SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kai ta gyada ta mik’e tadauko gyalenta ta fito, dukansu suka dunguma zuwa gidan..

Shigowan Fareed kenan cikin gidan tun daga haraban gidan yakejin k’aran fashewan abubuwa, dagudu ya k’arasa cikin falon. Bin falon ya somayi da kallo komai a hargitse, center table a fashe abubuwa duk a fashe. Jin wani k’aran a dakinshi yasa ya nufi dakin dasauri, ganin Sulthana yayi tsaye duk gashin kanta a barbaje hannayenta na jini sai fashe fashe take tana ihu kamar bah itaba.

Jikinshi ne ya soma rawa ya k’arasa kusada ita ta daga sauran mirrown dake hannunta za wurga mai, dasauri yaja da baya mirrown ya fadi gefenshi ya fashe…

Ihu ta saki mai k’ara ta nufeshi dagudu ta rikeshi tana dukanshi tako ina. Kallanta kawai Fareed keyi jikinshi a mace hawaye na gangara daga idonshi, dakyar ya tattaro karfinshi ya rik’eta murya na rawa yace

“Queen meya sameki? Why all this”

Dukanshi kawai take a k’irji da iya karfinta. Janyota yayi dakyar zuwa falo ya zaunar da ita k’an kujera sai kokarin tashi take tana ihu da karfi..

Motocin su Mami neh suka tsaya a kofar gidan, umman Fareed ta k’alli Aisha da Mamaki

“Nan neh gidansu Yarinyar?”

Kai Aisha ta gyada sannan tace

“Nan neh nasan tanama ciki”

Da mamaki umman Fareed ta k’alli Mami tana cewa

“Nan fah gidan Fareed neh”

Dasauri Aisha tace

“Eh sunan yayanta knan”

Umman fareed ta kwalalo ido ta fito daga motan dasauri, tuni Masroor ya fito daga tashi motar yana jiran fitowansu dan ta nunamai gidan. Aisha ce ta musu jagora zuwa bakin kofar gate din. Kofar a bud’e take dan haka suka shiga gidan kai tsaye..

Ihun da sukaji neh yasa suka tsaya chak, Masroor ya saki kuka mai sauti dagudu ya shiga falon dake gidan. Sulthanan shi ya gani rungume jikin Fareed tana kuka da ihu tana kokarin ture Fareed daga jikinta

Tsugunawa Masroor yayi ya runtse idonshi yana girgiza kai bakinshi na furta

“Noo! Noo!! Sulthana”

Juyowa Fareed yayi firgice jin murya a bayanshi, dai dai nan su Mami suka shigo falon kowa na kallansu da Mamaki. Umman Fareed ta k’araso ranta b’ace

“Fareed meh nake gani haka? Ka aje yarinya a gidanka”

Baice komai bah har yanzu kuma yana rik’e da Sulthana daketa ihu tana dukanshi, kokarinta kawai ya saketa. Hawayen dake mak’alle a idanunshi suka sauka muryanshi na Rawa yace

“Umma I’m very sorry, its not what uh think. Yanzu abinda yafi shine mukaita asibiti”

Kasa cewa komai Mami tayi ta k’arasa inda Masroor ke tsugunne yana kuka kamar yaro. D’agoshi tayi tsaye tasa hannayenta tana sharemai hawaye

“Stop crying son, karka jama kanka wani ciwo”

Muryan Fareed yaji yana cewa

“Friend help me mu kamata mu kaita Asibiti”

K’ara k’allan Sulthana yayi yaga yanda take ihu da bige bige, ya rintse ido ya bude. Daky’ar suka kamata sukasa a mota suka nufo asibiti dukansu..

batareda wani bata lokaci bah aka amsheta ganin manyan mutane kuma tare da likita. Dr Sa’ood da wasu likitoci ke kanta, aluran barci sukai mata sannan suka hau mata gwaje gwaje. Sun d’au lokaci suna dubata, Fareed na tsaye har lokacin hawaye yake ya kasayin komai..

Saida suka natsa sannan Sa’ood ya kira su Mami Office dinshi. Bayan sun zauna ya soma magana

“Ur excellency duk binciken daya kamata muyi duk munyi anma bamuga komai bah. Ni sai nake gani kamar Cutar bata asibiti baneh inaga..

