SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dagowa Sulthana tai Da Fara’a
“Dagaske Sadiya”
Kai Sadiya ta Gyada itama da Fara’a kwance a Fuskanta.
Saida ta Cinye Tuwon Tas Sannan ta Dago ta Kalli Sadiya dake zaune kusa da ita
“Sadiya Kaina na Ciwo tun Jiya”
Dasauri Sadiya ta mik’e batare datace komai bah ta fita daga dakin, Chan Sai gata dauke da Wani jikon Magani
“Gashi Mama tace Kisha, Sai kizo kiyi wanka”

Jim tai tana K’allan Sadiya, A Sanyaye Tasa Hannu ta K’arba Maganin Tasa Sannan Ta Mik’e, Zani Sadiya ta mik’a mata ta Amsa sannan tabar dakin. Kayan jikinta ta cire ta daura zanin Sannan ta Fito, A tsakar Gida tasamu Mama Bakin Murhu Tana Iza Wuta
“Sulthana kin Fito?”
Kai Ta gyada kanta a kasa
Murmushi Mama tai
“Maza kije ga Ruwa chan a kewaye kiyi Wanka”
Tho Tace ta Nufi Bandakin Idonta Cike da kwala, Zama Tai a Bayin Ta Fashe da Kuka a Hankali, Kuka take Sosai mara Sauti
“Umma meyasa zaki tafi ki barni, Dan Allah ki dawo nima kirinka sona kamar yanda Maman Sadiya ke santa”
Jin Muryan Mama a Wajan Yasa tai Saurin Goge hawayenta ta Fara wankan..

Tana Gamawa ta Fito tasamu Mama ta fito mata da Kayan da Zatasa, Saida ta kimtsa Sannan Baba Ya shigo dakin shida Mama, Tana Ganinshi ta Zame ta Zauna a Kasa. Kallanta yayi cikeda kulawa
“Sulthana fadamin meya Faru”
Hawaye neh ya Gangaro a Idonta, Duk abinda ya faru ta Sanarmusu.

Shiru Dukai Mama ta Kalli Baba
“Mallan Abinda Mallan Jamilu yake Baya Kyautawa, Sai kace Bashi Ya Haifeta bah, Niko a Mafarki Bantaba Ganin Irin Wannan bah, Abinda yakamata kishiyar mahaifiyarta tayi Sai kuma a Sameshi Wajanshi”
Shiru Baba yayi na Wasu mintina, Chan Ya dago Ya Kalli Sulthana
“Kiyi Hakuri Sulthana, A Matsayina na Aminin Mahaifinki Zanyi kokari Naga nayi mai magana ki koma Makaranta Sannan Ya daina Daura miki Talla”
Turo Baki Sulthana tai Idonta Ya kawo Kwalla
“Baba Ni bazan koma bah, ni Anan zan Zauna”
Mama neh Tai Saurin Cewa
“Mallan idan shi Mallan Jamilun Baya Santa Akwai Masu so dayawa, Wallahi da Zai amince ni Zan Iya rik’e Sulthana.”
Murmushin Takaici Yayi tareda Mik’ewa
“Hmm Hajjo knan”

Ummy Abduol✍????
????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 36 to 40*

Murmushin takaici Yayi tareda mik’ewa
“Hmm Hajjo Knan”
Bai jirah mai Mama zatace bah yabar Gidan…

Harya Fita ya dawo
“Sulthana dauko Hijabinki Muje”
Narai Narai da Ido tai Tana K’allan Mama
“Mama Dan Allah Kada mu Maidani ni banasan Gidan Baffa, Kullum Dukana Yakeyi”
Sadiya ce Ta Shigo dakin Dasauri Tareda Durkusawa
“Dan Allah Baba Kada a Maida Sulthana a Batta mu Rinka zuwa makaranta”

Hade Rai Baba yayi ya Kalli Mama
“Miko mata hijabi mutafi”
Jiki a Sanyaye Mama ta mikama Sulthana Hijabin Sadiya dak’e ratayi jikin Gado mai runfan dake dakin. Karba Sulthana tai tana kuka sosai, Saida tasa Sannan suka fito daga dakin, Kuka sosai Sadiya take tana Rokon Baba, Baiko Saurareta bah ya kama Hannun Sulthana suka bar Gidan..

Gidan Mallan Suka nufa, A Runfan da Almajiranshi Suke Baba ya hangoshi, Juyawa yayi ya K’alli Sulthana daketa Sharan Kwalla
“Tsaya a nan ina zuwa”
Tho Tace Ya nufi Runfan Mallan da Sallama
“Hade Rai Mallan Yayi Ganin Tareda Sulthana Suke”
Baba ya Mik’a ma Mallan Hannu suka Gaisa
“Mallan Jamilu Wurinka Nazo” cewar Baban Sadiya
“Tho Mallan Sani ina Sauraronka”
Jim Baban Sadiya yayi tareda Girgiza Kai

“Mallan Jamliu a matsayina na amininka mai kuma baka shawara, kuma kana Dauka. Yauma nazo da Nasihar nan da nasha maka Akan Y’arka Sulthana”
Tsaki Mallan Yaja Tareda Kauda Fuska
“Mallan Sani Na fada maka ka daina sa bakinka a Wannan maganar dan Sam bazan fasa abinda nai niyya bah”

Murmushin Takaici Baban Sadiya yayi Kanshi a Kasa
“Mallan Jamilu Knan, Nasan kasha fadamin haka Anma a matsayina na Aminin kah ya kyautu na Baka shawara ka dauka. Dubah kaga yanda kaima Yarinyan nan duka, Haba Mallan Sulthana Fah Amana ce a Gurinka”
Shiru Mallan Jamilu Yayi yana Cika yana Batsewa
“Ina mai rokon arzikin Kai hakuri yarinyan nan ta koma gida, saboda bai kamata Yarinya karama kamar Sulthana na Gararanba a Gari bah. Dan Allah kai min Wannan Alfarman”
Guntun Tsaki Mallan Jamilu yaja Sannan Ya Kalli Baban Sadiya
“Taci Darajan Kah, Anma dah bah haka bah bazata zauna min a gida bah”
Murmushi Baban Sadiya yayi ya Mik’a mai Hannu sukai Musabaha Sannan sukai Sallama..

