SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru Ameena tai tana Muzurai, nan da nan Hafsatu ta maida bayani. Baffa ya Kalli Ameenatu da Mamaki
“Lallai Ameenatu, Wuyanki ya Isa yanka, Tho bari kiji Baki isa ki chanzamin Abinda nai niya bah. Wallahi Ameenatu ki fita idona in rufe”

Bataco komai bah kanta na Kasa, Sulthana tun fitowan baffa ta hau kiciniyar Daura ruwan, yana waigowa yaga ta daura yayi kwafa ya koma daki abinshi. Mama najin ya shiga dakinshi Ta fito tana kallan Ameenatu
“Ameenatu kisa ido kamar yanda nasa, Allah bah Azzalumin Bayinsa baneh”
Kai Ameenatu ta gyada batace komai bah
“Keh bazaki makarantan baneh” cewar Mama
“Aini jiya muka zana jarabawanmu na k’arshe”
Dafe Goshi Mama tai tana Murmushi
“Oh na manta, Tho Allah yasa An gama Makarantan a sa’a”
Ameen Ameenatu tace ta wuce dakinsu Cikeda Takaicin Abinda Baffa yakeyi..

Ruwan nayi ta sauke ta surka mata takai mata bandak’i sannan taje ta Sanar da Ita. Tana fitowa ta tsaya bak’in Kofar dakin Baffa Gabanta na bugawa cikeda Tsoro, Daurewa tayi tai sallama a bakin Kofar dakin, Fitowa Baffa Yayi yana k’allanta
“Menene”
Dan Jim Tai Jikinta na rawa
“Keh nake Saurare”
Duk’ar dakai tai sannan tace
“Dan Allah Baffa inaso na cigaba da Zuwa makaranta”
Bude Baki Baffa yayi da mamaki yana K’allanta
“Lallai na Yarda Bak’ida Kunya Sulthana, Ki Kalli tsabar Idona Kice Makaranta Kikeso ki Koma”
Jin Daga Muryan Baffa Yasa Mama dasu Ameena suka Fito
Kara Kallanta yayi rai bace
“Ki Sani Kin Gama zuwa makaranta, keda makaranta har Abada kisan wannan”
Kuka sosai Sulthana tahau yi
“Zakimin Shiru koh sainq zaneki a nan wajan”
Nan da nan ta hadiye Kukan sai hawaye datake fitarwa

Mama ta Kalli Baffa itama Rantq Bace
“Wallahi Mallan Karinka jin Tsoron Allah, Bai Kamata Masani kamarka yana irin wannan bah, Ya Za’ayi ka hanata Zuwa makaranta kuma gasu Hafsatu na zuwa”
“Saboda su yadace suje makaranta bah ita bah” cewar Baffa
Tsaki Hafsatu tai tadau kwandon Soson Wanka tai shigewanta bayi.
Murnushin takaici kawai Ameenatu tai itama ta koma dak’i, Yarone cikin Almajiran Baffa ya shigo cikin gidan dah Sallama Saida Ya Russuna Sannan yace
“Wai ana Sallama da……

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

       *Page 21 to 25*

“Wai ana Sallama da Hafsatu”
Dah mamaki Mama ta K’alli dan Aiken
“Dah Sassafen nan”
Tsaki Baffa yayi
“Ina Ruwanki, Kai jekace tana zuwa”
Hafsatu naji ta fito dasauri ta dire bokitin a Tsakar gida ta shige dak’i, A Gurguje ta shirya koh karyawa bata tsaya yi bah tayima Mama sallama Ta fice, Binta da K’allo Sulthana tai tareda girgiza kai dan Tasan bai wuce Ahmad Mayan matan nan..

Tsaye ta Sameshi a Kofar Gida sai k’ara kallan kayan jikinshi yak’e, da Fara’a ta k’arasa inda Yak’e tace
“Barka da Zuwa Habibyna”
Dan Murmushi yayi yana Cigaba da K’allanta
“Haba Hafsy nah, nifah na Lura bah sona kike bah”
Waigawa Zaure tai Sukayi ido hudu da Sulthana dake Zaune sai Kallansu tak’e, Hararanta tai Sannan ta juyo ta K’alleshi
“Mubar nan dan Gadon Gulma da munafinci na Sauraronmu”
Baice komai bah suka jera suna Tafe suna Hira har kusa da Makarantan su
“Kaima Kasan Ina Sanka Habiby, Bani dah Tamkar kah duk duniyan nan”
Murmushi yayi tareda shafa sumar kanshi dake Cike dam Bakyan Gani
“Banga Alamar Haka bah Hafsy, Dah kina sona dah kin bini Partyn dana gaya miki a Birni, Anma kin ki”
Marairaice Fuska tai Tana K’allanshi K’asa kasa
“Bah Laifi nah Baneh habiby kai kanka Kasan Halin Baffa, Mai zai hana tho ka turo gidanmu ai mana aure kaga Shiknan sai ka kaini Birni mu rinka zuwa Partyn tare koh”

Gintse dariya yayi ya gyada kai kawai
“Kaji” cewar Hafsatu data Marairaice
“Naji Hafsy but inaso na sauyaki, Ki waye ki zama yar birni Sosai, Ki koma sah kaya irin na yan birni ki fita daban cikin matan Kauyen nan. Bt Kudi neh yamin Cikas, Anma karki damu danaje birni na dawo komai zai daidaita”
murmushi jin dadi Hafsatu tai tana cigaba da K’allanshi, Harga Allah tana Matukar san Ahmad, musamman yanda ya fita daban Cikin Mazan Kauyen, Gashi dan Gayu mai zuwa birni, Gashi Kyakyawa san kowa kin Wanda Ya rasa..

