SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 41 to 45*

Babban riganshi ya kakkabe Yabar Gidan rai bace, binshi da K’allon takaici Mama tai tareda Girgiza kai. Bakin Rigiyan tah K’arasa ta taya Sulthana Wanke Gyadan suka daura a wuta, Abinci ta zubo mata Taci ta koshi. Gyadan na Dahuwa Mama ta juye mata ta daura mata ta Fita..

Kamar zata Shiga Gidansu Sadiya Sai kuma ta Fasa dan Fushi take dasu Saboda sun maidata Gida. Bakin Kasuwa ta Nufa da Gyadar, takoyi Sa’a Anata Siya. Kudi taga an Mik’o mata Naira Dari biyar, Ta zaro ido Batareda ta Dago bah, Bah Chanji.
“Kidai dubah, Gyadar tabani Saha’awa”
Muryan dataji neh yasa ta dago da Sauri sukai ido hudu da ita, Da Mamaki Ta K’alleta
“Sulthana Dama kina nan? Kullum idan na Tambaya Sadiya sai tacemin Kunyi tafiya har yanzu baku dawo bah, Meyasa kika daina zuwa makaranta Kika koma Talla”
Idon Sulthana neh ya Ciko da K’alla
“Baffa na neh ya Hanani”

Jim Matar tai tana K’allanta
“Laifi kika mai knan”
Dasauri Sulthana ta girgiza kai
“Aa malama banmai komai bah”
Kallan Gyadan tai
“Wannan Gyadan zaikai na Nawa?”
Dasauri Sulthana ta Amsa
“Nah Dari Uku ya Rage”
Murmushi malaman Tai ta Mik’a mata Dari biyar din
“Na Siya duka, Mik’e muje ki Rakani gidanku inaso nai magana da babanki”
Bah Musu ta Mik’e ta Juye mata gyadar a Leda ta mik’a mata, Turan ta daura Akai suka Kama hanyar Gida..

Da Sallama Suk’a Shiga Gidan, Mama ta amsa tana Zaune Kan Tabarma Gefenta Ameenatu Suna Shan iska, K’arasawa Mallaman Tai Ta Zauna Suk’a Gaisa da Mama. Dasauri Ameenatu ta gaidata dan ta koyar dasu a Makaranta, Gyaran Murya Mallaman tai tana Cewa
“Ni Mallama ce a G.G.S.S dake Garin nan”
Da Fara’a Mama ta k’ara Gaisheta, Mallaman Ta amsa tareda Cewa
“Mahaifin Sulthana Nake nema”

Dan Jim Mama tai Sannan Tace
“Ameenatu Yimai Magana Yana Waje Wajan Dalibai”
Tho Tace Ta mik’e tadauko hijab Ta Fita, Chan Sai Gasu Tare sun Shigo, Da Fara’a Ya Karaso
“Barka da xuwa malama”
Murnushi tai tana K’allanshi
“Barka dai Mallan”
Zama yayi Mama da Ameenatu Suka mik’e suka bar wajan, ya K’alli Sulthana dake gefe tanata Raba ido
“Keh Bazaki tashi bah sai kin Gama ji kiji dadin barbadawa Gari”
Dasauri ta mik’e Jiki na Rawa tabar Wajan. Maido da dubanshi yayi ga mallan
“Ina Fata dai Lapia Malama”

Murmushi ta kuma Yi
“Gaskiya bah Lapia bah Mallan”
K’allanta yayi da Alamar Mamaki
“Meh ya Faru Mallama”
Dago kai tai ta K’alleshi
“Zaikai Shekara daya knan dah bana ganin Sulthana Jamilu a Makaranta, nakan tambayi kawarta Sadiya Sani Kullum sai tacemin Sunyi tafiya basu dawo bah, Yau kuma Sai Gashi na Ganta a bakin Kasuwa tana Talla”
Shiru tai tana k’allanshi Ganin Yanda Ya Hade Girar Sama data K’asa
“Eh Hakaneh Sulthana ta dena zuwa makaranta”
Da Mamaki Mallama ta K’alleshi
“Saboda meh Mallan”
Kauda Fuska Yayi sannan Yace
“Saboda na Cireta, Banida Kudin dah zan Rinka biya mata Kudin Makaranta”
Mamaki neh ya kama Mallaman Saboda tasha jin Labarin Mallan Jamilu da kuma dukiyarda Mahaifinshi yabar mai..

Girgiza kai Tai
“Mallan Sulthana tana Cikin Yaranda Keda Matukar kokari a Makarantan nan, Ka daure ta cigaba da Zuwa makaranta. Ina mai tabbatar maka insha Allahu wata rana zakai Alfahari da Ita”
Tsaki Mallan Yaja Yana K’allanta a hassale
“Bazata komah bah ko dolene”
Murmushin Takaici tai
“Tho Shiknan Mallan ka Yarda ta cigaba da zuwa ni nayi Alkawarin zan cigaba da daukan Dawainiyar tah”
Mik’ewa Mallan Yayi Dasauri Rai Bace
“Ce Miki Akai Banida Kudin dazan Biya mata? Makaranta neh Kuma nace bazata Koma bah ko Yarki ce”
Ran Mallaman neh Ya Baci itama ta mik’e a Hasalle
“Anya Mallan Jamilu kai ka Haifi Sulthana Kuwa? Dan ni koh a Karance Karance da yawan Karatu danai ban taba ganin Irin Wannan bah”..

