SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yau Sulthana na cikin farinciki saboda yau bestynta Ayoush zatazo, har Mamaki Fareed yake yanda yaga taketa b’are b’are. Girki kala kala ta hada don taran k’awar nata. Wuraren k’arfe hudu da rabi Sulthana na dak’i kan dadduma bayan ta idar da Sallah taji horn din mota, zumbur ta mik’e ta fito a guje. Fareed ta wuce dake falo zaune yana kallan news ta fita tsakar gidan, dai dai lokacinda Ayoush ta fito d’aga motansu ta fara knocking gate din gidan..

Sulthana na bud’ewa suka rungume juna suna dariya, Ayoush ce ta fara cewa

“I missed uh besty”

Dariya Sulthana tayi tace

“I miss uh 2”

Hannun Ayoush ta kama suka shiga cikin gidan, a falo suka samu Fareed yana k’allo Ayoush tad’an rusunna ta gaidashi ya amsa fuska a sake Sannan suka shiga dakin Sulthana. Ciye ciye sukai kala kala, Sannan Suk’a barke da hira.. Ayoush ta d’ade a gidansu Sulthana, sunyi exchanging phone number Ayoush ta tafi cikeda kewan k’awar nata da kuma mamakin ganin bah kowa a gidan sai Fareed da Sulthana..

A kauye kuwa ciwon Mallan neh ya tashi gadan gadan, Hafsatu ta fito a guje ta nufi gidan Mallan sani aminin Baffa tana kuka sosai. A tsakar gida ta sameshi yana cin abincin rana, ta k’arasa inda yake zaune ta tsugunna tana sheshekan kuka

“Baba dan Allah kazo ciwon Baffa neh ya tashi”

Maman sadiya dake gefe ta tab’e baki tareda kauda kai dan ita ta tsani Baffa saboda wulakancin da yayima Sulthana. Rufe abincin Baba yayi ya mik’e ya wankr hannu yana k’okarin sa takalmi

Mama tace

“Ina zaka Mallan baka gama cin abinci bah?”

Yad’an waigo yana cewa

“Barinje na gani yanzu zan dawo”

Batace komai bah anma ranta a b’ace yake, tare suka fito da Hafsatu tana tafe yana binta a baya har gidan…

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*



     *Page 176 to 180*


        Na sadaukar da wannan page ga parrots din Deejatou novels grp *Deejatou, Fateema Ashemi, Meela adeel, Nafeesah Hasheer n Zee naseer*

Batace komai bah anma ranta a b’ace yake, tare suka fito da Hafsatu tana tafe yana binta a baya har gidan. Ameenatu ce a tsakar gidan tsugunne tanata kuka ganin Mallan sani yasa ta mik’e dasauri ta k’araso wajanshi tana nunamai d’akin da Baffa ke ciki. Dakin ya shiga ya tarar dashi kwance yana tari sosai idanunshi sun kakkafe, gefenshi Mamace itama kukan take..

Addu’a mallan sani ya soma tofama Baffa shima hankalinshi tashe. Ameenatu da Hafsatu na tsaye daga bak’in kofan cirko cirko suna hawaye sukaji Sallama a k’ofar gida, hafsatu ce ta fita. Wani mutumi ta gani tsaye sanye da Bak’ar jallabiya yana rik’e da qurani a hannunshi na dama, dayan hannun kuma ya rataya jakar fata..

Gaidashi tayi ya amsa yana cewa

“Naji labarin tashin lafiyan Mai gidan nan shine nazo na gwada sa’ata da wani magani ko Allah zaisa a dace”

Shigo kawai tace mai tamai jagora har cikin d’akin, har yanzu Tarin yake idanunshi a kakkafe. Zabura Mutumin yayi yana k’allan Baffa da mamaki, jikinshi ne yayi sanyi ya k’alli Mama yace wannan bah komai baneh face jinnu kuma insha Allahu zai samu lapia..

Mallan sani ya k’alla yace

“Ka rike min shi namai karatu insha Allahu za’a dace”

Rik’eshi Mallan sani yayi shi kuma mutumin ya soma karatu, nan da nan Mallan jamilu ya soma ihu tana bank’are bank’are tareda buge buge, Mama ita ta rik’eshi ana cigaba da mai karatun. Ganin su biyu bazasu iyaba yasa Mama ta kwalama su Ameenatu kira, duk suka taru suka rik’eshi Mutumin na cigaba da karatu..