Bell din makaranta Aka kada ta K’alleshi tana Yar Murnushi
“Habiby Mu hadu Anjima da Magriba a dandali”
Bata jira mai zaice bah ta shiga makaranta dasauri. Murmushin cin nasara yayi a ranshi Fadi yak’e
“Keh kina tunanin ni Ahmad Aurenki zanyi, Baridai na Samu abinda nake nema bak’i kara ganina a garin nan”..

Yauma kamar jiya Baffa dakansh ya diban mata Gyadan ta Dafa ta Fito Talla, Mutane sai kallanta suke da Mamaki dan basu taba ganin yayan Mallan jamilu da Talla bah, Bakin Kasuwa taje Yauma Anma Tai Rashin Sa’a Baifi Gwangwani hudu aka siya bah Har Gaf da Magriba, Ganin Dare na Neman Yi yasa ta dawo Gida cikeda Fargaban Abinda Baffa Zaiyi mata, Bata sameshi a gida bah Yana Wajan Almajiransa, a Kofar dakinshi ta aje Gyadar ta Shiga aikinta na Yanma..

Sai Bayan Isha’i ya Shigo Gidan dasauri, Gyadan da ta ajemai a kofar dak’i ya K’alla yayi kwafa ya Shiga Cikin Daki, Baifi Minti Goma Bah Ya Fito Dasauri Ya Shiga Dakin Mama
“Saratu! Saratu!!”
Mama data Sallame Sallah ta K’alleshi da Mamaki
“Lapia Mallan Kake Kwalamin Kira haka??”
Kin Shiga dakina neh kin dauki Kudi”
Kallanshi tai da Alamar Mamaki, “Ban ganeh Kudi bah, na Taba daukan kudinka ban fadama bah”
Bai kara cewa komai bah Ya fita daga Dak’in, Sulthana ya soma Kwalama Kira, Ta Shigo Tsakar Gidan Dasauri tareda Rusunawa
“Na’am Baffa”
Ido Ya zazzaro yana Kallanta
“Kudina Zaki bani da Kika dauka”
Mama ta Kalla dasauri sannan ta maida dubanta ga Baffan dake Tsafe ya Kafeta da Ido
“Wallahi Baffa ban dau Maka Kudi bah”
Ameenatu Dake Dak’i ita da K’awarta habiba ta fito dasauri
“Baffa Lapia”
Kudi na Ajiye a daki ko kin Gani?”
Girgiza kai tai dasauri
“Aa banga kudi bah”
Ina Hafsatu? Cewar Mama
Dan Jim Ameenatu tai Sannan Tace
“Tunda Akai Magriba ta fita Bata Dawo bah”

Dak’i Baffa Ya shiga Chan sai Gashi da Dorina katuwa mai Baki dayawa, Mama ta Kalleshi
“Meh Zakayi Mallan”
Keh! Nan da nan Jikin Sulthana yadau Rawa
“Wallahi Baffa Bandau maka kudi bah, Dan Allah kai Hakuri Karka dakeni”
Daka Mata Tsawa Yayi
“Ki Fito Min da Kudina, Oho! Wato dan nace bazan saki a makaranta bah shine kika satan min kudi dan ki koma makaranta koh”
Kuka sosai Sulthana take
“Wallahi Baffa ban dau maka kudi bah, Dan Allah Karka Dakeni.”
Hakuri Ameenatu ta soma bah Baffa anma ko Kallanta Beyi bah, Bulalan dake Hannunshi ya soma dukanta Dashi ta koina, ihu Sulthana take Tana Rokonshi Anma ina. Rike bulalan Mama tai a Fusace
“Haba Mallan, Wannan Wane irin rashin imani neh, wanne tabbaci kake dashi na cewa ita tadau maka kudi”
Huci sosai Baffa Yake
“Sakar min Bulalan nan Saratu, Yayana basa Sata, Saida Wannan Yar Iskan Yarinyan ki sakar min Bulala nace”
Bazan Saki bah, mallan Kaji Tsoron Allah”
Wani Tsawa ya saki tareda Fizge bulalan Daga Hannun Mama, Rusunawa Ameenatu tai tana Kuka tareda Rokon Baffa, Anma Ko Kallanta Beyi bah, Saida Ya duketa San Ranshi Sannan Ya Kyaleta. Kuka Sosai Sulthana take, Duk Jikinta ya Farfashe. Dakyar ta Mike Tsaye, ya Kalleta a Harzuk’e Ficemin Daga Gida Karna K’ara Ganinki a Gidan nan..

Kuka Sosai ta k’ara Fashewa dashi tana bashi Hakuri, Binta yayi da Bulalan ta Falla a guje tabar Gidan ya koma Ciki ya rufe Kofa, Yana Shiga Yaga Mama ta fito Sanye da Hijabi, Ya kalleta da Mamaki, Ina Zaki?
“Gaskiya Mallan bazan cigaba da zama a gidan nan kana Azabtar da Yarinyan nan bah Na gaji Gaskiya”
Kafada Ya daga Tareda Cewa
“Idan Har kika fita kofar gidan nan tho ki sani a bakin Aurenki”
Ameenatu da har lokacin tak’e Tsugunne a Kasa tana Kuka ta dago ta Kalleshi da Mamaki…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button