SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ba’adau lokaciba ya fito daga gidan, Kallo d’aya zakaima Baffa kaga ramar da yayi. Duk ya fige kamar bashi bah, ganin Manyan Mutane Yasa jiki na rawa ya shiga cikin gida yasa aka shishimfida tabarma sannan ya fito yace
“Bismillah ku shigo”
Sam bai lura da Sulthana dake jikin Mami a makale bah. Tsakar gidan suka shiga Suka zazzauna, Ameenatu ta fito daga dakin Mama dauke da kwanun sha ta aje Sannan ta gaidasu, harta mik’e suka hada ido da Sulthana. Mik’ewa tayi dasauri tana nuna Sulthana bakinta na rawa
“Su..Sul…Sulthana”
Baffa ya mik’e yana kallan inda Ameenatu ke nunawa, jin kamar an kira sunan Sulthana yasa Mama fitowa daga dakinta hakama Hafsatu
K’ara shigewa jikin Mami tayi tana boye Fuska, Baffa ya soma Hawaye yana cewa
“Sulthana ki gafarceni, nasan nayi kuskure. Sharrin shedan neh da kuma rashin sani”
Jin abubuwan da Baffa yake cewa yasa ta d’ago tana kallanshi da Mamaki. Mama ta k’araso wajan itama tana hawaye
“Sulthana dama kina raye, bah inda bamuje nemanki bah. Baffanki kullum ke yake anbata”
Sai kallansu Sulthana take da Mamaki, Abban Fareed neh yace
“Mallan zauna muyi magana”
Bah musu Baffa ya zauna yana matsar kwalla. Tunkan Abba ya sake Magana Baffa ya soma zaiyane musu duk abinda ya faru yana hawaye. Kuka Sulthana take na farinciki da Allah yasa ita bah shegiya bace. Bayan ya gama Abban Fareed shima ya dora da basu labarin zaman datai tareda fareed da kuma wanda tayi a gidansu Mami..
Zabura Baffa yayi ya gyara zama yana rarraba ido
“Dama da Gwamna da Mataimakinshi nake zaune”
Ya juya ya Kalli Mama dasu Ameenatu tana mai cikeda Farinciki. Hafsatu da yanzu ta zama salaha tace
“Sulthana ki yafemin lefukan dana miki, nasan nayi kuskure”
Yau Sulthana na Cike da Farinciki yau ga yan uwanta na santa suna neman gafaranta.. batareda wani dogon tunani bah tace
“Baffa, Mama, yaya Ameenatu, yaya Hafsatu duk na yafemuku tuntuni, dama ban rikeku bah. Ina sanku sosai”
Mik’ewa tayi ta rungume Baffa, ya fashe da kuka yana cewa
“Allah ya jikan Mahaifiyarki Allah ya gafarta mata. Ke kuma Allah ya miki Albarka”
Ameen tace Sannan ta janye jikinta ta rungume Mama da sauran Y’an uwanta..
Su Daddy yan kallo suka koma kowa yana tayata Murnar sassantawa da Mahaifinta da y’an uwanta
Mama ta mik’e ta soma kici kicin d’aura girki na musamman Dan tarban manyan Bakinsu…
Saida aka natsa, Sulthana tana d’akinsu Yaya Ameenatu itada Mahnoor sunata basu labarin Birni sukuma su Daddy suna kam tabarma cikin ihuwa sunata hira da Baffa kamar sun saba. Su Masroor kuwa suna chan gefe zaune sunyi jugum jugum kowa da abinda yake sakawa a ranshi…
Ummy Abduol✍????
????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????
By Ummy Abduol
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Page 198*
Su Masroor kuwa suna chan gefe zaune sunyi jugum jugum kowa da abinda yake sakawa a ranshi sannan Abba ya gyara zama yaba Baffa labarin Soyaiyar dake tsakanin Sulthana da y’ayansu sanna ya d’aura da cewa
“Dole yanzu zamu kirata neh ta zaba wanda takeso a cikinsu”
Baffa ya b’ata rai
“Haba ranka ya dad’e ai duk wannan bai taso bah, kuma fah iyayenta neh ku da kanku kawai ku zaba mata wanda zata aura”
Daddy yayi murmushi yana k’allan Baffa
“Aa baza’ayi haka bah, idan mukai haka kamar mun tauyeta neh. Tho idan kuma muka zaba mata wanda ita bai kwanta mata bafa?”
