SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Murmushi tamai tareda godiya ta mik’a mai abincinshi suka cigaba da hira..

Washe gari wuraren k’arfe sha biyu na rana Sulthana ta gama shirinta tsaf, yau batasan meyasa bah bugun zuciyarta yafi na jiya. Falo ta zauna tana jiran wayan besty, batafi minti biyar da zama bah kiran besty ya shigo wayan. Ta mik’e dasauri ta rufe gidan ta fito waje, drivern ta gaishar sannan ta shiga motan suka bar kofar gidan

Sunyi nisa Ayoush ta juyo ta kalli Sulthana tana murmushi

“Kin t’aba shiga government house?”

Kai Sulthana ta girgiza, Ayoush tace

“Chan zamu”

Zaro ido Sulthana tai da mamaki

“Wah kike dashi a government house? Tho ai ma baza’a barmu mu shiga bah”

D’an dariya Ayoush tayi k’asa k’asa tace

“Bakiga motan da muke ciki bah? Na government neh so bah wani bincike zamu shiga, tho bakima sani bah y’ar governor din ce k’awata tare mukai school. Kuma Maminta k’awar mum dita neh”

Gyada kai Sulthana take da mamaki, dai dai lokacin da suk’a karaso gidan gwamnatin. Booth dinsu aka duba sannan aka bari suka shiga, tafiya sukayi mai nisa gada gate din gidan. Sulthana ko sai raba idanu take tana k’allan cikin gidan cikeda sha’awa, wani dad’i ke ratsa ta yau gata a gidan gwamna. A d’ayan bangaren bugun zuciyarta ne ya tsananta…

A bakin wani d’ank’areren gini sukai parking, Ayoush ta bud’e marfin kofan motan ta fito, itama Sulthana ta fito tana cigaba da k’arema Gidan kallo. Hannunta Ayoush ta rik’e tana mata magana a hankali

“Ki daina k’alle kallen nan kada a raina mu”

Nan da nan ko Sulthana ta d’aure, Ayoush taja hannunta suk’a nufi wani k’ofa dake gefensu. Bodyguards neh a wajan murd’adu bak’ake, hannu Ayoush tasa a jaka ta ciro wani i.d ta nuna musu, a take suka bud’e mata kofa taja hannun Sulthana da jikinta keta rawa ganin bodyguards din..

Tangamemen Falo neh mai cik’e da kayan Alatu, wata maid ce ta fito dasauri tana musu Sannu da zuwa tareda tambayanta wanda tazo gani. Noor tace atakaice, maid din tadau wayan dake falon ta soma kira, saida ta gama Sannan ta k’allesu tace

“Bata nan taje Shopping”

Ayoush ta shafa goshinta

“Oush!”

Ta k’alli sulthana wacce ta shagala da k’allan Hadad’en Falon tace

“Gashi banida numbernta I loose her contact”

Sai a sannan Sulthana ta k’alleta tace

“Mud’an jirata idan bata dawo bah sai mu tafi”

Maid din najin haka tace

“Uh can come in”

Tafe take suna binta a baya har zuwa wani had’adden falo mai kyawun gaske. Sakin Baki Sulthana tai tana k’allan Falon, Ayoush ta zungureta tana kyafta mata ido. Nan da nan saita kanta…

Waya Ayoush ta d’auka ta soma kiran mum dinta tana d’auka tace

“Mum Noor batanan wai taje Shopping, kuma kinga banga Mami bah. D’an Allah kid’an kirata a waya dan ni banasan rainin wayan Maids din nan”

Tana gama wayan ta kashe ta kalli Sulthana fuska bah Annuri,

“Zakisa a raina mu wallahi, sai kalle kalle kikeyi”

Murmushi Sulthana tai ta duk’ar da kanta k’asa. Wata Maid ce ta shigo tace

“Follow me”

A tare suk’a mik’e suna biye da ita har zuwa wani falon, shima falon ya tsaru sosai har yafi sauran da suka baro. Wuri maid din ta nuna musu suka zazzauna, chan sai ga wata ta kawo musu kayan motsa baki ta fita..

Sunkai minti sha biyar a falon a zaune sai ga Mami ta shigo falon da sallama sanye cikin kaya na Alfarma, Gaban Sulthana ya yanke ya fadi ta k’asa dagowa ta kalli Mami. Ayoush tad’an rusunna ta gaida Mami, Itama Sulthana ta Rusunna kanta a k’asa ta gaidata. Amsawa Mami tai Fuska a sake tareda tambayanta Mutan gidan, Ayoush ta amsa da Ameen..

