SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

       *Page 26 to 30*

Ameenatu da har lokacin tak’e tsugunne a kasa tana kuka ta dago ta kalleshi da mamaki
“Mallan Yanzu dah bakinka kake Fadin irin wannan maganan” cewar Mama Tsaki yayi batare da yace komai bah yayi shigewarshi dak’i
Dosar kofan fita Mama tai Ameenatu ta mik’e dasauri ta kamota tana cigaba da kuka
“Mama dan Allah karki tafi, kiyi Hakuri”
Hawaye ne ya gangaro a idon mama

“Na gaji da zama ana Azabtar da Yarinya ina kallo banida halin magana, Duk inda naji sai aita nunani ana gulmana mutane sai suyita tunanin ni nake wahalar da Sulthana”
Hawayen idonta Ameenatu ta Share
“Mama karki manta idan har kika fita kin saku, Dan Allah Mama karki fita kiyi Hakuri, Idan Kika fita Zamu Shiga wani hali”
Murmushin takaici Mama tai
“Ameenatu duba ki gani yanda ya Kori yarinyan nan da Daren nan, Ina Yake tunanin Zata? Yanda Kauyen nan Yakeda Hatsari kuma gata K’arama”
Shiru Ameenatu Tai nadan wani lokaci.

Sallaman Hafsatu sukaji ta shigo Gidan Rik’e da Bak’ar leda ganinsu Mama a tsaitsaye Yasa Ta K’araso kusa dasu
“Mama lapia meya Faru?”
Ameenatu ce ta shiga zaiyana mata duk abinda ya faru, Dan Murmushi tai tareda Girgiza Kai Sannan ta Kalli Mama
“Tho Mama mu ina ruwanmu, tunda ya koreta ai shiknan mun munma huta wallahi”
Tsaki Ameenatu taja
“Hafsatu kinada Matsala, Bansan Keh inda kikasa gaba a rayuwarki bah”
Turo baki tai ta kauda kai..

Mama ta dafa Kafadar Ameenatu
“Ameenatu kuje ku nemo Sulthana dan Allah, Kunga Dare neh Akwai hatsari”
Kara turo baki hafsatu tai tana Gungunai
“Ni Mama na Gaji Wallahi”
Tsawa mama ta daka Mata, Hijab Ameenatu ta koma ta dauko suka fito itada Kawarta Habiba suka Fita Hafsatu na Binsu a Baya, Sallama Habiba tama Ameenatu ta wuce gida, Ameenatu ta juya ta Kalli Hafsatu dake tafiya kamar wacce kwai ya fashema a ciki
“Haba Hafsatu ki dago kafa Mana Wai meye Haka”

Dogon Tsaki Hafsatu taja nifa Gaskiya Ya Ameenatu kun Takura min, Allah badan Mama ta matsaba bah Abinda zai kara fito dani da Dadaren nan. Girgiza kai Kawai Ameenatu tai ta cigaba da Tafiya tana haske hasken Hanya da Torch light..

Sulthana kuwa tana Fitowa Gudu kawai take batareda tasan inda ta nufa bah, Saida tai mai isarsa Sannan ta Samu guri ta zauna Tana kuka sosai mai Sauti, Kuka take kamar ranta zai Fita
“Umma meyasa kika tafi kika barni? Meyasa baki bari mun tafi tare bah. Ina sanki Umma, ina Kewanki”
Kuka ta cigaba dayi gwanin ban tausayi, duk ilahirin Jikinta zugi yake mata bin jikinta tai da K’allo taga duk Baffa ya fafasa mata jiki. Nan da nan jikinta yayi zafi, Idanunta suka fara Lumshewa. Kangon Ginin Kasan dak’e Gefenta Ta mik’e dakyar tana Ganin Jiri ta k’arasa ta Shiga Cikin Kangon ta zauna, Jin Jirin tai na K’aruwa ta lumshe ido da k’arfi ta Bude tareda Girgiza kai. A hankali ta Sulale a Wajan..

Bah Indah su Ameenatu basu jeh bah, Tun daga Gidan Kawayen Sulthana Har Wuraren dah suk’e zaton Zata Iya boyema, Anma bata bah Alamarta. Hankalin Ameenatu Yakai Kololuwa Wajan Tashi, Ganin Dare Yayi sosai Yasa Suka Koma Gida. A tsakar gida Suka samu Mama sai kaiwa da komowa take, Tana ganinsu ta K’araso dasauri
“Yaya kun Ganta?”
Kasa magana Ameenatu tai, Hafsatu ce ta Yatsine Fuska
“Duk inda Muke tunanin Za’a sameta munje bamu ganta bah”
Bata jirah mai Mama zatace bah ta Wuce dakinsu..