Shiru Baffa yayi baice komai bah. Abba yad’au waya ya kira Umma yace su fito duka, duk suka fito daga dakin Mama itada Mami suka zauna k’an tabarman. Baffa Yacema Mama ta kira Sulthana tace tho
Dakin ta shiga ta kirata suka taho tare, koda sukazo sun samu Fareed da Masroor xaune a wajan. Kusada Mami ta zauna k’anta a kasa, Abba ya kalleta da fara’a
“Y’ata mun kiraki neh dan muji ra’ayinki. Munaso ki fada mana tsakanin Masroor da Fareed wa kikeso”
Gabanta neh ya fadi ta d’ago ta kalli Masroor taga kanshi a kasa ta maida dubanta ga Fareed shima kanshi a kasa. Kasa magana tayi gabanta na cigaba da bugawa. Mami ta tabota
“Sulthana kiyi Magana mana karkiji Tsoro ki Fada abinda ke ranki”
Shiru tayi nad’an mintina Sannan tad’an dago bakinta na rawa tace
“Ya Fa…”
Dasauri Fareed ya d’ago ya kalleta da Alamar Mamaki, Masroor ko runtse idonshi yayi zuciyarshi na bugawa da sauri. Umman Fareed tace
“Kiyi Magana mana Sulthana keh muke jira”
Ta maza tayi ta saukar dakanta kasa tace
“Yah Masroor”
Sauke kai Fareed yayi yana girgixa kai ahankali, dasauri ta tashi tabar wajan. Abba yace
“Tho Alhamdulillah tunda yarinya ta fadi wanda takeso yanzu sai ayi maganan sadaki koh”
Su Umma najin haka suka mik’e suka bar wajan, Su Fareed suma suka mik’e suka fita waje. Fareed ya share hawayen idonshi yace
“I’m very sorry friend”
Ya mik’ama Masroor hannu yace
“Congratulations am very happy for you, Allah ya sanya Alheri”
Jikin Masroor neh yayi sanyi shima ya mik’amai hannu
“Ni yakamata nabaka hakuri, bakai bah”
Fareed ya girgixa kai ya shiga mota ya zauna ya daura kanshi jikin stering motan ranshi jagule..
Sulthana na shiga d’akinsu ta fada kan gado ta fashe da kuka, Ameenatu ce ta dafata tana cewa
“Meke faruwa Sulthana?”
Mik’ewa zaune tayi hawaye chabe chabe a idonta, tace
“Bansan da wani ido ya Fareed zai kalleni bah. Gani nake kamar namai Butulci”
Hafsatu ta dafata tana Murmushi
“Mahnoor ta mana bayanin komai, kuma bakida laifi saboda bai sanar dake bah Sannan kuma na lura bah wai sanki yake bah tausayinki neh”
Sulthana ta k’ura mata ido da Mamaki, gyada mata kai Hafsatu tayi sannan ta juya ta Kalli Ameenatu wacce itama su take kallo ta juya ta maida dubanta ga Sulthana tace
“Ya Ameenatu ta dad’e tanasan Likitan nan, tun sanda ta soma ganinshi ta fara sanshi, kullum sai tayi min maganar shi.”
Mik’ewa Ameenatu tayi rai b’ace
“Baki kyautamin bah Hafsatu Ashe bazaki iya rik’emin d’an sirrin nan dana baki bah”
Murmushi Sulthana tayi ta share hawayen Fuskanta ta mik’e ta fito tsakar gidan, ganin su Fareed basa wajan yasa tasa takalmanta ta fita kofar gida. Zaune ta sameshi cikin mota shida Masroor suna hira jefi jefi, nesa dasu ta tsaya Masroor na ganinta ya fito ya karaso inda take yana murmushi
“Har na cire rai Beauty, sai gashi nine gwaninki”
Hannu yasa ta rufe fuskanta tana dariya
“Dan Allah ya Masroor inaso nayi magana da Ya Fareed”
Murmushi ya mata
“Bbu komai ki sameshi a mota”
Dariyan jindadi tayi
“Thank uh Bro Masroor”
Da Sassarfa ta k’arasa bakin motan ta bud’e ta shiga tana Kallanshi
“Ya Fareed kayi hakuri dan Allah”
Sai a Sannan ya d’ago ya kalleta tareda k’irkiro Murmushi
“Bakimin komai bah Queen, Laifina neh da ban fadamiki tun tuni bah naiyi zurfin ciki, haka Allah yaso. Allah ya nufa ke bah Matata bace”
D’an dukar dakai tayi tana wasa da zoben dake hannunta tace
“Nagode ya Fareed, bazan t’aba mantawa dakaiba a rayuwata. Kayimin Abubuwa da dama wanda banida bakin godiya, ka taka muhimmiyar rawa a rayuwata thank uh v….”
Saurin katseta yayi ya d’aura yatsanshi a lebenshi
“Uh dn’t have to thank me”
Jim tayi nad’an wani lokaci sannan tace
“Ya Fareed akwai wani abu danakeso kayimin dan Allah”
Batareda wani bata lokaci bah yace
“Menene shi Queen?”
Tacigaba da cewa
“Inaso dan Allah Ya Fareed ka auri ya Ameenatu”
Dasauri ya juyo yana kallanta da mamaki, gyada mai kai tayi tana y’ar murmushi. Kasumbar dake fuskanshi ya shafa