Tunda Mami ta shiga Hankalinta na kan Sulthana haka kawai yarinyan taji ta burgeta, ta kalli Ayoush tace

“Sai kuma gashi bata nan taje Shopping kuma kindai san Halinta idan ta fita”

Murmushi Ayoush tai

“Eh haka aka fada mana, tafiya zamuyi yanzu bt zamu dawo wata rana. Muma zauje wani guri neh”

Mami ta gyada kai tace

“Ai gwara ke akanta, ita yaushe rabonda naga ta shirya da sunan zuwa gidanku”

Murmushi kawai Ayoush tayi batace komai bah. Mami ta k’alli Sulthana tace

“Wai k’awarki bata magana neh”

Ayoush ta kalli Sulthana tana Murmushi

“Hmm Queen ai haka take”

Ayoush ta mik’e tace

“Mami zamu tafi”

Sulthana itama ta mik’e har lokacin kanta a k’asa,

“Tun yanzu?” cewar Mami

Dariya Ayoushi tayi

“Ai zamu dawo”

Mami ta mik’e tana cewa

“Tho ina zuwa”

Chan sai gata dauk’e da brown envelops guda biyu, Ayoush ta mikamawa tace

“Gashi keda k’awarki tunda tak’i sakin jiki”

Itadai Sulthana nai Murmushin dole take kanta a kasa. Godiya Ayoush taima Mami itama Sulthana murya a sanyaye tace

“Mun gode”

Mami tai Murmushi tace

“Bbu komai”

Sallama Sukai mata Suka fito suka shiga motarsu suka d’au hanyan Fita..

Suna K’okarin fita Motarsu Mahnoor ta shigo gidan, sam su Ayoush bata lura da suwa ke cikin motan bah. Itama Mahnoor din k’anta na k’asa tana chating a wayanta. Kamar ance ta d’ago ta sauke idanunta kan Motarsu Ayoush, Zaro ido tayi bakinta na rawa tana nuna motarsu Ayoush bakinta na k’okarin furta Wani abu..

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*


     *Page 181 to 185*

  _na Yank'e labarin neh saboda banasan nakai har bayan Sallah ban gama bah Ina fata zakumin afuwa. Fans naga sakonin ku dayawa ina godiya Sosai Allah ya barmu tare_

Kamar ance ta d’ago ta sauke idonta kan motarsu Ayoush, zaro ido tayi bakinta na rawa tana nuna motarsu Ayoush bakinta na k’okarin Furta

“Sul..Sulthana”

Kamin ta ankara motarsu Ayoush har yabar cikin gidan a guje..

Alhamdulillahi Baffa ya samu sauk’i sosai Mama dasu Ameenatu sai murna suke. Yau yana kishingide akan tabarma a tsakar gida Mama na mishi fiffita, duk abinda ya faru ta kwashe ta sanar ma Mallan ga mamakinta sai gani tai ya tab’e baki baice komai bah..

Sallama akai a kofar gidan, Mama ta kwallama Ameenatu kira taje chan sai gata itada wannan Mallamin. Tun kafin su k’araso Mama tace

“Ga Mallamin nan”

Tashi Mallan Yayi ya zauna duk da bai jin k’arfi, wuri Mallamin ya samu ya zauna suka gaisa da Baffa da Mama. Godiya Baffa ya soma mai yayi saurin dakatar dashi da hannu, daidai lokacin su Hafsatu suka zo suka zauna tareda gaidashi. Ya amsa fuskanshi bah walwala, Magana ya soma cikin rawar murya

“Dama nace idan kaji sauk’i zan dawo dan akwai wata muhimmiyar Magana danakeso mu tattauna dakai”

Baffa ya gyara zama su Ameenatu suna k’okarin tashi Mallamin ya dakatar dasu

“Aa ku zauna dan ku zama sheda”

Komawa sukai suka zauna, mallamin ya soma magana yana hawaye

“Ni d’an garin zamfara neh, iyayena duk yan chan neh. Mahaifina Mallami ne sananne a chan garin mu, Shekara goma sha biyar da suk’a wuce na kasance banajin magana duk abinda iyayena suka umarceni da nayi bana yi. Banida abokanai sai y’an isa marasa ji yan uwana”

Tsagaitawa yayi ya share hawayen fuskanshi Sannan ya cigaba

“Duk wani kayan maye da aka sani ina sha, muna farauta da abokanaina sannan mu kashe mutum a wajanmu bah wani abu baneh. Sacce sacce da fashi duk babu wanda bama yi munyi k’aurin suna sosai a garinmu. A haka har muka fara bin gari gari muna shiga gidajen mutane muna fashi”

Ya d’ago ya kalli Baffa wanda shima Mallamin yake Kallo ya cigaba da cewa

“Akwai wata rana da mukazo garin kano inda mukai wata mummunar fashi har muka kashe wani babban d’an siyasa a kofar wannan kauyen”

Zabura Baffa yayi ya gyara zama

“Dama ku kuka kashe Alhaji tijjani isiyaku?”

Kai Mallamin ya gyada kanshi a k’asa ya cigaba da cewa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button