SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaune ya sameta itada bak’i, zama yayi kan Carpet suka gaisa da mutanen falon. Yana nan zaune har suka gama ta sallamesu Sannan yad’an duk’ar dakai murya na rawa yace

“Ina kwana Umma”

Shiru tayi tana kallanshi, jin shirun yayi yawa yasa yad’an dago suka hada ido yayi saurin maida kai kasa. Umma ta nisa ranta b’ace ta soma magana

“Fareed ina hankalinka yaje ina iliminka? Bantaba expecting haka daga gareka bah”

A hankali ya d’ago cikin sanyin murya yace

“Dan Allah Umma kiyi hakuri nasan nayi kuskure”

Ajiyan zuciya ta sauke

“Fareed kasan matsayinda mahaifinka yake kai yanzu, bai kamata haka na bullowa bah. Bakama gudun maganganun mutane kadauko yarinya ka ajeta a gidanka har na tsawan shekara”

Hawaye cike da idanunshi ya dago

“Umma kiyi hakuri d’an Allah wallahi it was’nt my fault, gani nai kamar bazaki yarda ta zauna dake bah. And yarinyan need help babanta ne ya koreta witout any serious reason”

Umma ta girgiza kai tana murmushin takaici

“Fareed uh are stil young, bazaka ganeh abinda nake nufi bah.”

Baice komai bah kanshi a kasa. Nasiha Umma ta soma mai mai ratsa jiki, Sannan tace ya tashi yaje. Godiya yayi ya mik’e ya koma side dinshi jiki a sanyaye..

A asibiti kuwa ta dad’e a jikin Masroor tana kuka mai ban tausayi daga bisani ta janye jikinta daga nashi tana kallanshi

“Ya Masroor meyasa zaka tafi ka barni, meyasa kak’i yarda dani.”

Hawayen idanunshi ya share

“Kiyi hakuri Beauty nasan nayi lefi i’m sorry”

Batace komai bah ta koma kan gadon ta kwanta ta juya mai baya. Hannunshi Yasir ya kama yajashi suka fita. Aisha ta matso kusada gadon tad’an taba ta tana cewa

“Sannu Queen ya jikin”

Tashi zaune tayi tana yatsine fuska

“Ayoush meya kawoni asibiti? Bah gida kuka kaini bah”

Murmushi Aisha ta mata

“Kin tuna kince gabanki na faduwa? To shine ya Fareed da kikayi barci ya kawoki asibiti”

Tana kokarin jeho mata wani tambayan tai saurin katseta da cewa

“Yauwa Queen inaso na tambayeki”

Gyada kai tayi tana kallanta, Aisha ta cigaba da cewa

“Aina kikasan Masroor, Sannan keh wacece coz ance ya Fareed bah brodanki baneh?”

Murmushin takaici tayi

“Zakisan duk abinda baki sani bah dnt worry, yanzu ina ya Fareed”

D’an jim tayi tace

“I donno myb yana office”

Batace komai bah ta koma ta kwanta zuciyanta a jagule..

Kwanan Sulthana biyu a asibiti, tun daga ranan da aka kwantar da ita bata k’ara ganin ya Fareed dinta bah. Masroor kuwa kullum yana tare da ita shida Aisha, haka Mahnoor tazo dubata itama. Sulthana tasha Mamaki sosai jin su y’ayan gwanma neh. Ranar da Dr Sa’ood yayi discharging dinta ta tareshi da tambayan ya Fareed baice mata komai bah yabar dakin..

K’allan Aisha tayi fuskanta bah walwala

“Aisha d’an Allah ki kaini Office din ya Fareed”

Nan da nan fara’ar dake fuskan Masroor takau ya hada girar sama data k’asa. Sulthana na ganin haka tasha jinin jikinta ta koma ta zauna. Waya ya dauka ya kira Mami ya sanar da ita sallamansu da akai, batareda bata lokaci bah tace ya d’aukota suzo gida. To yace ya kashe wayan ya kalleta fuska bah walwala

“Mami tace na daukoki muje gida”

Batace komai bah ta mik’e tadau gyalanta ta yafa Aisha ta soma hada musu kayansu. Ganin suna abu slow yasa yad’au wasu kayan ya fita yana cewa

“Ku sameni a mota”

Aisha ce ta amsa. Bayan fitanshi Sulthana ta kalli Aisha idanunta cike da hawaye

“Aisha ina Ya fareed? Meyasa yak’i zuwa inda nake? Duk wanda na tambaya shi sai yayi banza dani.”

Aisha batace komai bah ta k’ama hannunta suka fita daga dakin, Office dinshi suka nufa a kofar office din Aisha ta tsaya itakuma ta tura kofar ta shiga jikinta na rawa

Zaune ta sameshi yayi tagumi ga tulin folders a gabanshi, jiki a sanyaye ta k’arasa kusadashi ta dafa kujeran dayake kai

“Ya Fareed! Ya Fareed!!”

