance rai a hannun Allah. mutanen dake wajan kowa ya watse aka barsu su kadai sunata kuka..

Da taimakon Babban Almajirin Mallan da wasu almajirai aka shiga dashi d’akinshi saboda hadarin dake garin..

Magani aka hau yima Mallan Anma kamar ba’ayi, mallan Sani duk inda yaji Mallami sai ya nemoshi ko ya amso maganin Anma Abin dai gaba yake. Su Ameenatu da Hafsatu idan ka gansu gwanin ban tausayi, abu ya hadu musu biyu ga rashin Sulthana ga rashin Lapian Baffa…

Mallan ya koma kamar bashi bah ko magana baya iyayi, idanunshi kullum a bud’e yana k’allan sama komai saidai aimai baya iya komai… niko Ummy Abduol cewa nai Allah ya k’ara

Fareeda yayi Parking a haraban gidanshi ya d’an kalli sulthana daketa bin Gidan da Kallo

“Muje koh?”

Bah musu ta bud’e kofan motan kamar yanda taga yayi dazu ta fito shima ya fito suka nufi cikim gidan. Kofan main palour ya bud’e Ya shiga Sulthana na biye dashi, zama yayi kan Kujera ita kuma ta zauna k’asa kan Carpet ta makure tana bin Falon da Kallo cikeda kauyanci

“Meyasa kika zauna a k’asa tashi ki zauna kan kujera, ki saki jikinki ki rink’a min magana kinji”

Kai ta d’aga ta mik’e ta zauna k’an kujera tana cigaba da bin Falon da k’allo. D’an dariya yayi k’asa kasa yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button