Kofa Mallan Ya nuna Mata
“Maza ki tattara kibar min Gida, Karna Kara ganinki a Gidana, Itakuma Sulthana’n zataxo ta Sameni Wato K’arana Ta kawo Miki koh”
Tsaki Mallaman Taja Tabar Gidan Rai Bace, Jin ta fita Mama ta fito daga Daki
“Haba Mallan Abinda kai ya dace? Gaskiya abinda kake Baka kyautawa, Mallan Kaji Tsoron Allah Haba sai kace bah Mallami bah”
Baice komai bah Sai Hucin Dayakeyi, Dakinshi Ya shiga ya Dauko dorina ya nufi Zaure, Duka Yama Sulthana Sosai Sannan Ya bar Gidan Cikeda Bacin Rai..

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 46 to 50*

  Wannan Shafin naki neh *Bilkisu Jibril* Nagode Sosai Allah Yabar K'auna

Dasauri ta Mik’e tana Zaro ido, Trayn dake gefenta ta dauka ta Fara tafiya tana waigensu. Tsaki Yasir Yaja Yana Cewa
“Yara basajin Magana musamman na Kauye, Ji Wannan yarinyan dan Allah, Yanxu haka aikenta akai ta tsaya nan ruwa ya mata duka”
Shidai Masroor shiru yayi yana Bin Hanyan da Sulthana ta nufa da Kallo. Taboshi Yasit yayi Tareda Yatsine Fuska
“Yadai Shagwababe”
Dukan Wasa Masroor yakai mai
“Bansan Iskanci fah Yasir I hate dis name”
Dariya Yasir Yayi harda Kyakyatawa
“Ni kuma kaga I love the name, Shi zan Cigaba da Kiranka”
Tsaki Masroor yayi batareda Yace Komai bah yayi shigewarshi Motan Ya Zauna, Murmushi Yasir yayi shima Ya shiga motan ya Kunna suka Bar wajan..

Sauri Sulthana take Hannunta na Hago Rik’e da Tryan Gyadarta na Dama ta Dafe Kirjinta tana Numfashi Dasauri dasaur, Gajiya ta soma yi dan haka ta rage Saurin datake Ta cigaba da Tafiya. A kwanan dazai kaita gidansu tai arba da Ameenatu, Ganin Halinda take ciki yasa Ameenatu ta rik’eta Dasauri
“Sulthana Lapia? Meke Damunki”
Kasa magana Sulthana tai Sai K’irjinta datake nunama Ameenatu, kamata tai suka nufi gida. suna shiga gidan Ameenatu ta soma kwallama Mama, Mama ta fito dasauri ganin Halinda Sulthana take ciki yasa Ta K’araso inda suke ta kama Sulthanan ta nufi dakinta da Ita…

Ameenatu ta Fita dasauri ta Dauko wani Kaya ta shigo ta cire mata na jikinta ta Chanza mata, Mama ta fita ta Dibo Garwashi a kasko ta soma Gasa mata Jikinta. Lokaci Guda Sulthana ta fita Hayyacinta Numfashinta na cigaba da Fita sama sama, Hankalin Mama da Ameenatu bah K’aramin tashi Yayi bah, Duk abin nan da ake Mallan na Dakinshi kwance abinshi. Ganin halinda Sulthana take ciki yasa Mama ta nufi dakin mallan dasauri, Da Sallama ta shiga ya amsa yareda dagowa
“Lapia meke Faruwa naganki a rude”
Hankali tashe Mama tasoma magana
“Mallan Sulthana fah batada lapia Sosai gatachan Kwance bata numfashi sosai”
Tsaki Mallan Yayi ya koma ya kwanta
“Wallahi Saratu kinada Matsala, Tho ina ruwana dan batada lapia”
Da Mamaki Mama ta k’alleshi
“Haba Mallan, wai meyasa kake haka ai yarinyan nan ko tsintanta kai baka kamata irin wannan rik’on bah Balle Y’arka daka Haifa”

K’ara jan Tsaki yayi tareda juyawa
“Saratu kina damuna Ki Fita kiban Guri Barci Nakeji”
Girgixa kai Mama tai cikeda takaici ta fito daga dakin, Hafsatu ce ta fito daga bandaki Ta aje buta ta kokarin shiga dakinsu, Mama ta tareda dasauri
“Hafsatu dan Allah idan kinada Dari Uku ki ranta min Zankai Sulthana Chemist ne batada Lapia”
Tabe baki Hafsatu tai
“Ni Mama ina naga Dari uku banida ko sisi nan da kika ganni”
Mamaki ne ya cika Mama harta kasa boyewa
“Haba Hafsatu Dazu fah dasafe naji kina fadama Ameenatu saurayinki ya baki dubu daya”
Turo baki Hafsatu tai tana gungunai
“Inadashi anma gaskiya Mama bazan bada dan Akai Sulthana Wani Chemist bah”
Bata jira mai Mama Zatace bah tabar wajan tana Surutai a Hankali. Binta da Kallo Mama tai tai Cikeda Bakin Ciki..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button