SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ita tace miki tana sona?”

Girgiza kai tayi alamar Aa. Ya numfasa yace

“But queen I have no feelings for ha, and zai iya yuwuwa bata sona. Kawai ki barshi nagode”

Ta turo baki ta soma gungunai

“Nidai Dan Allah Ya Fareed ka aureta, shes kind kuma batada matsala. Nasan zata soka and kuma kagani zaku saba”

Dariya yayi Mara sauti yana k’allanta kasa kasa, baisan ya musa mata kuma a ganinshi wannan karamci tamai and kuma bah lefi yarinyan tanada kyau Sam bata kamo k’afar Queen dinshi bah dukda ita b’akace.

Ya juyo da Fara’a kwamce kan Fuskanshi yace

“Shiknan Queen na Yarda”

Ihu ta saki tana dariya har saida Masroor ya K’ara sako wajan dasauri. Fitowa daga motan tayi ta shiga cikin gida da gudu. Dakyar suka shawo kan Ya Ameenatu ta fita wajan Fareed, a waya Sulthana ta fadama Masroor abinda ke faruwa, Yaji dadi sosai shima. Ameeantu da Fareed sun fahimci juna kuma har ya Amince zai aureta, su Daddy sunyi Mamaki sosai jin Maganan. Basu bar Kauyensu Sulthana bah saida aka tsaida Ranar Bikin Masroor da Sulthana sai Fareed da Ameenatu wata d’aya, Aka ba Baffa sadakinsu Dubu D’ari d’ari dan Baffa yace baison Asa Sadakin dayawa..

Mama ta rok’i Alfarman a bar mata Sulthana har zuwa ayi bikin. Baffa ya tambayi Sulthana ta amince batai Gardama bah, Masroor sam baiso haka bah bah yanda zaiyi hakanan ya hakura sukai musu Sallama suka tafi bayan Sun Cika Baffa da kudi. washe gari Mami ta turo Driver da Kayan Sawan Sulthana da Kayan Abinci dana sawa nasu Mama cike da Mota…

Kula Sosai Sulthana take samu a gidan Mahaifinta ta bangaren Mama da Baffa har takan rasa wayafi kula da ita. Kullum suna Makalle da Masroor a waya haka soyaiya Suke mai Tsafta da Shiga rai. Fareed na Xuwa wajan Ameenatu hakan yasa suka k’ara shakuwa da ita, ya sai mata waya itada Hafsatu. Shima Masroor na xuwa shida Yasir..

Mama ta zage tanata gyara Y’ayan nata daidai karfinta, Mami ma Tana aiko Mahnoor da Wasu kayan gyaran jikin anaba Mama dan tayi Musu. Yau Saura kwana biyar Biki, Yau Sulthana take expecting Mahnoor dan tace mata zatazo har a gama biki. Tana gidansu Sadiya K’awarta Wayan Sulthana yahau Ruri, ta d’auka da Fara’a tana cewa

“Kin iso neh”

Harta mik’e ta koma ta zauna tace

“Yah Hafsatu tana Nan kice ta kawoki”

Bata jira mai zatace bah ta kashe kiran. Sadiya dake gefenta tace

“Ta iso neh?”

Da Fara’a tace

“Eh wai da lefe suka zo”

Dariya Sadiya tayi ta mik’e dasauri

“Ah bari muje muga Lefe”

Tab’e baki Sulthana tayi sadiya tad’au mayafinta ta fita daga gidan dasauri. Tana fita Mahnoor ta shigo gidan itada ya Ameenatu, sulthana ta mik’e dasauri ta rungumeta tana Dariya

“Uh welcome”

Dagota Mahnoor tayi daga jikinta tana k’are mata kallo

“Friend kinga yanda kika koma? Kin K’ara kyau sosai”

Turo baki Sulthana tayi tana doka kafa a kasa. Nan suka zauna suka soma hiran yanda bikin zai kasance basu bar gidan bah sai Yanma lis lokacin sun tabbatar yan kawo lefe sun tafi..

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

            *Page 199*

Lefe na gani na Fada aka kawo kowaccen su akwati dozin biyu akai mata. Mutanen Kauyen sai shiga suke suna kallan kaya kowa na tofa Albarkacin bakinshi..

Ranar Alhamis Ameenatu da kawayenta Sukayi k’auye day, su kuma su Sulthana dukayi Fulani day itama itada nata k’awayen. Ranar Juma’a aka sasu Lalle da daddare. A Daren Masroor da Fareed sai d’an rakiyansu Yasir dukazo gidan, a tare amaren suka fito kowacce ta k’araso wajan angon nata. Masroor sai Kallan Sulthana yake da Murmushi

“Beauty kin k’ara kyau meye sirrin?”

