SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Falon ya miki kyau neh?”

Murmushi tayi wanda saida dimples dinta suk’a lotsa. Kallanta ya tsaya yi ganin irin kallan dayake mata yasa ta duk’ar dakai. mik’ewa yayi yaja Trolleyn kayanta Yana cewa

“Taso na nuna miki”

Bah musu ta mik’e tabi bayanshi, wani bedroom dake hannun dama ya bud’e ya shiga juyawa yayi bai ganta bah ya lek’o ya ganta bakin kofa tsaye yace

“Shigo mana”

Zuciyanta na bugawa ta shiga dakin, wow tace a ranta dan tunda uwarta ta haifeta bata taba ganin daki mai kyau irin wannan bah. Murmushi ya mata ya kamo hannunta ya zaunar da ita kan katafaren gadon dake dakin

“Meyasa kike d’ari dari dani neh. Bazan cutar dake bah, daga yau nan neh dakinki”

Batasan lokacinda ta saki lallausan Murmushi bah har saida Fararen Hak’oranta suka baiyana

“Dagaske?”

Shima murmushin yayi dan Yaji dadin yanda tad’an saki ranta. Gani yayi kuma ta bata fuska tana k’okarin kuka, hankali tashe yace

“Menene”

Bai ankara bah ta fashe da kuka tana shesheka

“Shiknan bazan koma gidanmu bah? Meyasa Baffa baya sona. Dan Allah kaje ka bashi hakuri idan namai laifi neh, ni y’arshi ce”

Tausayi ta bashi ya zauna kusada ita tareda rik’o hannayenta

“Ki daina kuka, insha Allahu nan bada dad’ewa bah komai zai daidaita zaki koma wajan Baffanki kinji”

Kai kawai ta gyada tana cigaba da matsar k’walla. Kawar mata da damuwan yayi ta hanyar cewa

“Tashi na nuna miki yanda ake anfani da komai”

Bah musu ta mik’e tana binshi a baya, da cikin d’akin suka fara sannan suka shia toilet nan ma ya nunnuna mata suka fito zuwa sauran sauran wurare dake cikin gidan..

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

   _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

     *Page 166 to 170*

Kwanan Sulthana Uku a gidan Fareed, Kullum cikin tunanin Y’an uwanta take dakuma Masoyinta Masroor, takanyi kuka idan ta tuna koranda Baffa ya mata da kuma gudunta da Masroor yayi. Har yanzu sanshi da kewanshi na mak’alle a zuciyarta, bah lefi cikin kwana ukun sun d’an saba da Fareed yakan jata da hira duk da ba wani amsan kirki take bashi bah.

Aranan na hudun Sa’ood yazo gidan suna zaune a falo suna hira Sulthana na dak’i tana barci. Sa’ood ya nisa yace

“Magana nakeso muyi dakai Fareed”

Gyara zama Fareed yayi Sannan yace

“Ina jinka”

Sa’ood ya soma magana yana k’allan Fareed

“Zamanka da mace ku biyu bah abu baneh mai kyau, shedan ake gudu.”

Ajiyan zuciya Fareed yayi

“Gaskiya neh Sa’ood, saidai kasan Matsalan Ummah bazata taba yarda Sulthana ta zauna da ita ba kuma ma kagani yanzu bah zama take bah”

Shiru Sa’ood yayi yana tunani chan yace

“Dole mu nemi mafita dan wannan bah abu mai yuwuwa baneh”

Fareed ya d’ago yana cewa

“Ga shawara”

Sa’ood ya ce

“Ina jinka”

“Mezai hana nasata a boarding school har zuwa sanda zan sanar da Abba da ummah”

Murmushi Sa’ood yayi

“Yes haka ya kamata”

Sun aje akan ranar monday da Sassafe zasu kaita zaria academy dan mata registration..

Abubuwan sunma Yasir yawa gashi kullum sai Masroor ya kirashi akan Zuwa kauyensu Sulthana. Yau yana barin School kauyen ya nufa kai tsaye. Batareda wani d’ar bah yasamu Almajiri yace yamai Sallama da Sulthana. Almajirin yace

“Ai Sulthana ta b’ace ba’a ganta bah yanzu sati uku knan”

Hankali tashe Yasir yace

“Garin yaya?”

Almajirin ya tab’e baki yace

“Nima ban sani bah, andai ce Mallan ne ya koreta.”

Ran Yasir ba karamin Baci yayi bah yace

“Mallan din na nan”

Yaran yace

“Ai mallan bashida lapia tun ranar data bace ya fadi a bakin Masallaci har yanzu bai warke bah”

Hannu yasa a Aljihu ya ciro d’ari biyu ya mik’ama yaran yana murmushi

“Gashi abokina nagode”

Amsa yaran yayi tareda godiya shi kuma ya shiga motanshi yabar kauyen Hankali tashe. Yanzu taya zai gayama Masroor wannan mummunan labarin.

