SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

SULTHANA COMPLETE HAUSA NOVEL

Dakinta ta koma yanda tabar Sulthana haka ta dawo ta sameta, Ameenatu ta dago ta K’alli Mama Hankali tashe
“Mama meh Baffan yace”
Girgiza kai Kawai Mama tai batace komai bah, Ameenatu ta gane mai Ake Ciki ta Mik’e tsaye Tana Share Kwalla
“Mama barinje Gidan Baba Sani nasan Zai Taimaka”
Saurin Rikota Mama tai tana girgiza mata kai
“Aa Ameenatu karkije Kinsan idan kikaje idan ranmu yayi dubu ya baci a gidan nan saboda kinsan sai Mallan Sani yamai magana”
K’allan Sulthana Ameenatu tai ta Fashe da Kuka
“Mama haka zamu zuba ido muna K’allan Halinda Sulthana take Ciki bamuda Bakin magana. Wai meyasa Baffa yake Haka Neh”
Bata jira mai Mama zatace bah ta nufi dakin Baffa Idonta rufe Saboda bacin Rai..

Sallama tai a dakin, Baffa ya amsa tareda mata izinin ta Shigo, ta Shiga ta Samu Guri Kusa da Gadon K’arfenshi ta zauna. K’allanta Baffa Yayi Yana yar Murmushi
“Ameenatu lapia”
Dagowa tai ta K’alleshi Bako digon Tsoro a ranta
“Baffa Abinda kakeyi Babu kyau, Meyasa kake Wahalar da Sulthana. Dan Allah inaso nai Maka Wani Tambaya”
Murtuke Fuska yayi yace
“Ina Sauraronki”
Jim tai nadan wani lokaci Sannan tace
“Baffa Anya kuwa kai ka Haifi Sulthana”
Juyowa Baffa tai dasauri Cikeda Mamakin Maganan Ameenatu…

Tho Fah

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 51 to 55*

       I Dedicated is Page to Uh *My Ummyn Yusrah* nagode da Soyaiyyarki Gareni

“Baffa Anya kuwa kai ka Haifi Sulthana”
Juyowa Baffa tayi dasauri Cikeda Mamakin Maganan Ameenatu. Bata ankara bah Taji Saukan kyakyawan Mari a Fuskanta, A gigice ta dago Ta K’alleshi tareda Dafe Kuncinta. Huci Yake Sosai Yana K’allanta
“Ameenatu ashe duk K’allan danake miki na Mai Hankali bah haka baneh, Ficemin a daki tun ban zaneki bah”
Dasauri tabar Dakin Tana Hawaye dafe da Kuncinta, Batabi takan Dakin Mama bah ta Fita daga Gidan rai bace..

     *Shin Suwaye Masroor da Yasir*

Alhaji Aminu Sunan Mahaifin Masroor dan Asalin Jahar Gombe neh Zama Ya kawoshi Garin Kano, Yanada Mata Hajiya Salma mace mai Hakuri da Juriya da Sanin Yakamata, Alhaji Aminu Babban dan siyasa neh Wanda a Halin Yanzu Yafito Takaran Gwamna Jahar Kano. Yanada Y’aya Biyu a Duniya Masroor shine Babba dan Shekara Ashirin da Shidda, Saurayi kyayyawa Ajin Farko, Dogo Mai Cikar Zati. Yayi K’arastunshi Na primary da Secondary a Kano daga Bisani Mahaifinshi ya turashi K’asar Turkey inda Yake Karatunshi na Architecture, Kasancewarshi Tun yana Yaro Ma’abocin Zane Zane..

A Yanzu Haka Yana shekaranshi na k’arshe a Makaranta, Satinshi Daya knan Da Dawowa K’asan Dan Sun Samu Hutu. Yanada K’anwa mai Suna Mahnoor Y’ar Shekara Sha Biyu tana Js2 yanzu. Suna Zaune Cikin Jin Dadi da Annasuwa a Familyn Kasancewar Mahaifiyarsu ta basu Tarbiya mai Kyau da Kulawa..

Yasir Ya Kasance Aboki kuma Aminin Masroor, Sun Kasance Abokanai tun Suna Yara Ta Sanadiyan Iyayensu Mata da Suk’e Kwaye. Zuwansu Kauyensu Sulthana yasano Asaline kan Project da Yasir Yake Rubutawa Akan Traditional Herbs, An Musu Kwatancen Wani Tsohon Mallami mai bada Maganin shine Sukazo ruwa Ya Tsaresu a Hanya..

 Cigaban Labari

Cikin Garin Yasir keh K’okarin Shiga Masroor ya juya yana K’allanshi
“Pls mu koma Gida, I’m Feeling Sick”
Da Mamaki Yasir Ya K’alleshi
“Kuma! Kaifa Shagwababen nan Tsiyata Dakai Knan”
Kauda Kai Yayi Batareda Ya bashi Amsa bah, Kan Motan Yasir Ya Juya Suka tasanma barin Garin. Saida Suk’a Bar Kauyen Sannan Masroor ya Saki Ajiyar Zuciya Mai K’arfi Har saida Yasir ya juya ya k’alleshi. Murmushin Takaici Yaja
“Abinda mukajeyi mah baka bari munyi bah, Masroor Kanada Damuwa”
Murmushin Mugunta Yamai Yana Yatsine Fuska
“Haba Mallan Ka kaini Kauye ina K’okarin Mutuwa, Allah K’ar ya K’ara Kaini K’auyen nan So Boring Wallahi”
Murtuke Fuska Yasir Yayi Bai K’ara Cewa Komai bah Yar Suka Isa Gida..