Rufe fuskanta tayi da Hannayenda da sukasha had’adden kunshi. Ya rik’o hannunta yana kallo yace

“Waya miki wannan design din yayi kyau sosai”

D’an murmushi tayi ta turo baki

“Ya Masroor ka daina wannan maganan kanasa inajin kunya”

Dariya yayi yana shafa sumar kanshi

“Ki daina jin kunyana beauty, nidake yanzu mun zama d’aya karki manta gobe za’a daura mana aure ki zama tawa na xama taki”

Hannu tasa ta rufe fuskanta tana dariya K’asa kasa, daidai nan Yasir ya karaso wajan yace

“Ni kun barni chan gefe”

Ya kalli Sulthana

“Madam kinsan meye?”

Ta girgiza kai tana kallanshi, ya gyara tsayuwa ya sassauta Murya

“Nifah Sistern nan naki nakeso”

Tace “wah kenan?”

Yace “Hafasat”

Da zumud’i tace

“Dagaske?”

Kai ya gyada Mata, Masroor yayi saurin cewa

“Dallah kyalle wannan, mayaudari neh karki yarda
kadama ki fadamata”

Duka Yasir yakaimai

“Kai bansan fah iskanci i’m serious”

Sulthana tace

“Karka damu Ya Yasir zansan Yanda zanyi”

Godiya ya mata yabar wajan. Sun d’an taba hira sannan suka musu Sallama Suka tafi..

Washe Gari ya kasance ranar Sati, a ranar duban mutane suka shaida d’aurin auren Fareed da Ameenatu, sai Masroor da Sulthana. D’aurin auren daya samu hallartar Manyan Mutane tun daga kan shi kanshi shugaban k’asa, Gwamnoni, sarakuna da saurayan Manyan mutane masu fada aji a nigeria..

Har hawaye saida Baffa yayi dan bai taba tunanin zaiga irin wadannan Mutanen bah a rayuwarshi. Masroor baki yak’i rufuwa, Ana gama d’aurin aure yad’au wayanshi ya soma nemqn layin beauty. Ya dad’e yana ringing kamin a kawo mata ta d’auka tana y’ar Murnushi, cikeda Farinciki yace

“Beauty am now urs uh are mine. An d’aura”

Dariya tayi ta kashe kiran tad’au buta tayi alwala tazo ta tada nafila. Addua tayi sosai har tana hawaye musamman data tuna ana aurenta Ummanta bata raye, tayimata Addu’a sosai. Sannan ta tashi ta koma cikin k’awayenta..

Anyi d’aurin aure lapia kowa ya koma gudanshi. Wuraren k’arfe hudu na yanma aka d’au Amare dan kaisu Gidajensu, Ameenatu da Sulthana sai kuka suke bama Kamar Ameenatu, Nasiha mai ratsa jiki tayi Baffa da Mama sukai musu sai Maman Sadiya. Sannan aka d’aukesu zuwa government house..

Su kuma achan ake shagalin bikinsu Fareed da Masroor dan sun hada taron ne shi yasa gidan ya cika mak’il bah masaka tsinke. Yan kauye nan suka saki baki suna kallan Aljannar duniya, Wani had’aden Part dake gidan aka kai Sulthana, ita kuma Ameenatu sai daga baya za’a kaita. Mai make up aka kira ta d’andasa musu kwaliya sukasa had’aden golden gown dan zuwa dinner. Yau k’auye duk an basu anko sunsha sunata washe baki cikeda Murna. Kowacce Amarya tareda angonta suka tafi wajan dinnern, suma angon nan cikin Babban riga Fari tas dah aikin Golden. Sunyi kyau ainun gwanin ban sha’awa

A gurin dinner anci ansha anyi nak, su deejatou harda zuba abinci a leda lol. Bayan an gama an dawo sannan Aka kai Ameenatu gidanta. Washe Gari da safe akayi bud’an kai, shima wani buki akai na musamman Bayan an gama akasa yan kauye a mota aka maidasu bayan an cikasu da alheri sunata godiya. Aka bar Sulthana daga ita sai Mahnoor, Aisha batasamu zuwa bikin bah dan ta koma makaranta…

Mahnoor batabar Side dinbah saida sukai sallan isha. Wuraren k’arfe tara ango ya shigo sanye da fara k’ar din yadi sai zuba kamshi yake Hannunshi rike da leda, k’ara rufe fuskanta tayi cikin gyale tana wasa da zoben zinarin dake hannunta. Kan gadon ya zauna gefenta a hankali yasa hannu ya yaye gyalen ya d’ago fuskanta, runtse ido tayi tana murmushi shima murmushin yayi yace

“Open ur eyes beauty, Masroor dinki neh.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button