SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Bayan munyi fashin da kwana biyu rannan ina kewaya wannan kauyen naganka kaida wad’ansu mutane kuna cinikin gona. Tsayawa nesa daku har kuka gama cinikin aka damk’a maka kudinka a hannu, binka na somayi har xuwa gidan danaga ka shiga Sannan na juya na tafi. A ranar da daddare na kawoma gidanka Samamme”

Duk da rashin karfin da Baffa yake dashi baisan lokacin daya mik’e tsaye bah tana nuna mallamin bakinshi na rawa

“Da..Dama kaine ka shiga gidana? Ka rusamin farincikin dake gidana??”

Kuka Mallamin ya fashe dashi yanaba Baffa yakuri, Mama tace

“Tabbas na tuna lokacin nan, a Gidan marigayiya Mahaifiyar Sulthana koh”

Girgixa kai Mallamin yayi yana cigaba da hawaye

“Bansani bah, nadai san ita wacchan kamar buxuwace”

Baffa ya rintse ido ya nunashi da Yatsa shima hawaye na fita a idonshi yace

“Kun ganshi nan shine Mahaifin Sulthana, a daren ranar aka samu cikinta”

Ameenatu ta mik’e dasauri ta dafe k’irji

“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”

Mallamin ya d’ago da Mamaki yana k’allan Baffa

“Ban ganeh meh kake nufi bah”

Baffa ya share hawayen idonshi yace

“Bayan ka kwanta da matata ta samu ciki kuma harta haihu yanz…”

Katseshi Mallamin yayi da cewa

“Wallahi tallahi ko kurani zaka bani na dafa na rantse zan dafa ban k’wanta da Matarka bah. Nadaiyi niyya ta hadani da Allah na fasa”

Baffa ya zaro ido yace

“meh kake nufi”

“Wallahi ba abinda ya shiga tsakanina da matarka wallahi”

Kuka sosai Baffa ya fashe dashi harda d’aura hannunshi aka, Mama tace

“Mallan kamana bayani yanda zamu fahimta”

Zama baffa yayi yana cigaba da kuka ya fara magana

“Kamar yanda ya fada shekaru baya da suka wuce wani barawo ya taba shigowa gidan tsohuwar matata mahaifiyar sulthana knan, ya shigo da k’atuwar bindiga ya bukaci mu bashi kudin dana saida gona. Dama na bata ta ajemin dan haka nace taje ta d’auko mai, tasata yayi a gaba har cikin d’akin barcin mu ni kuma ina falo ya kulleni harda bakina gashi ya kulle kofan ba halin dazan fita nai ihu azo a taimakemu”

Matse kwalla Baffa yayi ya cigaba dacewa

“Ban ankara bah naji maganan d’an fashin nan nacewa riba biyu yakeso ya samu ya amsa kudin ya kuma kwanta da Matata. Bansan sanda na fashe da kuka bah ina nan zaune a falon, ihunta naji tana bashi hakuri shi kuma yana dariya. Chan sai gashi da kudin a leda ya bud’e kofa ya fita, ita kuma tazo ta kwanceni tana kuka sosai”

“Bayan sati biyu da Faruwan hakan tazomin da labarin tanada ciki, tun a lokacin na fara hantaranta dan nasan bah cikina baneh”

Baffa ya fashe da kuka ya nuna Mallamin yace

“Ka cuceni, Allah ya isa tsakanina dakai.”

Mama ta matso tana kuka itama

“Kai hakuri Mallan shima ai gafaranka yazo nema”

Kuka baffa yake wuiwui

“Bah irin rantsuwar da batayi bah akan bah abinda ya shiga tsakaninku anma ban yarda bah. Ashe dagaske ne”

Ya k’ara rushewa da kuka

“Ki yafeni Rabiatu, ban miki aldarci bah naci amanar dana dauka naki. Ki yafeni”

Kuka yake sosai yana cigaba da cewa

“Kah cuceni ka rusamin farinciki, yanzu dama Sulthana y’ata ce naketa mata wannan kiyaiyar”

Zumbur ya mik’e yana k’okarin sa takalmin shi. Mama itama ta mik’e

“Ina zaka Mallan?”