Wani Hadadden Gida Na gani na Fada Sukai Horn Masu Gadu su Wajan Uku suka Taso a Guje Suka Bude K’aton Gate din Dake Gidan, Saida Sukai Parking Sannan Yasir Ya K’alli Masroor Dake Kokarin Fita Daga motan
“Kauye Bah! Hmm Shagwababe Yanzu mah Kah Fara Zuwa Insha Allah”
Bai Jira Mai Zaice bah Ya Fita Daga motan Ya nufi Main Palourn Gidan Fuskah bah walwala. Binshi da K’allo Masroor yayi Sannan Ya Fito ya rufe Motan ya rufa mai Baya..

A Falo suka Tadda Hajiya Salma Tana Zaune Kan Lumtsatiyar Kujerun Dake Falon Sanye da Farin Medicated Glass Hannunta Rik’e da Jarida Alamar Karatu Take, Jin K’aran Bell Yasa dago. Wata mai aiki ce ta Fito Jiki ja Rawa ta Bude Kofan Tareda Duk’awa ta Gaida Yasir Sannan Tabar Wajan. Ajiye Jariymdan Hannunta Tai Tana Murmushi
“My Sons Har an Dawo”

Wajanta Ya nufa Yana Bata Fuska
“Mami Bamuyi Komai bah, Infact koh Cikin Garin bamu k’arasa bah Masroor yasa Muka Baro”
Dai dai Nan Masroor ya Shigo da Sallama Yana Hararan Yasir
“Mami Gulmana Ya Kawo koh, Karya yake dukma abinda Ya Fada”
Girgiza Kai Mami tai Tana Y’ar Murmushi, Tunasu ta Shiga Yi da Yatsa
“Ku Biyun nan Bah Abinda zance sai Allah Ya Shirya”
Mik’ewa Tai
“Bazan Tsaya Jin Shirmen nan naku bah inada abin yi”
Saman Benen Gidan Tahau Tana Yar Murmushi tareda Cewa
“If uh need any thing Call the Maids”
Bata jira mai Zasuce Bah ta Shiga Wani Kofa Ta rufe…

A Bangaren Sulthana Fah
Ameenatu na Fita Tayi Arba da sani Saurayinta Cikin Almajiran Mallan, Gaisawa Suk’ai Ya Kalleta nadan Mintina Yace
“Ameenatu K’amar kina cikin Damuwa”
Dan Murmushin Yak’e tai
“Bbu komai Saminu Dama Magani nakeso na Saya Banida K’udi kuma Baffa na Barci”
Bah T’areda bata lokaci bah Yace
“Har na Nawa”
Dan Jim Tai Sannan Tace
“Dari Uku neh Dai nake tunani”
Hannu Yasa a aljihu ya Ciro Dari Biyar Wacce Ita k’adai ta Rage mai ya mik’a Mata
“Gashi Bah Yawa Kiyi Anfani dashi”
Godiya Ta shiga yi Mai sannan Sukai Sallama Ta koma Gida…

Dakin Mama ta Shiga tana Nuna Mata Kudin, Chak ta Tsaya Ganin Mama Zaune tana Kuka Gaban Sulthana dake Kwance Warwas Bata Numfashi..

Ummy Abduol✍????
[28/08, 01:12] Friend Hussaini: ????????????????????????????????
????????????????
SULTHANA
????????????????
????????????????????????????????

By Ummy Abduol

      *Page 56 to 60*

Dakin Mama ta shiga tana nuna mata kudin, Chak ta tsaya ganin Mama zaune tana kuka gaban Sulthana dake kwancd Warwas Bata numfashi, A Hankali ta Sulale ta Zauna a Wajan Tana K’allan Mama
“Mama Meyasa kike kuka”
Cigaba da Kukan Mama tai Dak’yar ta Iya Cewa
“Sulthana Bata Numfashi, Allah dai Yasa bah rai baneh Yayi Halinsa”
Mik’ewa Zumbur Ameenatu tai ta Fita Ta nufi Dak’in Baffa, A Rufe ta Sameshi Alamar Ya Kulle daga Ciki. Dukan Kofan ta fara tana magana cikin daga murya saboda ya jiyota
“Dan Allah Baffa ka bude kofan, Sulthana bata numfashi ka tashi dan Allah mu Kaita Chemist”
Kuka Take sosai a wajan tana cigaba da buga kofan anma a banza, Hafsatu da tunda ta fara bugawa ta leko daga dakinsu tace
“Yaya Ameenatu ku daina damuwa da Lamarin Yarinyan nan, Wanda ma ya haifeta bai damu da Itaba Balle Ku”

Mari mai rai da Lapia Amenatu ta Wankama Hafsatu tana huci
“Hafsatu na lura Iskancinki k’ara Gaba yake, Tho Wallahi ki sani idan baki sauke gigin dake Kanki bah Sai nayi maganinki a gidan nan”
Kuncinta tah Rik’e baki bude
“Dan Nafada muku gaskiya shine zaki Mareni”
Tsaki Ameenatu taja ta Shiga Dak’in Mama a Fusace.
“Mama tashi Muje Chemist, Insha Allahu bah abinda zai Sameta”
Mik’ewa Mama tai tadau Hijabinta Tasa, Ameenatu ta Mik’e Sulthana Tsaye
“Mama Samin Ita a baya na Goyata”
Taimaka mata tai tah Goyata Suka Fito Suka Fita Daga Gidan, Dare Ya soma yi dan Sahu har sun Fara daukewa. Tafiya Suke dasauri sauri Mama na Haska musu Hanya da Torch light, Akwai Tazara sosai Tsakaninsu Da Chemist din Saboda Shi Kadai Garesu duk Kauyen..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36Next page

Leave a Reply

Back to top button