Zabura yayi ya juyo a tsorace yana kallanta. Ta shagwabe fuska

“Ya Fareed inata nemanka shine kaki zuwa ka dubani koh bayan kuma kaine ka kawoni”

Kirkiro murmushi yayi

“I’m sorry Queen ayuka neh sukaimin yawa”

Dawowa tayi ta zauna kan kujerun dake Office din tace

“Ya Fareed meyasa zanje gidansu Ya Masroor? Bah gidanmu zamu koma bah”

Mik’ewa yayi dasauri yana kallanta

“Gidansu Masroor?” ya furta da Alamar Mamaki

Kai ta gyada tace

“Eh haka yace”

Kafin yayi Magana aka banko kofan Office din aka shigo, a tsorace Sulthana ta kalli kofan ganin Ya Masroor tsaye yana huci kaman zaki yasa jikinta ya soma rawa. Karasowa wayanta yayi rai bace yace

“Fita ki wuce mota ki jirani”

A guje tabar Office har tana kokarin faduwa
A harzuk’e Fareed yace

“What do you think you are doing Masroor? Na lura san Sulthana kake to ka sani bazaka taba cin nasara bah becoz sulthana tawa ce!”

Dariya Masroor ya fashe dashi yana numa Fareed da hannu

“Kai har kana tunanin zan iya tsayawa ina musayan yawo dakai? No! Coz nagaba yayi gaba na baya sai labari”

Bai jira mai Fareed din zaice bah yabar Office din tareda bugo kofa. A mota ya samu Sulthana zaune itada Aisha sai zazzare ido take. Baice komai bah ya tada motan yabar Asibitin a guje, bah Sulthana kawai bah Har Aisha saida ta tsorata da yanda yake tukin. Government house suka nufa kai tsaye suna shiga suka tarar da Mahnoor da Maids bakin kofan Side din Mami suna tsaye suna jiran k’arasowan su. Yana parking Mahnoor ta nufo motan a juye, Sulthana na fitowa ta rungumeta tana dariya. Mahnoor tace

“Uh welcome friend”

Dariya Sulthana kawai tai mata duk hankalinta nakan ya Masroor ganin yanda yawani d’aure fuska. Mahnoor ce tai musu jagora zuwa cikin gidan, wani hadad’en daki takai Sulthana tana cewa

“Sis wannan shine d’akinki inji Mami”

Bin dakin da kallo Sulthana tayi tana Murmushi, gyallenta ta aje kan katafaren gadon dakin ta hau juyi cikeda jin dad’i sannan ta juyo da fara’a sosai akan fuskanta ta rik’e hannun Mahnoor tace

“Kicema Mami nagode Sosai, I’m so greatful”

Itama murmushi Mahnoor din tayi, Aisha tace

“Dak’in yayi kyau sosai”

Ledojin Hannunta ta aje tana cewa

“Zanje gida”

A tare suka fito duk’asuka rakata, Mahnoor tasa driver ya kaita gida sannan Mahnoor ta shiga nunama Sulthana Cikin gidan..

Sosai Sulthana taji dad’in kasancewa gidan, ko bakomai ta kafa tarihi ta zarce su Ya ameenatu dan ita yau gata a Cikin gidan gwamnati..

Basu samu had’uwa da Mami bah ranar dan batanan sai washe gari, Mahnoor ce keta d’ebe mata k’ewa. Da safe tare suk’a sauko da Sulthana Family dinning din dake gidan, Suma neh kawai Sulthana bataiba Ganin Mutumin datake Gani a tv yau a gabanta zahiri

Kanta a k’asa suka k’araso wajan Dinning din, Mami ce zaune da Abba sai Masroor dake gefe fuskannan nashi bah walwala. A hankali ta tsugunna har k’asa ta gaida Abba, cikeda kulawa ya amsa sannan ta gaida Mami itama ta amsa mata da Fara’a.

D’an dagowa tayi ta k’alli Masroor sannan tace

“Ina kwana ya Masroor”

Kamar bazai amsa bah chan kuma yace

“Lapia”

Bah Sulthana kadai bah har Mami da Abba sunyi Mamakin yanda ya amsa mata gaisuwan. Kujera Mahnoor taja mata ta zauna Sannan ta soma serving dinta.. Ganin tak’i sakin jiki taci abincin yasa Abba ya tashi yamusu sallama yabar Wajan..

Itama Mami ta mik’e tana cewa

“Ina zuwa”

Ganin haka yasa Masroor d’aukan plate dinda ke Gabanshi yabar wajan. Sai a sannan ta kalli Mahnoor idanunta taf da hawaye tace…

Ummy Abduol✍????Abduol✍????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button