Saurin katseshi Umman Fareed tai da cewa

“Wanne irin magana kakeyi Sa’ood, yarinyan da kowa yagani tana abu kamar mahaukaciya zakace bana asibiti baneh”

Ajiyan zuciya ya sauke sannan ya cigaba da cewa

“Umma! Bata lokaci kawai za’ayi, a shawarce shine a nemo malami dazai mata ruk’iya”

D’an Murmushi Mami tai ta mik’e

“Mun gode doctor insha Allahu hakan za’ayi”

Office din suka fito a bakin kofa sukaga Masroor tsaye kanshi a k’asa. Hannunshi Mami ta kama ya d’ago jajayen idanunshi yana k’allanta

“Son muje gida kasha magani”

Girgiza mata kai yayi dasauri

“No Mami zan zauna tareda Sulthana”

Rungumoshi jikinta tayi tana shafa bayanshi

“I know how uh feel Son, be Strong everything wil be fine. Baga Aisha bah she wil take care of her”

Dakyar ta lallabashi suka koma gida. Sai dare suka natsa Mami ta samu Abba a dakinshi ta sanar dashi duk abinda ke faruwa. Ya cika da mamaki sosai, shi kanshi yanajin son yarinyan musamman yanda yaji batada gata. Washe gari da safe shima mutanenshi sukaje gaisheta, Maman Aisha suka samu a wurinta da Fareed..

Sun gaisheta tareda mata addua coz har lokacin bata farka bah sannan suka tafi..

K’arfe 10 na safe a Asibiti tayi mah Masroor shida Yasir, direct dakin suka shiga kai tsaye. Aisha suka samu da Fareed a dakin. Masroor baice komai bah ya nufi bakin gadon yana K’allan Sulthana tareda tambayan Aisha jikinta. Ganin Masroor baimai Magana bah yasa ya mik’a mai hannu yace

“Morning Friend”

juyowa Masroor yayi ya galla mai harara ya juya ya maida Fuskanshi ga Sulthana. Daidai lokacin idanunta suka fara rawa Masroor ya kara matsowa kusada gadon yayi kneeldown yana k’allanta da hawaye cike idonshi

“Beauty open ur eyes its me Masroor”

Bud’e idonta tai dasauri tareda mik’ewa zaune ta k’uramai ido idanunta taf da hawaye. Ganin tana neman kuka yasa ya girgiza mata kai hawaye na gangara a idonshi

“Karkiyi kuka Beauty, nine dai Masroor naki”

hawayen daya gangaro mata ta share ta t’aba hannunshi taji tabbas shine, k’ara fashewa da kuka tayi ta rungumeshi. Shima kukan yake a hankali yana shafa suman kanta..

Duk yan dakin yan K’allo suka koma, Fareed ko gabanshi ne keta faduwa zuciyarshi ta shiga masa zafi ganin yana kokarin fashewa da kuka yasa yabar dakin dasauri. Direct Office dinshi ya nufa ya zauna akan kujeranshi ya daura kai kan table ya fashe da kuka mai tsuma zuciya. Kuka yake sosai anma bah mai Lallashin shi

A haka Sa’ood ya shigo Office din ya sameshi, Zama yayi yana kallan Fareed batare dayace komai bah. Saida ya bari yayi kukan mai isarsa sannan ya mik’e ya dawo kusa dashi tareda dafashi..

“Na barka kai kukan neh saboda ka samu relief, tel me whats wrong”

Idanun Fareed taf da hawaye ya d’ago yace

“Sa’ood na rasa Sulthana, na rasata.”

Dasauri Sa’ood ya zagayo ya tsugunna yana facing dinshi dakyau

“Bangane kah rasa Sulthana bah Fareed”

Runtse ido Fareed yayi hawayen da suka makale suka zubo ya d’ago yana k’allan Sa’ood wanda shima shi yake kallo

“Friend dina Masroor yana san Sulthana, kuma kasan yanda muke dashi da kuma yanda iyayenmu suke.”

Shiru yayi yana share kwallan dake idanunshi. Sa’ood ya nisa yace

“And so what Fareed, kanasan Sulthana?”

Dagowa yayi dasauri yana k’allan Sa’ood shekeke

“I so much love her, I cnt do witout her. And banasan abinda zai kawo matsala tsakanin wannan zumuncin dake tsakanin mu”

Sa’ood yaja dogon tsaki tareda mik’ewa

“Fareed fight and get wat uh want, karka kasa wannan a ranka. Kayi kokari ka yaki har kasamu abinda kakeso ka..”

Wayan Fareed dake ringing neh ya katse shi, ganin mai kiran yasa ya d’auka tareda Sallama Sannan ya mik’e yace

“Ganinan zuwa”

K’allan Sa’ood yayi

“Zanje gida Umma na nemana”

Gyada kai kawai Sa’ood yayi sukai Sallama yabar office din.

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

  *Page 191 to 195*

Fita yayi daga Office din ya nufi motarshi dasauri direct gida yayi, saida ya shiga side dinshi dake gidan yayi wanka da Sallah sannan ya shiga side din Umma gabanshi na faduwa..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button