SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Am sorry Queen I know i’m late”

Zaumbure baki tai ta kauda kai gefe, dariya Ayoush take k’asa kasa ta gaidashi da kanta ta saka jakan Sulthana a motar sannan ta karasa inda take tsaye

“Queen kiyi haquri mana kuje kinji”

Murmushi Sulthana taima Ayoush suka rungume juna sannan Sulthana ta shiga yaja sai kano ta dabo..

Fushi Queen dinshi keyi dashi, bah yanda beyi bah daran ranar ta rakashi yanada Dinner anma taki wai ita barci take ji. Hakanan ya hak’ura ya kira Sa’ood sukaje tare..

Masroor ne xaune cikin jirgi yau cike yake da farinciki zai dawo nigeria wajan iyayenshi. K’arfe hudu na shidda na yanma jirginsu ya dauka a kano, koda ya dauko Yasir ya gani tsaye shida Mami da Umma’n Fareed sai wasu mata dake bayanshi dukansu fuskokinsu d’auke da murmushi..

Dasauri ya k’arasa ya rungume Mami cikeda farinciki sannan ya rungume Yasir sunama Juna Dariya. D’an rusunawa k’adan yayi ya gaida Umman Fareed ta amsa fuska a sake, Mahnoor ta fito daga mota da gudu itama ta rungumeshi

“I missed uh bro”

Kanta ya shafa yana murmushi

“I missed uh too lil sis”

Yasir ya k’araso wajansu yace

“Dare yayi muje gida kwayi maganan”

Hannun Mahnoor Masroor ya kama suka shiga mottoci suka dun guma zuwa government house. A chan ma taron jama’a ya gani dan murnar dawowanshi da kuma murnar kammala karatunshi. Cikin taron harda Fareed da abokinshi Sa’ood suma sun samu halarta, anyi ciye ciye da adduo’i sannan kowa ya tafi gida..

Washe Gari dasafe Mahnoor zaune itada Masroor suna breakfast, Mahnoor tace

“Bro yaushe zamuje wajan Sulthana tunda ka dawo”

D’agowa yayi dasauri ya kalleta tareda sakin Fork din dake hannunshi..

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*

   _Mak'i Gani Ya Kauda Idonsa_

     *Page 171 to 175*
   Dedicated dis page to Aunty Nurse (Ayoush) Allah dawo min dake nigeria Lapia.

D’agowa yayi dasauri ya kalleta tareda sakin fork din dake hannunshi. Ta fama mai tsohon kumin daya dad’e a zuciyarshi baice mata komai bah ya mik’e yabar wajan. Mahnoor ta bishi da kallo cikeda Mamaki..

A kauye Mallan ciwonshi sai gaba yake kullum cikin magani anma babu abinda ya chanza. Rayuwa knan! Duk yan kudadenshi sun tafi wajan magani, Almajiranshi duk sun gudu sun tafi gida. Yanzu Mallan da iyalinsu sun zama abin tausayi Abinci ma dak’yar suke samu watarana ma haka suke kwanciya basuci komai bah. niko Ummy Abduol nace dama rayuwa haka take, yau gareka gobe ga wani. Abinda ka shuka shi zaka girba in Alkhairi ka shuka shi zaka gani, in kuma sharri neh shidin dai zaka gani

Allah kasa mufi k’arfin zuciyarmu. Ka bamu ikon aikata Alkhairi ka nisantar da zuciyarmu da Aikata sharri Ameen

Sulthana zaune a palour yana k’allo taji bud’e gate din gidan, mik’ewa tai dasauri ta fito haraban gidan dan dama shi take jira. Yana parking ta bud’e mai murfin motan tanamai Murmushi

“Ya Fareed tun dazu nake jiranka, ko ka fasa kaini yawon”

Goshinshi ya fada tareda furzar da aska

“Oh God! Queen bakya mantuwa neh?”

D’an zaro ido tayo cikeda shagwaba tace

“Yauwa nama tuna kace zaka saimin phone”

Muryan shagwaba yayi shima yace

“Tho Queen sai ki bari idan na huta”

Dariya ta kyalkyale dashi ya mik’a mata breifcase dinshi ta amsa tana tafe yaba binta a baya. Abinci mai rai da lapia ta dafamai ta jera a dinning, kallan warmers din yayi da Mamaki

“Waya kawo wadan nan abincin”

Bubuga k’afa tayi a kasa tana turo baki

“Nifah na dafa fah”

Iyeh yace cikeda mamaki

“Waya koya miki girki?”

Hannunshi ta kama ta zaunar dashi kan kujeran dinning din tana murmushi

“A school mana, ai munayin Home economics”

Gyada kai kawai yayi dai dai lokacinda ya saka loma d’aya. Ya lumshe ido ya bud’e

“Umm! Wannan ai saiya ciremin kunni”

Dariya tayi ta zauna itama ta zuba nata, saida yaci yayi nak Sannan ya mik’e yana cewa

“Bari nayi wanka na shirya sai muje”

Tsalle tayi tana dariya

“Thank uh ya Fareed dts why I love uh”

Da mamaki ya k’alleta tai saurin juyawa ta shiga dakinta tana cigaba da dariya.

