SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

          *Page 197*

Gudu yake sosai yabi ta bayan gidan inda zai sadashi da filin basket ball. Ganin tuk’in nashi bana hankali baneh yasa Sulthana k’ara fashewa da kuka

“Dan Allah ya Masroor kayi hakuri ka daina gudu”

Wani wawan burku yaja ya juyo yana k’allanta idanunshi a rune

“Sulthana bakya sona ko? Fareed kikeso?”

Batace komai bah k’anta a kasa, fita yayi daga motan ya jingina yasa hannayenshi a aljihu ranshi a b’ace. Tana ganin haka tafito jikinta na rawa ta tsugnna gabanshi kanta a k’asa

“Kayi hakuri ya Masroor, ya fareed na d’aukeshi yayana saboda shiya taimakeni. Ban tab’a sanshi bah kuma bai tab’a cemin yana sona bah”

D’agota yayo daga tsugunnen datake ya tallafo fuskanta suna kallan juna

“Ina Sanki Beauty, ina sanki sosai. Pls ki soni kar sanki yasa na shiga wani hali”

Rungumeshi tayi ta fashe da kuka, a hankali tace

“I love uh to ya Masroor”

D’agota yayi daga jikinshi ya kura mata manyan idanunshi da Mamaki

“What do uh just say”

D’an Murmushi tayi tasa hannu tana share hawayen fuskanta. Da lebbunanta ta furta

“I lav uh”

Tsalld yayi yace

“Woaw!”

Ta kyalkyace da dariya tana kallanshi. Motar Fareed neh tazo wucewa ganinsu awajan yasa yayi parking dan yau ji yake saidai duk abinda zai faru ya faru..

Parking yayi ya fito ya karaso inda suk’e tsaye, Masroor na ganinshi ya had’e rai ya juya ya kalli Sulthana yana cewa

“Shiga mota ki jirani”

Bah musu ta bud’e kofan tana kokarin shiga Fareed yayi maza ya k’ama hannunta, a tsorace ta juyo ta kalleshi. Masroor ya fizge hannunta daga nashi yana huci

“Fareed ka kiyayi kanka, meyasa kake kokarin shiga hurumin daba naka bah”

A hasale Fareed yace

“Hurumin daba nawaba ko hurumin daba naka bah”

Ya kalli Sulthana suka hada ido yace

“Tun ranar da Yayarki ta kawoki chemist din kauyenku Allah ya d’auramin Sanki. Nayita k’okarin in sanar dake ban samu daman hakan bah. Naje neman aurenki wajan Mallan anma yacemin an miki miji. Bayan kin dawo gurina inata kokarin na sanar dake abin yacitira”

Ya d’ago yana kallanta

“Ina matuk’ar sanki Sulthana. Na dad’e ina dakon soyaiyarki a zuciyana”

Fashewa tayi da kuka ta fadi a wurin zaune tana kuka sosai, harga Allah bata tab’a zatan Ya Fareed zai Furta Mata Kalmar so bah.
K’arasowa wajan Masroor yayi yana huci

“Fareed kana b’ata lokacin ka neh a banza, karka taba tunanin Sulthana a matsayin matarka. Na fada zan kuma k’ara fada Sulthana Tawa ce!”

Bai ankara bah yaci Fareed ya kai mai wani mugun naushi a baki nan da nan bakin ya fara jini, Fadane Sosai ya kaure tsakaninsu, Sulthana ta mik’e dasauri tana kuka ta shiga tsakiyarsu

“Ku daina fada d’an Allah”

Ta juya ta kalli Fareed dashima gefen idonshi ke jini tace

“Ya fareed ku daina fada, indai saboda nine na hakura banayi”

Ai kamar k’ara zuga Fareed take ya wawuri Masroor ya soma kaimai nushi, Shiko Masroor kasa dukanshi yayi dan sam baiso hakan ta faru tsakaninsu bah. Ganin Fareed na neman halakashi yasa shima ya fara maida Martani, dukan juna suke bana wasa bah Sulthana na gefensu tana kuka da ihu dan neman agaji. Daidai nan mottocin su Mami suka k’araso wajan a guje dan tun dazu bayan fitansu Mahnoor ta sanar da Mami abinda ke faruwa. Yawo suketayi har Allah yasa suka biyo ta wajan..

Umman Fareed ce ta fara fitowa ta k’araso wajan a zuciye, lafiyayyen Mari ta wanke Fareed dashi tana huci

“Bantaba sanin bakada hankali bah sai yau Fareed, yanzu akan mace shine kuke kokarin Kashe junanku?”

Kasa ma magana Mami tayi anma kana gani kasan ranta bah k’aramin Baci yayi bah. Mahnoor ta k’araso wajan ta rik’e Sulthana daketa kuka kamar ranta zai fita tasata a mota. Motar y’an sandan dake bayan nasu Mami Umman Fareed tasa aka shigar dasu Masroor aka kaisu Asibitin dake Cikin gidan..