Kuka Ameenatu tahau yi a hankali Kanta a K’asa, Mama ta dafata itama hankali tashe,
“Kiyi Hakuri Ameenatu, Insha Allahu Za’a ganta jeki kwanta kinji”
Kai kawai tai k’arfin Halin Dagawa ta Nufi dakinsu jiki a Sanyaye…

Hasken daya Haska mata Fuska neh Yasa ta Bude ido dak’ar, Ganin Gari ya Waye Tangaran da Alamar Rana mah ta Farayi Yasa ta Mik’e Zaune Dakyar tana Yatsine Fuska. Wanne Irin Mugun Ciwo Kanta keh mata da duk ilahirin Jikinta, dakyar ta mik’e tsaye Ganin Har yanzu tana Jin Jiri Yasa ta koma ta Zauna Tana Hawaye a Hankali. Abubuwan da Suka Faru jiya suka Dawo mata, Kuka ta Fara Sosai Tareda Daura Hannayenta Biyu akai
“Umma Ki Dawo dan Allah, Ina Sanki meyasa zaki tafi ki Barni, Wallahi Baffa naso ya Kasheni. Dan Allah Umma ki dawo mu zauna tare, Kin Barni Cikin…”
Kukan neh Yaci Karfinta, Sulalewa tai ta kwanta Tana Shafa Ciyayin Dake Kasan wajan tana Cigaba da Kuka..

Ta dade a haka Sannan Ta daure ta Mik’e ta Fito daga kangon Tana tafiya Saboda Yanda Takejin Jikinta yana mata Ciwo. Duk inda Ta Wuce K’allanta ake, Sai Yanzu ta Tuna Koh Dan kwalli babu a kanta. Runtse ido tai wasu Sabbin Hawaye suka gangaro Mata, Direct Gidansu Sadiya Ta Wuce dan Duk Kauyen nan ita kadaice Tasan Zata iya Taimaka mata da Wani abun…

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 31 to 35*

kuyi min afuwa jina shiru da kukai, Hakan ya faru neh bisa Rashin Lapia danai. Anma Alhamdulillah naji sauqi, Nagode Sosai da Kulawarku a Kaina

Dis page x 4 uh besty Ayoosh Gidado Yar’adua “My Gidos”

Direct Gidansu Sadiya ta wuce dan duk kauyen nan ita kadai tasan zata iya taimaka mata da wani abun. Dakyar ta karasa gidan ta Shiga da Sallama, A Tsakar gida ta Samu Sadiya tanayi ma Mamanta Sallama Zata tafi makaranta.
Juyowa tai ta K’alleta da Mamaki
“Sulthana! Daga ina kike? Jiya su Yaya Ameenatu nata nemanki”
Waje ta samu ta zauna a tsakar gidan tareda tafe kai, Dasauri Sadiya ta karaso inda take
“Mama! Mama!! Fito kiga Sulthana”
Mama da Baba suka fito a Tare dasauri,
“Lapia Sulthana meke Faruwa” cewar Mama
Kuka ta Fashe dashi Kanta a Kasa, Baban Sadiya neh ya K’alleta Cikeda tausaya wah
“Sulthana, Yi Magana Mana”
Kasa magana tai sai kukan data K’ara Fashewa dashi, Mama ta K’alli Baba tana nunamai Sulthana Hankali Tashe
“Mallan Kalli jikin Yarinyan nan, Duk yanda akai Duka Akai mata”
Sai a Sannan Baba ya lura da Raunukan dake Jikinta.

Girgiza kai yayi
“Hajjo dau Yarinyan nan ki kaita Ciki, Taci abinci tai wanka. Idan ta huta sai muji Koma menene”
Rungumeta Sadiya tai itama tana Kukan
“Kiyi Hakuri Sulthana, Mallan meh koh?”
Kasa cewa komai Tai sai kanta kawai tada Gyada. Da taimakon Sadiya da Mama ta Mik’e Mama ta kaita Dak’inta Ta zaunar da Ita, Dumamen tuwon dayaji man Shanu Mama ta kawo mata
“Sulthana ci abinci nasan Bakici Komai bah”
Kallan Abincin tai Sannan ta maida dubanta ga Mama
“Dagaske inci”
Gyada mata kai Mama tai Cikeda tausayawa wah, Hannu tasa Cikin Abincin ta soma ci tana Lumshe ido, Ganin Yanda takecin Abincin Hannu baka Hannu Kwarya Yasa Hawaye ya Gangaro ma Mama, Dasauri ta Mik’e tabar dakin Tana sharan Kwalla..

A tsakar Gida tai Kicibus da Sadiya tanata Safa da Marwa
“Keh Sadiya, Makarantan fah”
Turo baki tai tareda Kauda Kai
“Ni Mama bazanje makaranta bah, Kinga fah Sulthana batada lapia”
Sakin Baki Mama tai da Mamaki, A Ranta Fadi take
Lallai Sadiya Nasan Sulthana. Batace Komai bah Sai Girgiza kai datai tabar wajan, Sadiya na Ganin Tabar wajan ta Shiga Dakin Dah Sultanan keh Ciki. Zaune ata sameta Tana Cin Abinci, Kusa da Ita ta Zauna Tana Kallanta

“Sulthana Baffa neh koh?”
Nan da Nan hawaye suka cika Idonta, Sheshekan kuka ta Fara kanta a kasa
Matsowa kusa da Ita Sadiya tai ta Dafata
“Kiyi Hakuri kinji, Zancema Baba ya dawo dake nan gidan mucigaba da zama tare muna zuwa makaranta”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button