Masroor neh yayi paking a kofar gidansu Yasir. Waya ya dauka ya kiranshi ya sanar dashi isowar shi, ba’adau lokaci bah ya fito yana murmushi

“Har ka gama hutawan?”

Kai kawai Masroor ya gyada ya shiga mota ya zauna, yasir na ganin haka shima ya shiga ya zauna yana k’allanshi

“Yadai friend meke faruwa?”

Batareda ya kalli yasir bah yace

“Inaso neh muje gidansu Beauty”

Yasir ya yatsine fuska

“Muje muyi meh kuma Masroor? Duk sanda naje bana samunta bata dawo bah. Pls Friend ka cire yarinyan nan a zuciyarka myb ma bata raye”

Dago jajayen idanunshi yayi ya zubama Yasir,

“Wannan wanne irin magana neh Yasir? Na cire beauty a raina fah kace??”

Runtse ido yayi ya bude

“Bazan iya bah yasir, bazan iya bah. Indai zaka rakani to idan kuma bazaka rakani bah”

Ya nunamai kofa

“Zaka iya tafiya zanje ni kadai”

Murmushin takaici Yasir yayi

“Muje”

Kunna Motan Masroor yayi suka d’au hanya..

La’asar lis suka isa kauyen, masallacin kusada gidan sukai Sallah sannan yasir yayi sallama a kofar gidan. Hafsatu ce ta fito duk tayi bak’i ta fige kamar ba ita bah, Masroor na ganinta ya had’e rai. Yasir ne yace

“Munzo neman Sulthana neh”

K’uri tama Masroor tana k’allanshi shiko gogan ya kauda kai sai cika yake yana batsewa. Sai a sannan taganesu tad’anyi Murmushin y’ake tace

“Ina wunin ku?”

Yasir ne ya amsa ita kuma ta cigaba da cewa

“Sulthana ta b’ace ba’asan inda take bah shekara d’aya knan da k’usan rabi”

Hankalin Masroor ya tashi ya juyo ya kalleta murya na rawa yace

“Dan Allah bakuji wani labarinta bah?”

Kai Hafsatu ta girgiza tana matsar kwalla

“Bah wani labari. Muma Mallan na kwance bashida lapia tun lokacin”

Yatsine fuska Masroor yayi ya juya yana cewa

“Sai anjima Allah bashi lapia”

Rufamai baya Yasir yayi suka shiga mota suka bar k’auyen..

Yawo sosai sukasha ranar itada Fareed, Sannan daga baya sukaje plazer yasai mata hadad’iyar waya k’irar iphone5. Murna wajan Sulthana ba’a magana sai tsalle take a plazern cikeda Farinciki. Biyan kudin yayi suka fito tana Murmushi mai k’ara mata kyau, saida suka shiga mota sannan ta kalleshi da fara’a

“Thank uh ya Fareed”

Kai ya gyada yace

“Keh koh Queen! Wai aina kika koyo wannan shagwaban da rashin ji haka”

Turo baki tayi ta sauke kai tana duba kwalin wayan. Baice komai bah ya tada motan suk’a d’au hanyan gida.

Masroor driving yake anma hankalinshi sam bai jikinshi, ji yake kaman ya fashe da kuka. Gabanshi ne ya soma faduwa yad’an dago ya kalli Yasir Sannan ya maida dubanshi ga Titi. Yasir ne ya taboshi tareda nunamai Motan dake gabansu yana cewa

“Wannan bah benz din dr Fareed baneh”

Wani faduwa gaban Masroor ya k’arayi ya d’ago dasauri yana k’allan motan

“Eh itace”

Murmushi Yasir yayi

“Lallai Fareed d’an duniya neh, shine rannan yacemin baida budurwa anma ji kamar wata nake gani a motan”

Faduwan gaban Masroor neh ya tsananta, wuri ya samu yayi parking yana k’allan motan Fareed har suka b’ace. Ganin halinda yake ciki yasa Yasir ya fito ya zagayo tareda bud’e kofan wajan Driver

“Fito sai nai driving”

Bah musu ya fito ya koma inda Yasir din yake suka nufi Gida..

Kwanaki nata tafiya tunanin Sulthana ya hana masroor sukuni, abin ya soma damun Mami da Daddy, daddy baida choice hakanan ya k’ara tura mutane dan neman labarin Sulthana anma bah wani bayani..

Mahnoor tayi kuka sosai jin labarin bacewan Sulthana saboda yanda take santa. Abin Masroor sai gaba yake hankalin Mami da daddy ya tashi sosai bama kamar Mami basatan wani abu ya faru da d’an nata..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button