Yana kuka yana cewa

“Zanje neman Sulthana ta dawo gida, ta yafeni rashin sani neh”

Mama ta rik’eshi

“Kayi hakuri Mallan Kaga bakajin dadi, kuma Sulthana shekara d’aya fa knan da rabi rabonmu da ita. Bbu wanda yasan inda take”

Dakyar ta Lallabashi ya zauna, kowa a wajan kuka kawai yake bama kamar Baffa. Yana kuka hannunshi akai

“Allah ka yafeni, Rabi ki yafeni. Sulthana ki yafeni”

Sun d’ade a haka bah wanda yake rarrashin wani har na wasu lokuta sanna Mallamin yace

“Duk inda y’arka take indai tana raye tana rayuwa ne tareda Aljani, ma’ana akwai aljani a jikinta”

Baffa baice komai bah ya mik’e ya shiga dakinshi yana cigaba da kuka. Dakyar su Ameenatu sukaba Mallamin Hakuri ya tafi…

Mami na barin Falon d’akin da Masroor ke kwance ta nufa. Ga mamakinta sai ganinshi tayi tsaye yanasa Burtin din shirt dinshi da Alama wanka yayi

Kallo d’aya zakamai kaga ramar dayayi. Dasauri ta k’araso wajan baki bud’e

“Son idona gizo yakemin ko gaske meh? Kaine a tsaye a nan”

Juyowa yayi ya rik’e kafadanta yana Murmushi

“Nine Mami, am now fine”

Mahnoor ce ta shigo dakin a rud’e tana haki, hannun Masroor ta rik’e tana nunamai Kofar fita. Sakin Hannunta yayi yana k’allanta

“Menene? Waya biyoki?”

Haki take tayi saida yad’an tsagaita tace

“Mami wallahi yanzu naga Sulthana a wata mota sun fita d’aga nan gidan kuma a motar gidansu Aisha neh”

Tun kanta k’arasa maganan Masroor ya nufi kofar fita, Mami ta rik’eshi tana girgixa mai kai

“Ina zaka kaida Bakada lapia”

Idanunshi cik’e da kwalla yana k’okarin kwace kanshi daga rikon da Mami tamai

“Mami ki kyalleni naje dan Allah I want to see her”

Kallan Mahnoor tayi fuskanta a had’e

“how sure are you itace??”

Nan Mahnoor ta fara inda inda. Masroor sai kokarin kwace Hannunshi yake ya kasa saboda jikinshi daba k’arfi. Hannunshi taja ta zaunar dashi kan gado

“Kah kwantar da Hankalinka indai itace komai yazo k’arshe tunda tare suke da Aisha”

Baice komai bah k’anshi na k’asa baisan Mami taga hawayen dake zuba a idonshi taja hannun Mahnoor suka bar dakin..

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

 DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

       *Page 186 to 190*

Baice komai bah k’anshi na k’asa baisan Mami taga hawayen dake zuba a idonshi, taja hannun Mahnoor suka bar dakin..

Sun danyi nisa da government house, Sulthana ta rik’e kanta tana k’allan Aisha

“Ayoush ku kaini gida kawai kaina wanni irin ciwo yake”

Ayoush tamatso tareda taba goshinta

“Kuma jikinki bah zafi, kanne kawai ke ciwo?”

Kai kawai Sulthana ta gyada batace Komai bah. Gida suka kaita lokacin Fareed baya nan sukai Sallama ta tafi. Falo ta shiga ta zauna kanta na mata ciwo sosai, rintse ido tayi tareda tafe kan tun daga nan bata k’ara sanin inda kanta yake bah…

Ganin halinda ake ciki yasa Mami ta d’au waya ta soma neman layin Abba, lokacin yana tsaka da aiki ya daga tareda fada mata aiki yake. Saurin katseshi tai ta fadamai dalilin bugowanta daneman izinin fita. Bai musa bah ya amince ta kashe kiran..

Aminiyarta ta kira wato matar duty governor suka nufi gidansu Ayoush tareda rakiyan bodyguards dinsu. Masroor na ganin sun fita ya dau makulin motanshi ya mara musu baya..

Tarba sosai Mum din ayoosh tai musu, saida Suka natsa sannan suka sanar da ita dalilin zuwansu. Batareda batalokaci bah tayo kiran Aisha, tafito ta tsugunna har k’asa ta gaidasu. Mami ce tafara magana tana cewa

“Aisha menene Sunan Yarinyan da kukazo tare”

D’an dagowa Aishan tai sannan tace

“Queen!”

Mami ta girgiza kai tana y’ar murmushi tace

“Sunanta na gaskiya nake magana”

Batareda bata lokaci bah tace

“Sulthana!”

Masroor dake mak’e jikin labule ya fito dasauri ya k’araso inda Aisha ke tsugunne shima ya tsugunna

“Aisha dan Allah aina take?? Fadamin pls”

Kowa dake falon mamakin ganin masroor yayi bama kaman Mami. Aisha ta kalleshi tareda sauke ajiyan zuciya

“Classmate dita ce, a nan kano suke itada brothern tah”

Saurin girgiza kai Mami tayi tana cewa

“Wannan bah Sulthanan ka bace Masroor, kaji wannan fah y’ar kano ce kuma tanada yaya”

Hannun Aisha ya kama idanunshi cikeda da kwalla

“Pls ki kaini wajanta, ni nasan Sulthana na neh.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button