Daddy da Abban Fareed suma Ransu bah k’aramin baci yayi bah bama Kamar Abban fareed dan shi cewa yayi Fareed ne baida gaskiya dan koma menene bai kamata ya biyo Masroor har gidansu ya dakeshi bah. Dole hakan yasa aka hadu dan Sulhu wuraren K’arfe sha d’aya na dare a babban Falon Daddy..

Daddy da Abban Fareed a a gefe zaune sai Mami da Umman Fareed suma suna gefe. Su Masroor kuma suna k’an Carpet zaune kowa da kumburaren Fuska. Daddy neh ya soma magana fuskanshi bah walwala

“Banji dadin abinda ya faru bah, haba Masroor haba Fareed. Yanzu akan mace kuke kokarin kashe kanku”

Abban Fareed yayi saurin amshewa da cewa

“Yanzu idan abun nan yakai waje duniya zatai mana dariya akan cewa ga y’ayanmu suna fada tsakaninsu akan mace. Sam wannan abin bai dace bah”

Masroor ne ya soma d’agowa yace

“Daddy, Abba kuyi hakuri”

Abba ya nuna Fareed da yatsa

“Duk abinda ya faru ga babban mai lefi nan, haka kawai Masroor baya kamaka da dukaba dan kazo gidansu. kaida nakema Kallan mai hankali ashe bakada shi, karka manta kaifa babba neh ka girme ma Masroor anma ace haka na faruwa tsakaninku”

Daddy yace

“Ai bashi k’adai bah harda Masroor din, shima kana ganinshi bashida hakuri.”

Abba ya nisa yace

“Sam baku kyauta mana bah. Banji dadi bah kun bamu kunya”

Daddy ya nunasu da yatsa

“Sannan ku sani yarinya bazata taba aurenku bah duka tuna abin haka neh”

Mami tai Saurin cewa

“Ur excellency inaga hakan kamar tauyewa neh. Yakamata ita yarinya ta fadi wanda takeso sai a bata, wanda kuma bataso saiya hakura”

Gyada kai Abba yayi

“Wannan Gaskiya neh”

Daddy yace

“Abinda za’ayi gobe in Allah ya kaimu da Sassafe dukanmu zamu dunguma muje kauyensu dan mu samu asalinta. D’an duk wannan abin da mukeyi kamar munyi tuyane mun manta da Albasa”

Umma tace

“Gaskiya neh”

Abba yace

“Hakan ma yayi, daga chan sai ayita ta k’are ta fadi wanda takeso mu nema masa aurenta kawai”

Kowa dake falon ya amince Abba yace su Fareed su tashi su tafi, duk suka mik’e suka bar falon kowa jiki a sanyaye..

A daren Mami ta samu Sulthana a dakinta kwance tana aikin kuka, karasawa tayi ta zauna kan gadon ta dagota tareda share mata hawaye.

“Wannan kukan duk na menene? Ya isa haka kinji”

Kai ta gyada kawai kanta a kasa dan yanzu kunyan yan gidan takeji. Mami tace

“Gobe dasassafe ki shirya zamuje kauyenku dan..”

Kuka Sulthana ta fashe dashi ta rik’e hannun Mami gam

“Dan Allah Mami karku maidani wajan Baffa kasheni zeyi”

Rufe mata Baki Mami tayi cikeda tausayawa

“Bah barinki zamuyi bah, zamuje neh dan yasan kina wajanmu”

Dakyar Mami ta shawo kanta ta amince, saida taga Barci ya dauketa Sannan tabar dakin..

Ranar Fareed da Masroor babu wanda ya runtsa kowa da abinda yake s’akawa a ranshi. Ganin bacin ya gagara yasa Masroor mik’ewa yayo Alwala ya soma kai kukanshi gurin Ubangiji..

Kamar yanda akayi da Sassafe Abban Fareed da Umma sai shi Fareed din suka iso gidan, Already su daddy sun shirya. Wasu motoci daban suka d’auka bana gwamnati bah suka dau hanyar kauyensu Sulthana..

Fareed ne yakema Drivern kwatance har suka kawo kofar gidan. Gaban Sulthana ne ya fadi sanda ta kalli gidan, duka suka fifito daga mota anma banda Sulthana, Mahnoor ta bud’e kofan

“Sulthana fito mana”

Dakyar ta sauko kafa ta fito tana bin kofar gidan da Kallo, bah abinda ya chanza har yanzu komai na nan yanda yake, saidai ta lura kamar yanzu bah almajirai a runfar su. Yaro su Abba suka samu yamusu Sallama da Baffa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button