SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tad’an bude ido kadan tareda janye fuskanta ta dan kauda kai. Hulan dake kanshi ya aje gefen bedside ya mik’e tsaye tareda riko Hannunta

“Tashi muyi Alwala muyi nafila dan mugodema Allah”

Bah musu ta mik’e shi ya fara shiga yayi alwalan ya fito Sannan itama ta shiga. Ko kamin ta fito ya shinfida musu Sallaya, tana fitowa ta yafa gyalenta suka tada sallah.

Bayan sun idar ya d’auko ledan daya ajiye yace

“Dauko mana plate Beauty”

Bah musu ta mik’e ta aje gyalanta akan gado ta fito daga dakin, shige shige ta soma yi dakyar ta gano kicin din. Tsayawa tayi tana k’arema wurin kallo dan kaya neh mak’il a ciki masu tsada da daukar ido, murmushi tayi dan tasan wannan aikin Mami ce. Kwalin dinner set ta d’auko dakyar ta bud’e ta ciro plate ta wanke sannan ta d’auko cups shima ta wanke ta koma dakin. A gabanshi ta ajiye tana kokarin mik’ewa, dasauri ya rike hannunta ya jata ta fado jikinshi

“Ina zaki? Ai tare zaki zauna muci”

Turo baki tayi tana kokarin fizge jikinta daga nashi

“Nifah na koshi dazu muka gama cin abinci da Mahnoor”

Yanda tayi maganan bah k’aramin burgeshi yayi bah har saida ya kwaikwayi yanda tayi. Dariya tad’anyi ta k’ara shagwabe Fuska

“Nidai ka daina”

Kazan ya saka a plate din ya bud’e fresh youghut ya zuba a cup dinda ta ajiye Sannan ya soma bata a baki. Kauda kai tayi tana yatsine fuska

“Nifah ya Masroor na koshi”

Matso da fuskanshi yayi daidai nata har numfashinsu na had’uwa

“Wai yaushe za’a chanza min suna neh daga Ya Masroor”

Batace komai bah sai murmushi datayi. Tura mata kazan ya somayi tana ci tana bata fuska kamar xatai kuka, shi kuma yana mata d’ariya. Tadanci bah lefi sannan ta mik’e ta xauna kan gado tana cigaba da yatsine fuska

“Kagani koh kasa cikina ya cika dayawa”

Mik’ewa yayi ya kamo hannunta

“Tho zo na miki doki nasan cikin zai sassauta”

Tsugunawa yayi a kasa sannan yace tahau. bako kunya ta d’ane bayanshi ya soma tafiya ita kuma sai dariya takeyi, sun dad’e suna haka sannan ta sauka tana hanma a hankali

“Bacci nakeji”

Kai ya gyada yace yana zuwa ya fita daga d’akin. Kamin ya dawo ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta sauya kayan jikinta zuwa na barci tahau gado nan da nan barci ya d’auketa

Wanka ya shiga yayi a d’akinshi, koda ya dawo nata ta dad’e dayin bacci. Hannun jalabiyar jikinshi ya nad’e ya d’auketa chak ta bud’e ido dasauri tana kallanshi Murnushi ya mata ganin yana kokarin fita da ita daga dakin yasa ta soma zulezule, bai direta ko inaba sai lumtsatsiyar gadonshi.

Mikewa tayi ta zauna a tsorace

“Ya Masroor Bacci fah b
Nakeji”

Bako kunya yace

“Kazana da kikaci zan amsa abuna”

Bata gane me yake nufi bah tace

“Tho bah kai kace naci bah ni yanzu ina zan samu kaza na biyaka”

Tana magana cikeda shagwaba. Fitilan d’akin ya kashe ya rage na side lamp sunada haske sosai dan su kadai mah sun wadata d’akin. Kan gadon ya hau ya matso kusada ita tad’an mata, ya kara Matsowa ta k’ara Matsawa

“Beauty ni dodone? Meyasa kike matsawa”

Shagwabe fuska tayi

“Ni tho ka kwanta a gefe nima na kwanta a gefe”

Maganar tazo mai a bazata anma ya share yace

“Anma ai keh matata ce xan iya kwantawa a kusa dake ai”

Batace komai bah sai chuno baki datayi, matsowa yayi kusada ita ya rikota tareda matseta a jikinshi. Bud’e baki tayi zatai magana ya had’a bakinshi da nata. Ina ganin haka na tattara inawa inawa nabar musu gidan gaba d’aya na koma k’auyenmu..