Chan Mallan ya soma magana cikin wata murya da batasa bah

“Kayi hakuri karka konamu, zamu fita daga jikinshi”

Mutum ya tsagaita yace

“Meyasa kuka shiga jikin bawan Allahn nan kuna Azabtar dashi”

Wata murya ce ta soma magana tana cewa

“Mutumin nan bah Allah a ranshi, yana wulakanta ma d’an sarkin mu wacce yakeso shine mukazo mud’au fansa shima ya d’andana”

Mutumin yace

“Wacecce wace d’an sarkinki keso”

Wata muryan tace

“Sarauniya Sulthana”

Duka y’an dakin suk’a kwalalo ido suna kallan juna. Cigaba da magana sukai

“Kayi hakuri karka k’onamu zamu fita”

Mallamin yace

“Ku fita daga jikinshi kuma ta hanci nakeso ku fita. Karku k’ara dawowa idan har kuka dawo saina k’onaku”

Yana gama fadi Baffa yayi Atishawa sau uku sannan ya sulalle Barci mai nauyi ya daukeshi harda munshari. Mallamin ya share zufan daya k’aryo mai yace

“Alhamdulillah sun fita yanzu zan baku magunguna da hayaki da za’a rinka mai da kuma wasu Adduo’i”

Godiya su Mama suka hau mai baice komai bah ya bud’e jakar fatanshi ya ciro wasu magunguna ya mik’ama Mama tareda fada mata duk yanda ake anfani dasu sannan ya mik’a mata wata takarda wacce take kunshe da Adduo’i..

Godiya sukamai sosai baice komai bah ya mik’e hawaye suka gangaro mai a fuska. Mallan sani ya k’alleshi da Mamaki

“Lapia mallan meke faruwa?”

Hawayen idonshi ya share yace

“Idan yaji sauk’i inasan Magana dashi, akwai wani magana mai mahinmanci danakeso mu tattauna”

K’allan kallo suka hau yi yan dakin, mallamin ya musu Sallama ya bar gidan yana cigaba da hawaye…

Saura sati biyu su Sulthana su koma makaranta su shiga Ss1, yau Tana falo zaune tana k’allo lokacin Fareed na Asibiti. Masroor ne ya fado mata a rai ta runtse ido ta bud’e hawaye suka gangaro mata muryanta na rawa tace

“I miss uh ya Masroor”

Wayanta ne ya soma ringing ko ba’a fada mataba tasan Besty ce ta d’auka da fara’a tace

“Besty ya dai yau saura two weeks mu koma skul muma mu zama daga cikin seniors din nan”

D’an dariya Ayoush tai

“Gaskiya fah, kinsan meyasa na kiraki?”

Kai Sulthana ta girgiza sannan tace

“Aa”

Ayoush ta cigaba da magana tana cewa

“Inaso ne ki rakani muje wajan wata friend dita”

D’an jim Sulthana tai sannan tace

“Saidai ki tambayi ya Fareed anjima idan ya dawo i will flash uh sai ki kira na baki shi”

Ayoush cikeda jin dadi tace

“Ai indai ya Fareed ne banida matsala dashi”

Hira sukai k’adan daga bisani sukai Sallama. Fareed bai dawo gidan bah sai wuraren k’arfe tara na dare dan saida ya biya ya gaida Masroor dan bashi da lapia sosai…

A falo ya tarar da ita ta cika tayi fam. Yana k’allanta ya fashe da dariya hakan yasa ta k’ara kullewa ta fashe da kuka ta mik’e ta shiga daki tana cigaba da kukan, mik’ewa yayi yabi bayanta zuwa dakin, zaune ya sameta kan gado tana sheshekan kuka. Zama yayi kusada ita ya kamo hannunta ya hada da nashi cikin muryanshi mai sanyi yace

“Queen kin cika rigima, me kuma ya faru?”

Turo baki tayi ta shagwabe fuska tace

“Bah kai baneh ka fita tun safe sai yanzu ka dawo bah kuma ka barni inata jin tsoro”

Murmushi yayi har saida fararren haqoranshi suka fito yace

“I’m sorry swthrt kiyi hakuri patients ne sukamin yawa kuma na biya na gaida wani friend dina neh bashida lapia.”

Gabanta ne ya fadi tad’an dago tace

“Allah ya bashi lapia”

Ameen yace sannan ya mike yana cewa

“Kin hakura?”

Kai ta gyada tana murmushin yak’e dan tunda yace abokinshi bashida lapia taji jikinta yayi sanyi ga kuma faduwar da gabanta yakeyi..

Cikinshi ya shafa yace

“I’m hungry”

Kan tai magana wayanta yad’au ringing, batareda bata lokaci bah ta d’auka ta kara a kunne sannan ta mik’a mai tace

“Besty ce zatama magana”

Amsa yayi ita kuma ta fice daga dakin a sanyaye. Tana cikin zubamai abincin ya k’araso ya zauna kan dinning din yana k’allanta

“Wato abinda kuka shirya knan koh?”

Turo baki tayo ta kauda kai. Ajiyan xuciya ya sauke yace

“Shiknan Allah ya kaimu goben Lapia, n na fada mata karku dad’e”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button