Inda Sulthana take tsaye Baban Sadiya ya Nufa
“Sulthana Maza Shiga Gida Baffanku Ya hakura”
Nan da nan Fuskanta ya Chanza
“Dan Allah Baba ka tafi dani gidanka ni banasan Gidan Baffa dukana Yakeyi shida Yaya Hafsatu”
Jim Baban Sadiya yayi na Dan Lokaci, Shi Kanshi Yana Tausaya mata Yana kuma San Rik’eta Anma sam Mallan Jamilu ya Hana. Jin Tana Kuka Yasa Ya Lallasheta Tareda Rakata Har Cikin Zauren Gidan, Hannu Yasa a Aljihu ya Ciro Naira Hamsin Ya bata
“Gashi Ki siya wani abu kinji? Anma ki daina Kuka”
Kai kawai ta Gyada Ya mata Sallama Ya Bar Zauren..

Zama Tai Ta Fashe Da Kuka, Sai datai mai isarta Sannan Ta Mik’e ta Shiga Cikin Gidan. A Bakin rijiya Ta Hango Hafsatu Gabanta DaKwanonin wanke wanke sai Yatsine Fuska take. Sallama Tai a Hankali, Ameenatu dake Bakin Murhu ta Mik’e Dasauri
“Mama! Mama!! Fito ga Sulthana Ta Dawo”
Dasauri Mama ta fito da Fara’a ta K’araso inda Sulthana tak’e Tsaye
“Sulthana kin dagamin Hankali, Jiya bah Inda Su Ameenatu basuje bah Ba’a Ganki bah”
Hawaye neh Ya Gangaro mah Sulthana tai Saurin Sharewa Sannan Ta K’alli Mama
“Mama Dan Allah Kicema Baffa Ya barni na Koma gidansu Sadiya ni nafisan Chan”

Wata Uwar Ashar Hafsatu ta daka,
“Wallahi Kinyi kaddan, Idan Kika tafi Uban wah zai rinka Aikin Gidan”
Hararanta Ameenatu tai
“Kedai Hafsatu Bakida Hali Wallahi, Jiba Tun dazu Mama tasaki Wanke Wanken nan anma Baki koh Fara bah”
Tsaki Hafsatu Taja Tareda Turo dankwalin Kanta Gaban Goshinta
“Nifah Ya Ameenatu kin Fara takuramin a Gidan nan”
Bakinta Mama ta bige rai bace
“Hafsatu Bakinda Hankali, Ameenatu Yayarki ceh fah, na Lura Abubuwanki k’ara gaba gaba Sukeyi”
Turo baki tai Tabar Wajan Tana Gungunai..

Ameenatu ta K’araso inda Sulthana take tsaye
“Sulthana Ina Kika kwana? Waya baki wannan Kayan”
Kayan Jikinta ta K’alla sannan ta Dago ta K’alli Ameenatu
“A Wanchan Kangon na Kwana, Kayan Sadiya neh Mama ta bani”
Jim Ameenatu tai Batace Komai bah. Mama ta kama mata Hannu suka Shiga Dakinta, Lallashinta ta soma yi tana Bata baki har bacci ya dauketa a Wajan…

Sai bayan Azahar Mallan ya Shigo Gidan, Har lokacin Sulthana bacci tak’e. Dakinshi Ya wuce batareda tacema Kowa komai bah, Saida Ya gama Abinda Yake Sannan Ya Daga Labulen Dakin Mama dan ya sanar da Ita zai Fita. Sulthana ya hango kan Gado tana Bacci Hankalinta kwance
“Bude baki yayi da Alamar Mamaki, Lallai Yarinyan nan Wato har lokacin Bacci tasamu a Gidan nan”
Dakinshi ya koma ya dauko dorina Ya Tsula mata, Dasauri Ta mike Tareda Sakin Kuka
“Dan Allah Baffa Kai Hakuri Bazan Sake bah”
Jin Kukan Sulthana Yasa Mama dake Bandaki ta Fito dasauri
“Haba Mallan kaji tsoron Allah, Duk dukan dakama Yarinyan nan Bai isheka Bah”

Tsaki yaja ya koma Dak’inshi Ya Dibo Gyada Ya Fito, a Gaban Sulthana Ya direshi yana K’allanta
“Kinje Kin Kai K’arana wajan Aminina, Tho ki sani bai isa yasani na Sauya abinda nai niyya bah. Maza ki dau gyad’an nan ki Dafa, Kada ki bari na dawo na Tarar baki tafi Talla Bah”
Dasauri ta Amsa da
“Tho”
Jiki na Rawa tadau gyad’an ta Nufi bakin Rijiya Dashi. Babban Rigansh Ya kakkabe Yayi yabar Gidan Rai Bace, Binshi da K’allon Takaici Mama tai Tareda Girgiza kai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button