Bayan Wata hud’u

Masroor ne zaune a falo yana daddana system dinshi, hankalinshi duk ya tattara ga abinda yakeyi. Sulthana ta fito cikin wani riga pink iya cibi da wani matsatsen short, kayan sun mata kyau sosai. Jikin Masroor ta fada tana maida numfashi. Dasauri ya aje system din ya k’ara matseta a jikinshi

“Beauty naji jikinki ya k’ara zafi, nifa zafin jikin nan na. Cutana gashi kinki yarda muje asibiti”

Batace komai bah saima janye jikinta datayi daga nashi ta koma chan gefe ta zauna. Kara matsowa yayi yana kokarin tabata, bai ankara bah ta soma kwararo mai Amai, Aman take sosai jikinta na rawa. Riketa yayi har saida ta gama sannan ya mik’e ya dauko ruwa ya bata ta kuskure baki ya dauketa ya kaita daki ya kwantae da ita. Masu aiki ya kira suka gyara wajan ya koma dakin

Kwance ya sameta tana juye juye jikinta bah dad’i, daukanta yayi chak ya kaita bayi ya mata wanka ya fito da ita. Da kanshi yasa mata kaya ya d’auketa yasata a mota sukad’au hanya. Tana ganin sun nufi asibiti ta soma bata fuska, baice mata komai bah. Da kanshi ya d’auketa suka gida, bah tareda wani b’ata lokaci bah aka dubata tareda mata gwaje gwaje, a nan neh aka gano cikin datake d’auke dashi na wata biyu.

murna sosai Masroor yayi, d’aukanta yayi suka nufi gidan Mami bayan an rurubuta mata magunguna tareda bata shawarwar..

Ummy Abduol✍????

????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION

            *Page 200*

 ????

Da Farinciki suka k’arasa gidan Mami bah ko kunya ya mik’a mata takardan test din itadai Sulthana na zaune k’anta a kasa. Mami na gama karantawa ta girgiza kai tana mai cikeda farinciki

“Allah ya raba lapia”

Ga Mamakin Mami da Sulthana saijin Masroor sukai yace

“Ameen Mami”

Kunya sosai Sulthana taji har ta k’ara duk’ar dakai, shiko gogan ko a jikinshi. Tun daga ranar Sulthana ta k’ara samun kula daga wajan Mami da Masroor da duk sauran yan gidan mah. Tattalinta sukeyi sosai kamar kwai hakan bah k’aramin sata farinciki yayi bah..

A bangaren Fareed da Ameenatu basuda Matsala zama suke na soyaiya da mutunta juna. Ita tana d’auke da nata cikin na wata uku, Mama da Baffa bah k’aramin farinciki sukayi bah da samun labarin cikin da y’ayansu suke d’auke dashi. Yasir da Hafsatu sun hada kansu har anma Ranar biki. Haka Sadiya k’awar Sulthana da S’aood wanda ya ganta lokacin biki ya lik’e mata.

Bayan wata shidda Ameenatu ta haifi santalelen d’anta namiji inda akasa mai suna Farhan. Bayan wata d’aya Sulthana ta xankado santaleliyar Y’arta mai kamada Masroor sak. Murna wajan su Mami ba’a magana. Inda yarinya taci sunan Mahaifiyar Sulthana wato Rabiatu anma ana kiranta da Mimi. Kula Sulthana take samu itada jaririyarta sosai daga bangarorin biyu hakan yasa ta saki jikinta tana shayar da y’arta hankali kwance..

Ban k’ara komawa government house bah sai bayan Shekara biyu. Anan nakejin Labarin Ansha bikin Hafsatu da Yasir haka na Sadiya da Sa’ood dukanninsu suna d’auke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe. Sai Mahnoor dake karatunta na likita a k’asar Masar

Had’adiyar Mace mai jida kanta na gani ta fito a wata lumtsatsiyar Mercedes benz, saida na k’ara matsawa dakyau naga Ashe Sulthana ce. A gajiye ta shiga gida ta fada kan kujera tareda fadin wash. Y’ar yarinya ce fara sol kana ganinta kaga Masroor saidai tafi Masroor din haske ta taho dasauri da tafiyanta dabai gama k’wari bah ta fada jikin Sulthana. Rungumeta ta k’arayi tana y’ar Murnushi

“Mimi ina kikanar nannyn naki”

Dai dai nan nannyn ta karaso wajan a guje tana kwalla ma yarinyan kira. Ganin Sulthana yasa tayi turus ta tsugunna tana gaidata. Amsawa tayi ita kuma yarinyan sai k’ara shiga jiki Mamanta take tanama Nannyn dariya. Sulthana ta kalli Nannyn tace

“Barta kawai tunda na dawo”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button