Yini yasir yayi cikeda fargaban yanda zai fadama abokin nashi wannan labarin. Yakoyi sa’a bai kirashi bah sai washe gari, da kyar ya dauka suka gaida Masroor yayi saurin cewa

“Yasir kakoje?”

Shiru Yasir yayi har saida Masroor yace

“Kana jina kuwa?”

Ajiyan zuciya Yasir ya saki yace

“Ina jinka friend, naje anma ban samu ganinta bah”

Nan da nan Masroor ya rud’e ya shiga jeromai tambayoyi

“Meyasa baka ganta bah?? Bata nan neh? Ko taje talla?? Pls Yasir yimin magana uh sound strange”

Ta maza yasir yayi ya zaiyanema Masroor duk yanda sukai da Almajirin daya samu a kofar gidansu Sulthana. Wayan dake Hannun Masroor ne ya fadi hawaye suka cika idonshi, kuka ya saki mai sauti tana kiran sunanta da k’arfi. Neighbours dinshi suka fifito suka tsaya a bakin kofan hankalinsu tashe jin yanda yake kuka da k’arfi yana fashe fashe..

Saida yayi mai isarsa sannan ya mik’e idanunshi sunyi luhu luhu ya shiga toilet yayi alwala ya soma kai kukanshi ga ubangiji oh Masroor I pity uh

Washe gari da safe Fareed da Sulthana suna kan dinning suna breakfast kamar yanda suka saba y’an kwanakin. Maganan sata a makaranta ya mata. Tayi farinciki sosai daga baya kuma ta hade rai

“Yanaga kuma kin chanza meya faru?

Rau rau tayi da ido

“Yaya Fareed yanzu shiknan bazan k’ara ganin Mama da yaya Hafsatu da yaya Ameenatu bah”

Goshinshi ya dafa

“Oh God! Sulthana ki cire wadan nan mutanen a ranki su basa sanki kece kawai kika damu dasu”

Hawayen dake makalle a idonta suka zubo tana girgiza

“Ina Sansu Yaya Fareed suma suna sona”

D’an jim yayi ya mik’e yana cewa

“Shiknan yanzu dai bansan kukan, ki shirya gobe da Sassafe zamu tafi. Idan akai hutu saiki je”

Ihu ta saki tana Y’ar Murmushi

“Nagode Ya fareed”

Kai kawai ya gyada ya bar wajan a zuciyarshi yana raya. Lallai rashin kula da gata yasa Sulthana shiru shiru dan yanzu data d’an wartsake ya hango k’iriniya da shagwaba a idanunta..

Washe gari da wuri da wuri suka tashi, da kanshi ya shirya mata kayanta a trolley da duk abinda take buk’ata. Saida ya tsaya a wani babban supermarket yayi mata sayaiyya sosai sannan suka biya ta gidansu Sa’ood ya daukeshi suka nufi zaria..

Bayan gwajinda akai mata Mallaman sukace za’asata a js1 rok’onsu Sa’ood yayi asata a js3 saboda ta girma she is 15. Hakan ko akai saida akai mata komai aka kaita hostel dinsu sannan su Fareed suka dawo gida…

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Ta bangaren Masroor kuwa
Kullum da tunanin Sulthana yake kwana dashi yake tashi, yanzu Masroor ya koma shiru shiru bashida hayaniya. Hoton Sulthana shi yazan mai tv, lokaci lokaci yakan sa Yasir yajemai Kauyensu Sulthana ko da wani labari gameda ita anma bbu. Yasir na matuk’ar tausayama abokin nashi hakama Mami dan Yasir ya sanar da ita duk abinda ke faruwa…

Sulthana taji dad’in makarantan sosai dan a ranar datazo tai k’awa mai suna Aisha ibrahim itama y’ar jahar kano ce. Yarinyar wani senator ne a gwamnatin dakaci yanzu. Y’ar gayuce sosai ga Rashin ji da Tsiwa, tasu tazo d’aya sosai da Sulthana, wajanta take koyan Abubuwa kamar karatu da sauransu..

 *Bayan shekara d'aya*

Sulthana na hango tsaye a wajan makaranta sanye da k’ayan hostel hannunta Rik’e da trolleynta, ta k’ara tsawo da cika, fatanta ya murje tayi kyau sosai. gefenta k’awarta Ayoush itama tsaye da Alama hutu akai saboda yanda dalibai keta fitowa da jakunkunan su. Hira suk’e suna dariya chan saiga wata had’adiyar mota k’irar doddge tai parking. Fareed ne ya fito daga motan sabye da Farar yadi sai baza k’amshi yake. K’arasowa inda suke tsaye yayi yana y’ar murmushi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button